• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

by DAGA WAKILIN MU
May 27, 2023
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq na miƙa ragamar Ma'aikatar ta ga Dakta Nasir Sani-Gwarzo

Hajiya Sadiya Umar Farouq na miƙa ragamar Ma'aikatar ta ga Dakta Nasir Sani-Gwarzo

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta miƙa ragamar gudanar da ayyukan ma’aikatar ga Babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, bayan ta kammala aikin ta cikin gagarumar nasara.

Hajiya Sadiya ta riƙe ma’aikatar ne a matsayin ministar ta ta farko har tsawon shekara uku da rabi inda ta yi wa al’umma aiki tuƙuru babu gajiyawa.

Hajiya Sadiya ta miƙa wasu takardu ƙunshe a cikin kundaye biyu da ke bayyana ayyukan da ta yi a ma’aikatar a ranar Juma’a a Abuja, a ƙarshen Taron Duniya kan Ayyukan Agaji na Nijeriya (wayo Nigerian International Humanitarian Summit) karo na farko wanda ma’aikatar ta ɗauki nauyin shiryawa.

A jawabin da ta yi a taron, ministar ta gode wa Babban Sakataren da daraktoci da ma’aikatan ma’aikatar da na ofishin ta saboda gagarumin goyon bayan da su ka ba ta a dukkan tsawon wa’adin riƙe muƙamin ta.

Hajiya Sadiya Umar Farouq ta kuma yi kira ga ma’aikatan da su tsaya tsayin daka kan ƙoƙarin da su ke yi na ganin an cimma nasara a muradin Shugaba Muhammadu Buhari na ‘yanto ɗimbin marasa galihu daga ƙangin fatara da yunwa.

Ta ce: “Ga ni a yanzu ina miƙa waɗannan takardun masu ƙunshe da bayanan riƙon ragamar da na yi a matsayin Ministar farko ta Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa a cikin shekaru uku da rabi da su ka gabata. Na gode maku ƙwarai da gaske saboda goyon bayan da ku ka ba ni, a yau kuma na ke miƙa ragamar ga Babban Sakatare, Dakta Nasir Sani- Gwarzo”.

Da ya ke mayar da martani, Babban Sakataren ya gode wa Ministar, sannan kuma ya yi mata fatan alheri a duk inda ta sa gaba a shekaru masu zuwa.

Loading

Tags: Harkokin JinƙaiHumanitarian Affairsmiƙa ragamaMuhammadu BuhariNasir Sani-GwarzoSadiya Umar Farouq
Previous Post

Kabiru ƙanen Adam Zango ya angwance da Umaima

Next Post

An ɗaura, jarumin Kannywood Sadiqu Artiste da Amina sun zama ɗaya

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ango da amarya tare da su Teema Yola da Momee Gombe a wajen dina

An ɗaura, jarumin Kannywood Sadiqu Artiste da Amina sun zama ɗaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!