ABDULSALAM Musa ɗan wasa ne wanda ya yi fice a matsayin Sha’aban ɗan gidan tsohon Gwamnan Jihar Alfawa, Alhaji Bawa Maikada, a cikin fim ɗin nan mai dogon zango mai suna ‘Kwana Casa’in’ wanda tashar talbijin ta Arewa24 ke nunawa.
Da farko dai, shi ma’aikaci ne a Arewa24 ɗin, inda ya ke aiki a sashen su na soshiyal midiya. Su ne su ke kula da shafukan gidan talbijin ɗin na Instagram, FaceBook, Twitter da YouTube. Haka kuma ya kan yi aiki a matsayin mai ɗora murya, wato ‘voice artist’, a tashar.
Ficen da Abdulsalam ya yi a diramar ta sa mutane su na so su san ko shi waye, don haka mujallar Fim ta yi hira da shi kwanan nan a Kano.
Abdulsalam Musa, wanda haifaffen Kano ne, ya bayyana cewa a Kano ya girma, sannan ya yi karatun sa na firamare da na sakandire duk a Kano, yanzu kuma ya shiga jami’a a Kano.
A hirar, ya faɗa mana yadda aka yi ya zama ɗan wasa. Ya ce wata rana ne aka faɗa masa cewa za a fara ɗaukar wani sabon fim, amma za a ɗauki ‘yan wasan ne ta hanyar gwaji (audition). Aka faɗa masa cewar shi ma zai iya shiga gwajin tunda ɗan gida ne. Daga nan ya cike fom, aka gwada shi, aka ga ya dace, aka ɗauke shi.
Amma kuma kafin ya fara fitowa a ‘Kwana Casa’in’ jarumin ya fuskanci ƙalubale a wajen mahaifiyar sa da kuma shi kan sa a tunanin sa. Ya ce: “Da farko da na zo na gaya mata, ba ta ba ni goyon baya ba. Amma kuma daga ƙarshe ban san ya aka yi ba ta kira ni ta ce min in je in yi, babu damuwa, Allah ya bada sa’a.
“Bayan haka kuma sai in ji a cikin rai na kamar in haƙura, wata kuma zuciyar ta na ce min kawai na yi. Tun kuma ana haka har ma abin ya bi jiki, kuma gaskiya wannan ma ina ganin ƙalubale ne a gare ni.”
Da mujallar Fim ta tambaye shi irin yanayin da ya shiga lokacin da aka dasa masa kyamara, musamman tunda wannan shi ne fim ɗin sa na farko, sai ya ce, “A gaskiya da farko na ɗan ji tsoro-tsoro amma kuma abubuwan yau da gobe wanda Bahaushe ya ke cewa ta fi ƙarfin wasa, a hankali a hankali na saba. Amma dai an sha gwagwarmaya matuƙa!”
Shin ko Abdulsalam ya yi wani fim ɗin bayan ‘Kwana Casa’in’? Amsa: ”Zan iya cewa e, don na taɓa fitowa a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ shi ma na Arewa24, wanda kuma fitowa ɗaya ne kawai inda na fito ne a matsayin wanda ya kawo ziyara situdiyon su I.B. na kuma ɗora waƙa ɗaya wannan shi ne fitowa ta ta farko a fim.”
To yaya ya ke ya na haɗa karatu da aiki?
Ya ce: “A lokacin da na fara shirin ‘Kwana Casa’in’ na gama makarantar sakandire kafin kuma na fara jami’a, amma yanzu na ci gaba kuma ba na samun wata matsala a kan karatu na saboda da man ɗaukar shirin ‘Kwana Casa’in’ su na ware mana lokacin yin sa, wanda kuma bai shafi karatu na ba. Karatu na kuma ya na tafiya daidai yadda ya kamata.”
Kazalika, jarumin ya bayyana cewa bayan fitar ‘Kwana Casa’in’ ya samu gayyata daga wasu masu shirya finafinai, amma sai dai ayyukan da ka gaban sa sun hana shi amsa gayyatar su.

“A inda na ke aiki in mun fara tun safe sai dare. Amma dai yanzu akwai wani fim da ake yi mai dogon zango wanda ina ɗaya daga cikin jaruman kuma lokacin da na ke yin wannan fim ɗin sai ranakun ƙarshen mako. Amma bayan shi ba ni da wani aikin fim da na karɓa,” inji shi.
Ya bayyana yadda rikiɗewar sa zuwa ɗan wasa ta sauya masa rayuwa. Ya ce, “Tun bayan da aka fara haska shirin ‘Kwana Casa’in’ rayuwa ta ta canza saboda yanzu ta ko ina mutane an san san ka. Za ka shiga cikin mutane kuma wannan zai so ku yi hoto, kai ko ina ka je mutane za su saka ka farin ciki ballantana waɗanda su ka san ka haka. To gaskiya ina jin daɗi sosai. Wallah in na ga haka, na kuma samu nasarori da dama wanda har wasu mutanen su kan so mu yi aiki tare.
“Sannan kuma wasu abubuwan da na ke yi a ɓoye yanzu kowa ya sani. KZa ga wannan ma babbar nasara ce. Amma ba abin da zan ce wa Allah sai godiya”.
A ƙarshe, Abdussalam ya yi jan hankali ga matasa irin sa masu tasowa. Ya ce, “Ya kamata matasa su yi amfani da damar da su ke da ita wanda za ka ga mutum ya na da damar yin abu amma saboda rashin haƙuri sai ka ga ya kasa cimma burin nasa. Kuma da man ai ba a samun nasara a kowane abu in dai ba a yi haƙuri ba.
“Sannan kuma matasa su gane cewa ba dare ɗaya ake yin arziki ba. Kamar yanzu misali, idan mutum ya na da basirar yin zane in ka na da kuɗin sayen na’ura mai ƙwaƙwalwa za ka iya saya ka shiga kafar YouTube domin ka ga yadda ake yi kuma a hankali a hankali za ka samu ɗimbin ilimi a kan abin. Kuma daga ƙarshe ka zo ka dogara da kan ka har ma ka taimaka wa wasu. In kuma waƙa mutum ya ke so ya yi, zai iya zuwa situdiyo ya yi. Kar mutum ya ji tsoro. In ma fim ne, yanzu zamani ya canza, ana sayar da fom ɗin yin gwaji, wato ‘audition’, mutum ya je ya gwada. Wata ran sai ka ga ana zancen ka kai ma a duniya.”
Allah ya bada sa’a da basira
Allah ya kara basira
Allah yabadasa`a kamafi haka