ALI Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork, ya shahara sosai a aikin editin. A shekarar 2015 shi ne ya lashe gwarzon mai tace hoton fim a gasar Kannywood Awards kashi na uku da aka yi a Abuja. Daga baya kuma sai Ali ya rikid’e ya zama fitaccen jarumin barkwanci. Sai dai wasan barkwancin nasa yawanci ba a fim ya ke yi ba, ya fi yin su a wurin manyan tarurruka da ake gayyatar sa. Ya na kuma shirya gajeren bidiyo na bakrwakwanci ya tura a shafukan san a soshiyal midiya. Za a iya cewa a cikin jaruman barkwanci na yanzu babu wanda tauraruwar sa ke haskawa kamar sa.
Wakilin mujallar Fim ya tattauna da Ali Artwork kwanan baya a Kano inda ya fede masa biri har wutsiya game da harkokin sa na rayuwa. Sannan ya yi tsokaci kan rashin taimakon k’ananan jarumai da ake yi a Kannywood.
FIM: Za mu so ka gabatar mana da kan ka, kuma ka ba mu tak’aitaccen tarihin ka.
ALI ARTWORK: Suna na Aliyu Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork. Ni dai an haife ni a K’aramar Hukumar Tarauni a Unguwa Uku, (Kano). A nan na yi karatun firamare d’i na da na sakandire. Daga nan kuma kuma na tafi Sa’adatu Rimi College of Education, Kumbotso, na fara NCE 1, na kai NCE 2 abubuwa su ka damalmale, shi ne na fad’o harkar fim.
FIM: Ko za ka iya tuna shekarar da ka fara tace finafinai?
ALI ARTWORK: Na fara had’a hoton fim tun ina Junior Secondary School a shekarar 2008.
FIM: Da wane fim ka fara?
ALI ARTWORK: Akwai wani fim ana ce masa ‘Sabo Da Kaza’. Wani tsohon fim ne na Ibro. Daga nan kuma sai irin su ‘Adamsy’, ‘D’an Marayan Zaki’, ‘Ashabul Khafi’, ‘Ga Fili Ga Mai Doki’, da sauran su. To, duk ni na tace hoton su a wancan lokacin.
FIM: A cikin jerin finafinan da ka tace, wanne ka fi so?
ALI ARTWORK: Na fi son fim d’in ‘Maja’. Babban su kuma shi ne fim din ‘Gwaska’ saboda na samu award da shi, duba da yadda na sha wahala a aikin fim d’in, sai dai wahalar ba ta tashi a banza ba.
FIM: Ka na maganar cewa ka sha wahala a wurin tace fim d’in ‘Gwaska’, amma wasu kuma su na ganin kamar ba wani aiki ba ne ku ke mai wahala.
ALI ARTWORK: Ai duk wanda ya ce aikin mu ba shi da wahala to bai san aikin ba ne. Amma idan ka cire wanda ya zuba kud’in sa ya d’auki nauyin fim d’in da kuma daraktan, to babu wanda ya kai mu shan wahala. Saboda mu za mu gyara fim d’in ya zama fim. Shi tace fim da ka ke gani zan iya yi maka misali da kamar leburanci ne. Misali, a kira lebura a ce masa ana so ya gina gida. Ka ga za a kawo masa siminti, yashi, bulo, dusti, da sauran su; shi zai tashe su ya su zama gida. Idan aka ce babu shi, ya za ai gidan ya ginu? Ba zai ginu ba. To, kamar haka edita ya ke; za a d’ebo duk wani tarkace da ka sani a zo a zuba, shi zai tace wad’annan abubuwa, ya zo ya sanya su inda ya dace. Inda akai duka ya sanya duka, inda akai mari ya sanya k’ara irin ta mari, da sauran su.
FIM: Ya aka yi kuma ka rikid’e daga mai tace hoto zuwa jarumin barkwanci?
ALI ARTWORK: Mutane ne su ka zab’o ni. Kamar da wasa na tab’a fitowa a wasu gajerun bidiyon ban-dariya da ake yi mai suna ‘Rumbun Dariya’. To, daga wannan lokacin mutane su ka fara yi min kallon “wannan idan ya na harkar nan zai ci abinci da ita saboda ya iya”. Ni kuma a lokacin ban san ma na iya ba, sai ya zamana mutane na ba ni shawara: “Me ya sa ba za ka rik’a yin kaza ba?” Sai na ce masu ba matsala. To, ina yi da kad’an-kad’an ban damu ba, sai na wayi gari har idan na wuce mutane sun san ni, ana cewa ga wane da sauran su. Amma gaskiya ni da farko ba aktin ba ne ya kawo ni; da fasta ma na ke yi wa ’yan fim, daga baya na rikid’e na koma edita, shi ne har Allah Ya kawo ni wannan lokacin da na ke shirya wasannin barkwanci.
FIM: Ana ganin a yanzu ka daina ma tace finafinai, ka koma harkar wasan barkwanci zalla.

ALI ARTWORK: Gaskiya harkar barkwanci ba ta hana ni tace fim ba. Saboda ko a wannan shekarar na tace finafinai irin su ‘Abdallah’, ‘Aljannar Mace’, ‘Ja Ni Mu Je’, da sauran su; duk kwanan nan kuma aka yi su.
FIM: Ya maganar taimakon k’ananan jarumai da aka ce ana yi a masana’antar finafinan Hausa?
ALI ARTWORK: Waye ya ke taimakon su? Babu wanda ya ke taimakon k’ananan jarumai.
FIM: Mecece hujjar ka ta fad’in haka?
ALI ARTWORK: Hujja ta ita ce kullum tsiraru ne ake gani a harkar, duk wanda ya ce ma ya na taimakon k’ananan jarumai k’arya ya ke! Idan ana so a taimaki k’aramin jarimi… yanzu kamar wani fim da aka yi, ‘Bahubali’, kai ka san wannan duk duniya an taimake shi. Yanzu ka duba, ba wai Indiya kad’ai ba, duniya ma ta san shi. Amma mu wa zai d’auko ka ya yi maka irin wannan tafkeken fim d’in a matsayin ka na jarumi?
Furodusoshin mu su ma su na da tasu matsalar. Su na raina k’aramin jarumi ba don komai ba sai don su na ganin idan su ka yi fim d’in su ka kai kasuwa ba za a saya ba sai wane da wane. Amma yanzu alhamdu lillahi tunda aka fara harkar sinima mu na sa ran komai zai canza. Su kuma k’ananan jaruman abin da ke dakusar da su shi ne su zo su zauna a k’ark’ashin jarumi su ce wai shi zai taimake su har su yi fice. Kai yanzu fisabilillahi ka na k’aton jarumi za ka iya yi wa wani fim d’in da ba za ka iya yi wa kan ka ba? Ai bai zai yiwu ba.
FIM: Amma su manyan jaruman, kullum su na fad’in cewa su na taimakon k’ananan jarumai. Me za ka ce a kan haka?
ALI ARTWORK: Ka san me ake nufi da taimakon k’ananan jarumai? Yanzu misali, manyan jarumai za su rik’a d’aukar wani fim babba kar su sanya kan su a ciki, kawai su samu k’aramin jarumi ak’alla su yi masa fim uku. Kuma su kai kasuwa a yi talla su yi wa fim d’in dukkan abin da za su iya yi wa kan su. Nan ne na san za a taimaki k’ananan jarumai. Amma yanzu ka ce min ka na taimakon k’aramin jarumi amma kullum so ka ke ya fito a k’ark’ashin ka, hakan ne taimako?
FIM: A ganin ka daga ina matsalar ta ke?
ALI ARTWORK: Kowa ya na da laifi. Yanzu idan ka d’auki Don Jazzy; da Korede Bello da Banz da Dija, duk taimakon da ya dace ya na masu. Shi yanzu ba wai d’aukaka ba ce a gaban sa, kud’i ya ke nema masu, zai kai su inda ba su tab’a zuwa ba, kuma zai nema masu kwangiloli da manya-manyan kamfanunnika. Amma mu a Kannywood wa ya tab’a yin haka? Kullum so ake gan ka “a k’ark’ashin mu ka ke, sai yadda mu ka yi da kai, idan ba ka biyo mu kuma ba za mu bar ka, ba za ka kai labari ba”. To, idan ba ka had’a da addu’a ba sai abubuwan su cakud’e maka. Su kuma k’ananan jaruman saboda toshewar basira sai a ce masu “idan ba ka bi ta hannun wane ba, ba za ka yi komai ba.” An riga an cire masu tauhidi tun tuni!
Iyayen Ali Artwork su na taya shi murnar samun lambar girma
FIM: Kai yaron wanene?
ALI ARTWORK: Ni ba yaron kowa ba ne! Ni ba yaron kowa ba ne! Ni mai nema ne.
FIM: Ka na nufin ba ka da maigida wanda ya koya maka komai a harkar fim?
ALI ARTWORK: Maigida na shi ne Aminu Bacci, shi ya koya min sana’ar tace fim. Kuma har yanzu da ita na ke ci na ke sha, don haka maigida na ne. Amma idan ka cire shi duk wanda ya ce ni yaron sa to ni ba yaron sa ba ne in dai a masana’antar fim ya ke. Shi kuwa Aminu Bacci shi ya koya min sana’a amma duk wanda ya ce in zauna a k’ark’ashin sa sai yadda ya yi da ni, ba zai d’ora ni hanya mai kyau ba, kuma ba zai min umarni na bar abu marar kyau ba, to wannan ni ban d’auke shi a matsayin maigida na ba.
FIM: Shekarun baya kun tab’a samun matsala da Ali Nuhu, abin ya yi tsami har ya kai ga an kai ka wurin ’yan sanda an kulle ka tsawon kwana biyu. Yanzu ya alak’ar ka ta ke da shi?
ALI ARTWORK: Ni yanzu ban rigima da kowa. Ba ni da abokin fad’a, ni kowa nawa ne. Wanda ya ce zo mu tafi, za mu tafi, wanda kuma bai yi da kai ba ka rabu da shi. Ita rayuwa Allah da Ya halicce ka tun kafin ka zo duniya Ya riga Ya tsara maka abin da za ka zama. Kuma ita rayuwa zo mu zauna, zo mu sab’a ne. Wani lokacin ma sai an sab’a d’in sannan ake gane kuskure, sai kowa ya gyara.
FIM: Me ya sa yanzu ka rage shiga cikin ’yan fim?
ALI ARTWORK: Saboda ni handsfree ne! Idan an yi rashin adalci zan fad’a, idan an yi abin da ba daidai ba ma zan fad’a. To, sai ya zamana akwai wad’ansu mutane a cikin harkar wad’anda ba su son gaskiya, sun fi so ka bi su yadda su ke; ko da abin da su ke yi ya take addini, kai ma ka bi ka take. Ni kuma ba zai yiwu baba na Musulmi, baba ta Musulma, wani abu ya zo ya b’ata min huld’a ta ba. A cikin annabawan Allah ma akwai wad’anda aka umarce su da su sab’a wa Allah, su ka ce ba za su yi ba, ballantana kai da mu ka had’u da kai a bariki.
FIM: Ina ne bariki?
ALI ARTWORK: Duk mutumin da ya fita nema, in dai ya bar unguwar su ko kuma garin su, to bariki ya je. Kar ka d’auka wai bariki gidan karuwai ko gidan giya shi ne bariki kad’ai, in dai ka fita nema inda ba garin ku ba kuma za ka had’u da mutane iri-iri, to sunan wurin bariki.
FIM: Menene burin ka a Kannywood?
ALI ARTWORK: Buri na masana’antar fim ta canza. Ina so ta yi nisan da ba a tab’a tsammani ba. Amma sai mun cire hassada da bak’in ciki. K’irik’iri ga k’ananan jarumai mu na da su wad’anda su ka iya aktin amma an k’i a taimaka masu! Su kuma da ya ke marasa zuciya ne sun je sun biye wa wasu mutane kawai su na zaune da su, sai ka ji ana cewa, “Idan ba wane, ba za ka yi gaba ba.” Allah ne wanen? Ko wani abu ya fi ka a wurin Ubangiji? Allah ne Ya d’aukaka shi, kuma kai ma idan ka sa Allah a ran ka, ka rik’a addu’a, in dai a zuciyar ka babu bak’in ciki ko hassada ko manak’isa, to wallahi Allah zai taimake ka. Amma in dai ka dogara ga wani, to ka na tare da wahala.
FIM: Menene sak’on ka na k’arshe ga masoyan ka?
ALI ARTWORK: Ina godiya ga masoya na da su ke nuna min k’auna. Don Allah a ko da yaushe idan an ga na yi kuskure sai a sanar da ni, idan ka kira ni ta waya ban d’auka ba sai a turo min sak’o ta waya ta domin na gyara. Allah Ya sa mu dace.
![]()







