KAMAR dai yadda aka saba yaɗa cewa wani daga cikin ‘yan fim ko mawaƙi ya rasu a soshiyal midiya, haka ma a wannan karon an ga wani gajeren bidiyo ya na yawo ɗauke da saƙon cewa wai fitaccen mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi ya rasu sakamakon haɗarin mota.
A cikin bidiyon an saka hotunan Hamisu Breaker, sannan aka ɗora wata waƙa da fitaccen mawaƙi Sadi Sidi Sharifai ya yi ta ta’aziyyar marigayi Ahmad S. Nuhu, sannan aka rubuta RIP a cikin hotuna tare da saka wata mota da aka yi haɗari da ita da wani hoto da ke nuni da an saka gawa a cikin kabari.
Sai dai mujallar Fim ta yi bincike a kan wannan al’amari, kuma ta gano cewa ‘yan soshiyal midiya ne kawai su ka ƙirƙiri bidiyon su samu mabiya a shafukan su.

Kuma da ma wannan ba shi ne karo na farko da aka fara yi wa ‘yan Kannywood haka ba. Ana ma iya cewa ɗaiɗaiku ne daga cikin ‘yan fim ba a yi masu irin wannan sharrin ba. Don haka wannan labarin ƙanzon kurege ne.
Wakilin mu ya yi ƙoƙarin ji ta bakin mawaƙin, sai dai hakan bai yiwu ba, don ya kasa samun sa a waya.