GWAMNATIN Jihar Kano a yau ta bayyana matakin da ta ɗauka a game da maganar waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja da waƙoƙin da bidiyoyin da mawaƙan nan Safara’u da Mr. 442 ke saki a soshiyal midiya.
Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na-Abba (Afakallahu), shi ne ya bayyana matsayin gwamnatin a wata hira da ya yi da mujallar Fim a yau.
A hirar, Afakallahu ya ce hukumar sa ce ta farko wurin ɗaukar mataki kan Gwanja tun lokacin da wani lauya ya aika masu da takardar mai buƙatar cewa su dakatar da sakin sabuwar waƙar tasa ta ‘Warr’.
Ya ce: “Lokacin da lauyoyi su ka rubuto ƙorafi, sun rubuto wa Hukumar Tace Finafinai. Da su ka rubuto wa Hukumar Tace Finafinai, sai mu ka kirawo shi Ado Gwanja domin ya zo. A lokacin sai ya ce ba ya nan, ya na kan hanyar zuwa Ghana. To, lokacin na ba da umarnin a faɗa masa idan ya dawo ya zo, sannan kuma ya dakatar da sakin wannan waƙar saboda akwai ƙorafi a kan ta.
“Wannan shi ne abin da mu ka tsaya da shi a wannan lokacin. Amma mun samu labarin zuwan sa Ghana ya saki wannan waƙa. Don haka wannan matakin da mu ka ɗauka kenan dangane da wannan.
“Da ma kuma ita hukuma mataki-mataki ce, daga wannan za a ɗauki mataki na gaba. Da ma kuma mu na shirin ɗaukar matakin don ganin an ƙare, kuma mu tsirar da mutuncin mutanen jihar mu ta Kano tunda hurumin mu Kano ne.”
Da ya ke bayani kan lamarin Safiyya Yusuf (Safara’u) da Mubarak Abdulkarim (Mr. 442), shugaban ya ce, “Su su Safara’u mun gayyace su, amma sun ce ba su nan. Amma mun yi hira da gidan Rediyon Freedom mun kai masu ‘open invitaion’, kuma mun ce su zo.
“Akwai waɗannan waƙoƙi da irin waɗannan abubuwan da su ke saki na rashin ta-ido, ba don wani abu ba.
“Kuma kamar shi shugaban nasu, Mr. 442, ya nuna cewa ba a gayyace su ba, amma in an gayyace su za su zo. To kuma mun ba su ‘open invitation’, tunda faɗa su ka yi a gidan rediyo, kuma ‘yan gidan rediyo su ka kira mu su ka yi ‘balancing’, sai mu ma mu ka ce ga matsayar mu, mu na ƙara ba su goron gayyata.”
Afakallahu ya ce ba manufar hukumar sa ba ne ta hukunta mutum ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce: “Ba burin mu ba ne ko mu kora, ko mu ɗaure ko mu yi wani abu. Burin mu ne mu ga cewa mun kawo tsafta da gyara a kan waɗannan abubuwan na adabi, musamman waƙe-waƙen nan da ake yi da sauran su.

“Saboda duk wanda ya ga wannan abu yadda ya ke, babu wanda zai bar waɗannan abubuwa a yadda su ke tafiya; dole a ce an yi waɗannan gyararraki da sauran su. Wannan shi ne abin da aka yi.
“Wancan kuma wani mataki ne da ita Hukumar Kula da Gidajen Rediyo Da Talbijin ta ɗauka don hukunta shi Ado. Sannan ta ɗaya ɓangaren, su waɗancan lauyoyi sun kai ƙara a ‘Shari’a Court’ ta Ɗambatta, wanda alƙali ya ba da umarnin cewa ‘yan sanda su binciki waɗannan abubuwa da sauran su.”
Da mujallar Fim ta tambayi Afakallahu idan akwai wani mataki da hukumar sa ta ɗauka na ganin duk wanda ya yi waƙa kafin ya sake ta sai ya kawo wa hukumar ta tace, sai ya amsa da cewa, “Ai da ma aikin hukumar kenan. Amma abin ne ya zama cewa yanzu idan ka na Abuja za ka saki waƙa, mu kuma hurumin mu iya Kano ne, sai mu kare iya mutanen Kano.
“Ma’ana, ba za mu bari ‘yan ‘downloading’ su yi ‘downloading’ ba, ba za mu bari ‘yan gidajen kallo su haska ba, ba za mu bari a sa mana a gidajen bukukuwa ba, sannan kuma in ba ka yarda da tsarin Kano ba, ba za mu bari kai ma ka zo ka yi ‘performance’ a Kano ba, domin mu na da ‘values’ na ‘culture’ da ‘religion’ ɗin mu.”