MATASHIN mawaƙi mai tasowa a masana’antar Kannywood, Albashir Hamza Yareema, shi ma ya yi bankwana da kwanan situdiyo, ya zama maigida, domin kuwa a yau ya angwance da sahibar sa, Sadiya Abdullahi Ahmad.
Shi dai Albashir, tauraron sa ya fara haske a yanzu, musamman ganin yadda ya samu shiga cikin many an mawaƙa a ƙungiyar ‘Yahaya Bello Network Group’ (YBN), inda shi ma ya zama jakadan ƙungiyar.
Kuma da ma duk wanda ya san shi, ya san cewa ya fi rayuwa a situdiyo domin yawan waƙoƙin da ya ke yi wa dillalan waƙa.
Da bakin sa ya faɗa wa wakilin mujallar Fim cewa a sati ɗaya ya kan yi waƙoƙi sama da ashirin.

To, kyakkyawar yarinya Sadiya dai ta karya ƙwarin shi na kwana situdiyo, domin kuwa a yau Juma’a, 18 ga Maris, 2022 aka ɗaura auren su da misalin ƙarfe 2:15 na rana a masallacin Juma’a na ‘yan Ɗariƙa da ke unguwar Kadaure, Kaduna, a kan sadaki N100,000.
Wasu daga cikin ‘yan Kannywood da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Jamilu Nafseen, Ibrahim Saminaka, Abban Waƙa, Yusuf Waza-waza, Abdullahi Abu Uku, Sufi Na Kowa, Maikano Bagobiri, Muhammad Show Man, darakta Aphala da Hamisu Gwamna Jaji.
A jibi Lahadi kuma za a yi gagarumar dina wadda ƙungiyar su ta YBN ta shirya don taya sabon jakadan nasu murnar wannan aure.
Hasali ma dai, jagoran ƙungiyar na ƙasa, Abdul Muhammad Amart, shi ya bada umarnin a kai dinar ranar Lahadi saboda hidimar ƙungiyar da za su yi a gobe Asabar a Kano, inda daga can za su ɗunguma zuwa Kaduna.

Ana san duk wani jarumi da mawaƙi da ya ke cikin YBN zai halarci dinar, wadda za a yi a ɗakin taro na otal ɗin NUT da ke Mogadishu Layout.
Allah ya ba Albashir da Sadiya zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

