• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista na so ‘yan kasuwa su zuba jari don haɓaka shirin iskar gas na CNG

by DAGA IRO MAMMAN
January 2, 2024
in Nijeriya
0
Minista na so ‘yan kasuwa su zuba jari don haɓaka shirin iskar gas na CNG

Daga hagu: Abokin haɗin gwiwa, Mohammed El-Gawish; Minista Alhaji Mohammed Idris, da Ciyaman na ABG Group, Alhaji Bawa Garba, a wurin ƙaddamar da masana'antar ABG CNG Plant tare da yaye injiniyoyin CNG su 40 a ranar Talata a Abuja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su kasance kan gaba a shirin nan na Gwamnatin Tarayya na yin amfani da Matsattsiyar Iskar Gas (Compressed Natural Gas, CNG) a ƙasar nan.

Hadimin Musamman kan Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya faɗa a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa ministan ya furta haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin ƙaddamar da masana’antar iskar gas ta ABG CNG tare da yaye injiniyoyin 40 da su ka ƙware a harkar sarrafa CNG ɗin.

Idris ya ce wannan ƙoƙari da rukunin kamfanonin ABG Group ya yi abu ne wanda ya dace kuma ya zo a kan kari.

Haka kuma ya ce amfani da matsattsiyar iskar gas wani abu ne wanda ya zo kenan kuma shi ne hanyar rage kashe kuɗi a ɓangaren harkar sufuri.

Idris ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya jagoranci yadda za a koma ana amfani da iskar gas ta CNG a maimakon man fetur a motocin haya da ƙanana na shiga.

Ya ce: “Iskar gas ta CNG ita ce za a riƙa amfani da ita nan gaba, don haka ya na da muhimmanci ga ‘yan kasuwa a Nijeriya su yi amfani da wannan damar ta shirin gwamnati kan CNG ɗin ta hanyar zuba jari na ɗaukar ma’aikata da sayen kayan aiki da ake buƙata don haɓaka sashen a duk faɗin Nijeriya.”

Ministan ya bayyana cewa ya zuwa yanzu har gwamnatin Tinubu ta kasafta naira biliyan 100 a matakin farko ga harkar gas ɗin CNG, kuma ma har ga shi Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi na’am da shirin CNG ɗin wanda hakan ya taimaka wajen sanyin da ta yi kan maganar da ke tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya) a wajen taron

Shugaban rukunin kamfanonin ABG Group, Alhaji Bawa Garba, a nasa jawabin, ya ce amfani da iskar gas ta CNG wani maganin matsala ne salin alin wanda ya ke buƙatar goyon baya da ciniki daga gwamnati idan har ana so ya faɗaɗa har a riƙa yi wa Nijeriya kallon “Ƙasar Iskar Gas.”

Ya ce: “Kamfanin mu ya na godiya ga Shugaba Tinubu saboda bajintar da ya yi wajen yanke shawarar a riƙa yin amfani da CNG. Mu da ma can kamfani ne wanda ke fara yin abu, don haka shaidar shigar mu cikin tsarin CNG ita ce yadda mu ka horas da ɗimbin injiniyoyin sauya CNG a faɗin Nijeriya.”

Loading

Tags: ABGAlhaji Bawa GarbaCNGcompressed natural gasiskar gasMohammed Idrissufuri
Previous Post

Gwarzon dimokiraɗiyya: Hukumar zaɓen Laberiya ta karrama shugaban INEC

Next Post

Daraktan Kannywood Kamal Alƙali da tsohuwar jaruma Hauwa Garba sun samu ɗa namiji

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
Daraktan Kannywood Kamal Alƙali da tsohuwar jaruma Hauwa Garba sun samu ɗa namiji

Daraktan Kannywood Kamal Alƙali da tsohuwar jaruma Hauwa Garba sun samu ɗa namiji

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!