SHAHARARRIYAR mawaƙiyar Kannywood, Hajiya Maryam Sale Muhammad, wadda aka fi sani da Maryam Fantimoti ko Mamar Mawaƙa, za ta yi aure.
Za a ɗaura auren ta da Alhaji Mubarak Jibrin Muhammad Hotoro a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Masallacin Alhaji Baƙo Barde da ke Court Road, kusa da Kotun Nafi’u.
Ga waɗanda ba su samu damar halarta ba, su yi wa ma’auratan addu’a.