• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 26, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mista Gambaryan maƙaryaci ne, ku yi watsi da shi – Gwamnatin Nijeriya  

by IRO MAMMAN
February 14, 2025
in Nijeriya
0
Mista Gambaryan maƙaryaci ne, ku yi watsi da shi – Gwamnatin Nijeriya  

Mista Tigran Gambaryan a kotu lokacin da EFCC ta gurfanar da shi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta ƙaryata zargin da Ba’amurken nan Mista Tigran Gambaryan ya yi kan wasu jami’an gwamnatin Nijeriya, tana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da yaudara.

Gambaryan dai jami’in kamfanin Binance ne daga Amurka, wanda hukumar EFCC ta gurfanar a Nijeriya a 2024 bisa almundahanar kuɗi.

Kwanan nan ne Gambaryan ya fito ya ce wai Mashawarci na Musamman kan Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya taɓa neman ya karɓi toshiyar baki ta miliyoyin kuɗi a hannun sa don kamfen ɗin siyasar sa, amma haƙar sa ba ta cimma ruwa ba.

Haka kuma ya ambaci cewa wasu ‘yan Majalisar Tarayya guda uku sun nemi ya ba su toshiyar baki ta dala miliyan ɗari da hamsin ($150m).

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a wannan Juma’ar, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati ta san da ji-ta-ji-tar da Gambaryan yake yaɗawa, amma ba ta so ta mayar masa da martani duba da irin matsayar diflomasiyya da ta kai ga warware shari’ar sa.

Sai dai ya ce dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama.

Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne da kan su ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin hanci a lokacin, sai aka buɗe bincike nan take, ko da yake babu wanda ya shigar da ƙorafi kai-tsaye.”

Ya bayyana cewa ziyarar Gambaryan ta biyu ta kasance wani ɓangare na bincike kan yadda ake amfani da kamfanin hadahadar kuɗi na Binance don sarrafa darajar naira.

Ya ce amma binciken ya gamu da cikas sakamakon dabarun da Gambaryan da tawagar sa suka yi amfani da su.

Ministan ya ƙara da cewa Gambaryan ya samu ‘yanci a watan Oktoba na 2024 bisa dalilai na jinƙai, bayan cimma matsaya tsakanin Nijeriya da Amurka da ta kawo fa’ida ga Nijeriya.

Ya kuma ce gwamnati ta yi watsi da tayin da Binance ya yi na biyan dala miliyan 5 domin a saki Gambaryan, inda ta amince da wata yarjejeniya mai amfani da gwamnatin Amurka.

“Muna ƙaryata duk wata magana da Mista Gambaryan ke yi kan jami’an gwamnati da ke da hannu a shari’ar sa, kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan ƙarairayi baki ɗaya,” inji Idris.

Ministan ya bayyana cewa zargin da Gambaryan ke yi babu hujja, kuma bai da inganci duba da cewa yana ƙoƙarin ɓata suna da razana waɗanda suka tabbatar an gurfanar da shi a gaban shari’a ne.

Ministan ya ce yana da yaƙinin cewa tsarin shari’a na Nijeriya da na Amurka za su ba Gambaryan damar gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi.

A halin yanzu, ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi hankali kada su faɗa tarkon waɗannan ƙarairayi da ƙazafi da wannan Ba’amurken yake yaɗawa.

Tigran Gambaryan a kotu lokacin da EFCC ta gurfanar da shi

Loading

Tags: BinanceEFCCMohammed IdrisNuhu RibaduTigran Gambaryanyaƙi da cin hanci
Previous Post

Hoto: Jami’an Gwamnati Suna Jiran Isowar Shugaban Nijeriya A Habasha

Next Post

Hotuna: Shugaba Tinubu tare da sauran shugabannin Afrika a taron Addis Ababa

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
Hotuna: Shugaba Tinubu tare da sauran shugabannin Afrika a taron Addis Ababa

Hotuna: Shugaba Tinubu tare da sauran shugabannin Afrika a taron Addis Ababa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!