• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Me ya sa ba a ga wasu manyan jarumai a taron AKAFA ba?

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 26, 2022
in Nijeriya
0
Mata adon biki ... taron AKAFA

Mata adon biki ... taron AKAFA

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JIM kaɗan bayan kammala taron ƙaddamar da Ƙungiyar Jarumai Mata ta Kannywood (Association of Kannywood Female Artistes, AKAFA) a ranar Asabar da ta gabata a Kano, mutane su ka fara tsegumi dangane da jaruman da su ka je taron da waɗanda ba su je ba. Ganin yadda hotunan taron su ka bazu, duk wadda ta je wajen fuskar ta ba za ta ɓuya ba.

Taron dai na mata zalla ne; duk namijin da aka gani a wajen to wani aiki na musamman ya kai shi.

Sanarwar da mashirya taron su ka bayar ta ce ba a ɗauke wa duk wata mace da ta ke cikin masana’antar zuwa taron ba, tun daga kafuwar Kannywood shekaru 30 zuwa yanzu, wala’alla mai aure ce ko bazawara ko budurwa, kai har ma da ‘ya’ya da jikokin su.

Matan Kannywood a taron ƙaddamar da ƙungiyar su

To sai dai abin da mutane su ka riƙa tambaya a kai shi ne me ya sa ba a ga fuskokin waɗansu manyan jaruman Kannywood da ake yayin su a yanzu a wajen taron ba? Wato irin su Nafisa Abdullahi, Fati Washa, Teemah Makamashi, Hadiza Gabon, Ruƙayya Dawayya, Rahama Sadau, A’isha Tsamiya, Rahama Hassan, Jamila Nagudu, Hannatu Bashir, da kuma uwa-uba shugabar Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeriya (K-WAN), Hauwa Bello (Edita).

Binciken da mullar Fim ta gudanar ya tabbatar da cewa wasu jaruman syn so zuwa taron amma wani uziri ya hana su, yayin da wasu kuma ba su je ba saboda rashin jituwar da ke tsakanin su da masu shirya taron. Majiya ta ce Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya da Rahama Hassan sun so zuwa amma wani dalili ya hana su. Misali, aikin fim ɗin ‘Gidan Badamasi’ ne ya hana Gabon zuwa. Amma dukkan su sun bada gudunmawar kuɗi masu yawa domin gudanar da taron.

Su kuwa su Nafisa Abdullahi da Rahama Sadau, mutane ne waɗanda shiga sabgar ‘yan fim ba ta dame su ba, don ko bikin aure ko ta’aziyyar ‘yan fim ba su zuwa. “Kuma su na ganin kamar sun fi ƙarfin zuwa wajen taron da ‘yan fim su ka shirya,” inji wani ɗan fim, wanda ya ƙara da cewa, “Su kawai sai dai idan wani babban kamfani ne ya shirya taro, to shi ne su ke ganin wajen zuwan su ne.”

Ita kuwa Hauwa Edita, an ce abin da ya hana ta zuwa saboda an yi wa ƙungiyar ta ta K-WAN kishiya, ko kuma ana neman kashe ƙungiyar ta. Wata majiya ta ce an gayyace ta zuwa taron. Hannatu Bashir kuwa makusanciyar Hauwa Edita ce ta ƙut da ƙut, “don haka ta tsaya yi mata dannar ƙirji”, inji mai ba mu labarin. Ya ƙara da cewa, “Kuma ma, ita wata babbar ƙusa ce a K-WAN.”

Halisa Muhammad ma ba ta je taron ba duk da yake ta kan halarci duk wani taro da matan Kannywood su ka shirya saboda yawancin su su na ba ta matsayin babbar yaya ko kuma uwa.

Ita ma Teemah Makamashi ba ta je ba duk da kusancin da aka san akwai tsakanin ta da Rashida Maisa’a, wanda ya sa a da ko’ina su na tare. An ce tarayyar su ta ƙara ƙulluwa ne saboda yayan Rashida ya na neman Teemah ɗin har ana maganar auren su ya kusa. Hasali ma dai, tare da Teemah aka yi fafutikar kafa ƙungiyar AKAFA ɗin.

Jarumai mata a taron rantsar da shugabanni da ƙaddamar da AKAFA

Binciken mujallar Fim ya gano cewa dangantakar su ta yi tsami daga baya har ta kai ga sun rabu dutse a hannun riga, musamman bayan ɓatawar Teemah da yayan Rashida. “Hakan ya sanya sai Rashida ta fitar da ita daga guruf ɗin WhatsApp na ƙungiyar, ta maye gurbin ta da Sadiya Haruna, wadda kuma ka san ba sa shiri da Teemah Makamashi,” inji wata jaruma da ta ce mu sakaya sunan ta.

A yanzu dai an zura ido a ga yadda tafiyar AKAFA za ta kasance. Masu lura da al’amuran industiri sun nuna cewa irin salon tafiyar shugabancin AKAFA ne zai tabbatar da ɗorewar ƙungiyar ko akasin haka. Da yawa ‘yan fim dai su na yi wa ƙungiyar fatan alheri, su na nuni da cewa tarin jarumai mata da su ka halarci taron ƙaddamarwar da rantsar da shugabannin ya nuna cewa matan Kannywood su na goyon bayan kafa AKAFA.

Shugabar AKAFA, Rashida Adamu Abdullahi, ta na jawabi
Daga hagu: Aina’u Ade, Mansurah Isah, Rashida Maisa’a, Baballe Hayatu, da Samira Ahmad a taron

Loading

Tags: AKAFAAssociation of Kannywood Female ArtistesHannatu BashirHauwa EditaK-WANKannywood womenKanoƘungiyar Jaruman Kannywood Matamatan KannywoodRashida Adamu AbdullahiTeemah Makamashi
Previous Post

Raliya ta cikin ‘Daɗin Kowa’ ta zama amarya

Next Post

Zan nuna ƙwarewa, inji Rahama Sadau bisa gayyatar ta zuwa shirya sabon fim ɗin Bollywood a Indiya

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Rahama Sadau: "Al'adar Indiya na yin kama da tamu"

Zan nuna ƙwarewa, inji Rahama Sadau bisa gayyatar ta zuwa shirya sabon fim ɗin Bollywood a Indiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!