MATASAN nan biyu masoyan mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da su ka yi tattaki daga Kaduna zuwa Kano sun iso garin a yammacin jiya Alhamis, 8 ga Satumba, 2022.
Mujallar Fim ta ba da labarin yadda matasan, Anas M. Lawan da Mustapha Iliyasu, su ka kama hanya a ƙafa tinkis-tinkis tun daga Kaduna da zummar ganin Rarara a Kano don nuna masa goyon baya kan harkar sa ta siyasa.
Isowar su ke da wuya, su ka nufi ofishin Rarara da ke Titin Gidan Zu.
Sai dai kuma sun daki gurbi ko kuma a ce sun taki rashin sa’a, domin ba su samu ganin masoyin nasu ba saboda ya yi tafiya, ba ya gari.
Amma dai sun samu gagarumar tarba daga wakiliyar sa, fitacciyar jaruma A’ishatu Ahmad Idris (Ayshatulhumaira) wadsa ta tarbe su a madadin sa.
Jarumar ta shirya masu liyafa ta musamman domin nuna girmamawa a gare su.

Sai abin da jama’a da dama su ke cewa shi ne babu wani tabbas da ya nuna ko a ƙasa matasan su ka zo Kano kamar yadda aka san sauran masu yin tattaki na yi.
Haka kuma tattaki irin wannan ba wani sabon abu ba ne ko abin burgewa a ƙasar nan ganin yadda abin ya zamo ruwan dare wanda har ta sa wasu ma idan aka fara yi masu tattakin sai su ce mai yin ya koma, ba sa buƙata.
Akwai ma masu kallon abin a matsayin tallar kai da neman abin duniya.
Idan kun tuna, shi kan sa babban mai taimaka wa Rarara a ɓangaren soshiyal midiya, Malam Rabi’u Garba Gaya, ya faɗa wa mujallar Fim a farkon tattakin matasan biyu cewa maigidan nasa ba zai karɓe su ba idan sun iso.
Ya ce: “Magana ta gaskiya, ko sun zo ba na tsammanin za a karɓe su, duba da yadda matasa yanzu sun ɗauki wannan abu a matsayin sana’a. Gaskiya dalilin kenan.
“Sannan kuma wataƙila lokacin da za su iso garin ma ba ya nan, tunda har yanzu ba ya nan.”