A JIYA Talata Allah ya ɗauki ran mahaifiyar fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, Hajiya Halima K/Mashi.
Hajiya Yahanasu Sulaiman ta rasu ne da misalin ƙarfe 5:48 a ranar 12 ga Maris, 2024 a kan hanyar zuwa Asibitin Nassarawa daga Asibitin Murtala da ke Kano.
Dattijuwar mai kimanin shekara 90 a duniya ta rasu ta bar ‘ya’ya uku da jikoki sama da hamsin. Halima ita ce ta biyu a cikin ‘ya’yan.
Halima, wadda ita ce Shugabar Ƙungiyar Marubuta Alƙalam, ta faɗa wa mujallar Fim cewa ba doguwar jinya mahaifiyar rata ta yi ba, zazzaɓi ta riƙa yi saboda jikin girma.
An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar yau Laraba a unguwar Sheka, Ƙarshen Kwalta, a Kano.
Allah ya jiƙan Hajiya Yahanasu, ya albarkaci dukkan abin da ta bari, amin.
