• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Me Sani Moɗa ya ke ciki tun bayan yanke masa ƙafa?

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 29, 2020
in Taurari
0
Cuta ba mutuwa ba: Sani Idris (Moɗa) a gidan sa

Cuta ba mutuwa ba: Sani Idris (Moɗa) a gidan sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MALAM Sani Idris Kauru (Moɗa) ya na daga cikin manyan ‘yan wasan fim. Da shi aka fara, kuma sai da ya kai ƙololuwar shahara. Ɗan wasan, wanda babban ma’aikacin gwamnatin Jihar Kaduna ne, ya yi fice ne a ɓangaren wasan barkwanci, inda ya fito a finafinai babu adadi.
 
Labarin rashin lafiyar sa sanadiyyar ciwon suga (diabetes), wanda ya kai ga har aka yanke masa ƙafar sa ta hagu a cikin 2019, ba sabon abu ba ne. Abin tambaya a yanzu shi ne halin da jarumin ya ke ciki tun daga lokacin. Shin ya warke gaba ɗaya? Shin ya dawo harkar fim? Menene ra’ayin sa kan halin da masana’antar Kannywood ta ke ciki, musamman lalacewar kasuwancin finafinai? Ko akwai wata mafita da ya hango wa industiri?
 
Wakilin mujallar Fim, ABBA MUHAMMAD, ya tattauna da Moɗa kwanan nan a Kaduna kan waɗannan tambayoyi, shi kuma ya amsa su da kyau.
 
 
FIM: Tun bayan yanke maka ƙafa da aka yi, ya mu’amalar ka ta ke tsakanin ka da abokan sana’ar ka?
 
SANI MOƊA: Alhamdu lillahi! Ina godiya ga dukkan ƙungiyoyin shirya finafinai saboda sun kyautata mani a yayin da na samu wannan lalura. Kuma shi ya sa Annabi Muhammadu S.A.W. ya ce idan ka na son ƙima daga jama’a, ka guji abin hannun su. A wannan lokacin gaskiya sun yi mani adalci, saboda sun ga  yanayi da lalurar da na shiga. Har bayan dawowa na gida an samu ƙungiyoyi da dama waɗanda ba ‘yan fim ba ne, kamar ‘yan ajin Northern Hibiscus waɗanda su ka kawo mani ziyara tun daga Abuja su ka ba ni tallafin su. Ka ga waɗannan ba ƙungiya ba ne na fim. 
 
Bayan su, akwai ƙungiyoyi na fim da dama waɗanda wasu sun taso daga Kano saboda su duba ni, wanda a wannan lokacin in zan iya tunawa da Abba Miko Yakasai da Usman Mu’azu za su rasu a haɗarin da su ka yi, a dalili na ne, tunda a wannan lokaci sun nemi furodusoshi da daraktoci sun haɗa kuɗi za su kawo mani gudunmawa su ka samu wannan haɗarin. Ka ga akwai kyakkyawar alaƙa da kyautatawa a tsakanin mu da juna.
 
Gaskiya ban san cewa na yi kyakkyawan gini tsakani na da mutane ba sai da wannan abu ya same ni. Saboda haka masana’antar shirya finafinai ta Hausa ta gina mani abin da ban yi tunani ba. 
 
Ka ga wani ma ba zai ɗauka na yi nisa a aikin gwamnati ba, kuma har na kai kusan mataimakin darakta a aikin gwamnati. Amma ka ga bisa ga harkar fim ne aka san ni sai ya zamana cewa rububin da tallafi da abubuwa ya fi ƙarfi kashi casa’in cikin 100 harkoki ne na finafinai. Wannan abu ya faranta min rai sosai. 
 
Akwai wasu da su ka zo, mun kai shekara 15 ba mu haɗu ba sai a wannan lokacin. Sai ya kasance su su na kuka, ni ke ba su haƙuri.
 
Ina godiya ga ‘yan fim ‘yan’uwa na, musamman mutane na na nan Kaduna, waɗanda kusan kowane lokaci za ka ga sun yi runduna-runduna su na zuwa wuri na a asibiti a lokacin. Haka har gida, ka ga wannan ne ma zan ce na gida ne, kullum ina tare da su. Allah ya bar mu tare.
 
Sani Moɗa tare da ɗan shi
 
FIM: Bayan wannan lalura da ta same ka, ka ci gaba da yin fim?
 
MOƊA: Gaskiya ban ci gaba da harkar fim ba, amma a bisa dalilai guda biyu. Dalili na farko, su waɗanda zan yi aikin da su, a tunanin su ban kai lafiyar da zan yi aikin ba. Na biyu, ni kai na ina so na ga na samu kulawa ta jiki na, domin shi ciwon suga ba kamar na mai ƙanjamau ba ne, shi ka na iya yawo tare da shi ba kowa ya san ka na da shi ba. Mu kuma ka ga yanayin lalurar mu, musamman idan ka samu rauni, matsala ce a jikin mu; jikin mu kamar na maciji ne, ba mu buƙatar rauni. 
 
Maganar gaskiya, ban tuntuɓe su ba, kuma su ma ba su tuntuɓe ni ba. Sai dai a kwanakin baya na ga an tura mani saƙo ta WhatsApp cewa za a yi ‘audition’ na masu wasannin barkwanci a Mogadishu (wata unguwa a Kaduna). Gaskiya ko kallo ban je wurin ba saboda na san ba zan yi ba ko sun sanya ni. 
 
Ka ga wani lokacin na kan yi yawo da ƙafafuwa na guda biyu, da wancan da aka yi mani ina yawo tare da shi. Wani lokacin kuma na kan aje shi, saboda ita ɗaya ƙafar a halin da mu ke ciki yanzu ita mai lafiyar za ka ga kamar na ƙone, ita kan ta ina jinyar ta ne yanzu, shi ya sa a jiya na ce maka na je Asibitin Garkuwa.
 
FIM: Akwai wani shiri da ka ke da shi na karan kan ka game da harkar fim?
 
FIM: Shirin da na ke da shi, na samu shawarwarin mutane. Akwai wani aboki na ya ce mani, “Kamar yanzu ba ka da sha’awar ci gaba da harkar fim.” Sai na ce masa, “Duniya sun san ni a kan ta ne, don haka ba na iya barin ta, kuma ɗan bori ba ya kallon bori!” Sai ya ce mani me ya sanya ba zan buɗe (shafi a) YouTube ba? Na ce masa haka ne. Ka ga kamar Asu Baba Comedian, yawancin abubuwan da ya ke sakawa a YouTube ɗin sa, ni na ke rubuta masa. Wannan shi ne tsarin abin da ya cusa min ra’ayi, kuma zan yi.
 
FIM: In ka daina fitowa a cikin fim, ko za ka iya komawa furodusa?
 
MOƊA: Haƙiƙa, kamar yadda na faɗa maka, zan fara da wannan. Lallai ina da kyakkyawar alaƙa har da wani ‘script’ da na rubuta shi. Bari in gutsura maka kaɗan.
 
Tashin farko za a ga saurayi ya sauke budurwar sa a ƙofar gida tare da kayan da su ka yi ‘shopping’, domin da safe – gobe kenan – za a ɗaura auren su. Sun yi sallama, an yi irin dai Allah ya kai mu gobe in an ɗaura aure duk abin da za a yi za a san yadda za a yi, da dai irin wannan abubuwan. An ɗaura auren, kuma aure ne wanda aka yi duk duniya soyayya a wannan ƙauyen ba a yi irin wannan ba. Bayan an ɗaura aure, da zarar ya shigo ɗakin sai ta fashe da kuka. Ya faɗa wa mahaifan sa, ya faɗa wa iyayen ta, don a ga abin da za a yi. In ta na zaune da ƙawayen ta in ta ji muryar sa sai ta gudu ta shiga uwar ɗaka, kawai kuka ta ke yi. To menene dalilin wannan kukan? Daidai nan zan bar ka, ni zan faɗa maka dalili nan gaba.
 
FIM: Me za ka ce game da halin da masana’antar shirya finafinai ta ke ciki na durƙushewar kasuwar ta da wasu harkoki?
 
MOƊA: Mu ‘yan wasa da za mu je a biya mu, mu yi aiki mu dawo, ba mu ne matsalar ba. Domin duk wanda ya je ya yi aiki aka biya shi, daga nan ya rage naka ko ka ci riba ko ka faɗi. Amma furodusoshin mu su su ka buɗe wata kafa a wannan lokaci, wanda ga shi kowa ya koma ya na kokawa. Da ka kai fim ɗin ka kasuwa, gara ka ɗora shi a YouTube ya tafi yawo. Dalili shi ne su ‘yan kasuwan a wannan lokacin sun buɗe kafar da su za su ce maka ba su son Sani Moɗa a wannan fim ɗin, “ka sa mana wane da wane”. Kuma kuɗin ka ne fa, amma su za su yi maka ‘casting’! Da haka aka yi ruwa aka yi tsaki aka fara karya kasuwar. Sai ya zamana cewa kai Abba za ka kai kayan ka kasuwa, ni zan kai kaya kasuwa, idan ina da ƙafa sai in je in karɓi kuɗi na, kai kuma kai ta wahala har sai ka koma ka na roƙo. Me ya kawo haka? Saboda furodusoshin sun riga da sun bada kan su. Da su ka ga haka, sun riga da sun  kafu sun yi kuɗi, sai su ka ce bari su fito da wasu dabaru. Sai aka ce ‘Algaita’ ya fito, ‘Mai Duma’ ya fito, ‘Kaaki’ ya fito, ‘Mai Kazagi’ ya fito, ‘’Yan Kwambe’ sun fito, fassarori ga su nan daban-daban. Saboda haka da in je in sayi fim ɗin ka N200, bari in bada N70 in sayi fassarar Indiya ko N50. In ka fitar da fim ɗin ka, ka raba kwali da sauran su, ɗan fairesi (‘piracy’) sai ya saida kwafi dubu hamsin, kai ba ka saida kwafi dubu biyar ba! Kuma babu wani mataki da aka ɗauka. In sun koma sun je su na kame, kafin su ƙaraso an faɗa masu (su ‘yan faireshin): “Rana kaza za a zo Kaduna, duk ku gudu ku ɓoye!”
 
FIM: Ta ina ka ke ganin za a shawo kan wannan matsalar?
 
MOƊA: Gwamnati ce kawai za ta iya wannan aikin. Ta shigo dumu-dumu ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki. Ai akwai hukuma guda a kan fairesi.
 
Fairesin nan gumin wani ne; ya sha rana, ga ruwa, ga raɓa, ga iska, ga yunwa ka sha, duk don ka so ka ga ka biya buƙatun ka, amma wani rana tsaka, mutum zai saida kwafi dubu goma, kai ba ka saida kwafi ɗari biyar ba. Kuma za ka kai kasuwar ma a ci maka mutunci. 
 
Akwai lokacin da na je zan taro yaro na zai dawo daga Legas, motar da ya biyo haka na ga ana ta sauke finafinai buhuna-buhuna na fairesi. Sai na kira wani ‘police’ na ce masa, “Ka ji abin da ke faruwa.” Ashe shi ma ya zo neman nashi ne! Na kira Rabi’u HRB (furodusa) na ce masa ga halin da ake ciki, ga lokacin da su ke sauke kayan nan; da asuba su ke shigo da kayan nan. A nan ma wani zai kasa kayan ya saida su kafin ya shiga kasuwar.
 
Saboda Allah akwai abin da ya fi wannan zalunci? In gwamnati ta ga dama, za ta iya hanawa. Amma kuma ba za a yi haka ba, in ma an yi sai a ce ‘yan ‘human right’ sun shigo ciki, za a shiga haƙƙin ɗan’adam! Amma kuma ba za su shigar wa mutane ba su ce, “Don me ake ɗaukar kayan su ake satar fasahar su?” Su sun fi ƙarfi kan harkar zalunci. Yau yaro za a kama ya kashe wani, da zarar an yanke masa hukuncin kisa, sai su ce su na da ‘interest’ a kan kes ɗin. 
 
In dai gwamnati ba za ta shigo ciki ba, ko nawa za ka kashe a aikin ka, wallahi asarar su za ka yi.

Loading

Previous Post

Afakallah: Abin da ya sa Adam Zango ya yi mubaya’a

Next Post

Yadda jaruma Fadila (Ummi Lollipop) ta rasu: Hira da mahaifin ta

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Fadila (Ummi Lolipop) a sama. Hoto na ƙasa kuma Mahaifin ta ne a tsaye a gaban kabarin ta

Yadda jaruma Fadila (Ummi Lollipop) ta rasu: Hira da mahaifin ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!