• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin bai wa matasan N-Power sama da 460,000 tallafin aikin gona

by DAGA WAKILIN MU
March 15, 2022
in Nijeriya
0
Matasa a wajen taron

Matasa a wajen taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da wani sabon shiri domin tallafa wa matasan da su ka ci moriyar shirin nan na N-Power domin su samu jarin shiga sana’ar aikin gona.

Shirin, wanda aka jima ana jiran sa, ma’aikatar za ta aiwatar da shi ne tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Nijeriya (CBN), kuma waɗanda su ka ci moriyar kashi na ‘A’ da na ‘B’ na N-Power ne za su fara amfana da shi.

A wajen bikin ƙaddamar da shirin wanda aka yi a Cibiyar ‘Yan Jarida da ke Radio House a Abuja a ranar Litinin, an bayyana cewa daga cikin mutane 467,183 da aka horas, waɗanda kuma su ka nuna sha’awar shiga shirin, an zaɓi mutum 75,600 da za a fara yi wa bita wanda daga baya za a ba kowannen su rancen kuɗi har na naira miliyan 3 daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin ya ja jari idan an ga ya cancanta.

A wajen bikin ƙaddamarwar, ministar, wadda Babban Sakatare na ma’aikatar ya wakilta, wato Alhaji Bashir Nura Alƙali, ta gode wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari saboda ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi ba ji ba gani don rage fatara da yunwa a ƙasar nan da kuma tallafin da ta ke ci gaba da bai wa Tsare-tsaren Inganta Rayuwa na Ƙasa (NSIP).

Alhaji Bashir Nura Alkali

Haka kuma ta taya mutane 467,183 da aka horas murna, wato waɗanda su ka nuna sha’awar shiga shirin mai suna NEXIT CBN AGSMEIS daga cikin mutum 500,000 da aka yaye a kashi na ‘A’ da na ‘B’. 
Hajiya Sadiya ta bayyana cewa wannan shi ne mataki na farko daga cikin sauran matakai daban-daban da za a gudanar a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da Gundumar Birnin Tarayya (FCT).

Ta ce: “Buri na ne a ko yaushe in ga cewa ‘yan kashi na ‘A’ da na ‘B’ na shirin N-Power da aka yaye ba a bar su haka nan kara-zube ba. A wurare da dama, na sha bada tabbaci ga waɗannan ɗimbin matasa waɗanda  Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta sha fama tare da Babban Bankin Nijeriya ta horas da su sun cimma wannan muradin.

“A yau an kawo gaɓar da za a soma cika burin kammala wannan bitar domin a bada dama ga waɗanda su ka ci moriyar shirin kuma su ka nuna sha’awar su ta shiga sabon tsarin tallafi wanda CBN ya kawo.

“Domin a samu sauƙin gudanarwa, za a aiwatar da wannan shirin bitar ne mataki-mataki. Bari kuma in shaida maku cewa dukkan jihohi 36 da yankin Abuja sun shiga cikin wannan shiri na NEXIT da aka daɗe ana jiran sa.

“Jimillar mutum 75,600 su ka shiga cikin wannan kashi na farko na horaswar. Za mu ci gaba da horas da sauran kashi-kashin nan ba da jimawa ba.

“Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta sadaukar da kan ta wajen tabbatar da cewa an cimna nasarar aiwatar da dukkan manyan shirye-shiryen da aka kawo don tallafa wa al’umma domin a cimma muradan da aka tsara.

“​Shirin N-Power wani babban ɓangare ne na Tsare-Tsaren Inganta Rayuwa na Ƙasa waɗanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta ke gudanarwa da nufin cimma muradun ƙasa na rage fatara tare da samar da aikin yi.

“Shirin N-Power shi ne hanyar da za a bi a taimaki matasan Nijeriya su samu horarswar da za su gyara rayuwar su domin ganin sun kasance masu warware matsaloli kuma masu sana’ar kan su a cikin al’ummar su.”

A jawabin maraba da ya gabatar a taron, Babban Sakataren ma’aikatar, wanda Daraktan Tsare-Tsare, Bincike da Alƙaluma a ma’aikatar ya wakilta, wato Mista Raphael Oraeluno, ya hori masu cin moriyar shirin da su yi amfani da wannan dama da su ka samu da idon basira.

Dakta Umar Bindir

Ya ce: “Ina so in jaddada cewa tilas ne kowane mutum da aka horas ya kalli wannan dama ta musamman a matsayin wani alheri wanda ba zai banzatar da shi ba. Ku tuna da tafiyar da mu ka yi kafin mu zo wannan gaɓa. Kun fa samu wannan dama a ƙarshe. Ku maida hankali matuƙa a dukkan abin da za a koya maku a duk tsawon bitar da kuma bayan ta. A matsayin ku na masu cin moriyar shirin, za a ba ku dukkan horaswar da ku ke buƙata wanda zai ba ku garantin shiga cikin tsarin da CBN ya tanadar domin cimma wannan manufa.”

Shi ma Kodinetan Ƙasa na Tsare-Tsaren Inganta Ryuwa na Ƙasa (NSIP), Dakta Umar Bindir, ya shawarci masu cin moriyar da su yi amfani da tsarin na CBN kuma su zama masu dogara da kan su.

A ƙarshen bitar ta kwana biyar, za a ba masu cin moriyar, waɗanda su ka cancanta, rance har na naira miliyan 3 kowannen su kuma na wa’adin da bai haura shekara bakwai ba.

Mista Raphael Oraeluno
Jami’an ma’aikatar da matasan N-Power a wurin taron

Loading

Tags: Bashir Nura AlkaliMinistry of Humanitarian AffairsN-PowerNEXIT-CBNRaphael OraelunoSafiya Umar FarouqUmar Bindir
Previous Post

Ƙarshen tika-tika, tik! Halliru Ɗanmagyazo ya zama angon Firdausi

Next Post

INEC ta ƙara inganci, masu maguɗi ba za su ci kasuwa a ranar zaɓe ba, inji shugaban Kiristoci

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Rabaran Fada Polycarp Lubo

INEC ta ƙara inganci, masu maguɗi ba za su ci kasuwa a ranar zaɓe ba, inji shugaban Kiristoci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!