MASARAUTAR Gidan Igwai da ke Jihar Sokoto ta bayyana tuɓe mawaƙi Usman Umar (Sojaboy) daga sarautar Yariman Gidan Igwai ta taɓa naɗa shi.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da Sojaboy daga daga shiga duk wasu harkoki da suka shafi Kannywood a Jihar Kano saboda bidiyon da ya yaɗu a soshiyal midiya inda aka ga mawaƙin yana rungumar wasu mata.
A takardar da ta tura masa ɗauke da sa-hannun Alhaji Abubakar Marafa a madadin Sarkin Adar Gidan Agwai, masarautar ta ce: “An umarce ni a madadin mai girma Marafan Gidan Agwai domin in gabatar da wannan takarda ta dakatarwa da kuma tuɓewar ka daga sarautar Yariman Gidan Agwai saboda yaɗa bidiyo mai ɗauke da shagala da rafkana da badala, wadda ta saɓa wa addini da al’ada da ɗabi’un unguwar Gidan Agwai da al’ummar da ke cikin ta.
“Gundumar Gidan Agwai da ɗaukacin al’ummar ta sun yi tir da Allah waddai da yaɗa wannan badala, a kan haka suka barrantar da kan su daga wannan mummunar dabi’a da rashin dattako.
“Muna addu’a da kuma fatar za ka gyara ka kuma saita dukkan lamurran ka a kan tarbiyya da addini da ɗabi’un mu na Musulunci. Wassalam.”
A takardar, an nuna cewa an aika da kwafen ta ga fadar Sarkin Musulmi da ofisoshin Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato da Kwamishinan ‘Yansanda da daraktan DSS da Civil Defence na jihar da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Arewa.

A lokacin da ta yanke hukuncin dakatar da Sojaboy ɗin daga Kannywood, Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta haɗa har da jarumai matan da ya runguma, wato Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan.
Hukumar ta yanke hukuncin bayan ɓullar wasu fayafayen bidiyo na sabuwar waƙar sa mai suna ‘Bugun Zuciya’ a soshiyal midiya, wanda ke nuna fasiƙanci da ya saɓa wa addini, al’ada, ƙa’idoji da ɗabi’un Kano.
Hukumar ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe da dama daga al’umma da kuma malaman jihar a kan wannan lamari.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, wadda ya fitar a yau Litinin, hukumar ta bayyana cewa an sha gargaɗin Sojaboy a kan abubuwan da suka shafi lalata da kuma rashin mutunci.
Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya umurci sashen tacewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da waɗannan jarumai mata su biyu ba su shiga cikin duk wani shiri na Kannywood ba.
Ya kuma umurci duk wuraren shirya finafinai da nishaɗi su lura.
