SABON Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Maikuɗi Umar (Cashman), ya miƙa saƙon ban-gajiya tare da neman haɗin kan ‘yan Kannywood.
A takardar saƙon mai ɗauke da sa hannun sabon Sakatare-Janar na Ƙungiyar, Malam Muhammad Ibrahim Gumel, wadda ya fitar a ranar Laraba, 29 ga Janairu, ya ce, “A madadin ‘yan majalisa ta, ina yi wa dukkan waɗanda suka halarci zaɓe da aka yi a garin Lafiyar Jihar Nassarawa ban-gajiya da fatan kowa ya koma gida lafiya.”
Ya kuma ce, “Muna neman haɗin kan kowa da kowa don samun nasarar mulkin mu. Yanzu zaɓe ya wuce, don haka kowa ɗaya ne a wajen mu.”
Ya ƙara da cewa, “Yanzu haka muna nan muna tsare-tsaren nauyin da kuka ɗora mana.”
A ƙarshe, Cashman ya ce, “A shirye muke da mu karɓi shawara ko gyara daga duk wani ɗan wannan masana’antar da kuma neman addu’o’in ku.”
An zaɓi Cashman ne a matsayin Shugaban MOPPAN na ƙasa, a ranar Asabar, 18 ga Janairu, 2025, a Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa, inda ya kada abokin takarar sa, Alhaji Adamu Muhammad Bello (Ability). Dukkan su ‘yan Zariya ne.

Sauran waɗanda suka samu nasara a zaɓen su ne:
Mataimakin shugaba (Arewa ta tsakiya): Alhaji Bala Kufaina
- Mataimakin Shugaba (Arewa maso yamma): Shehu Hassan Kano
- Mataimakin Shugaba (Arewa maso gabas): Hamza Baba Muri
- Sakatare-Janar: Muhammad Ibrahim Gumel
- Mataimakin Sakatare: Nasir Umar Gwandu
- Ma’aji: Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj)
- Sakataren Kuɗi: Lawan Ahmad
- Jami’in Hulɗa Da Jama’a na 1: Ibrahim Amarawa
- Jami’in Hulɗa Da Jama’a na 2: Murtala A. Hassan
- Mai Binciken Kuɗi na 1: Hayatudeen Yakubu
- Mai Binciken Kuɗi na 2: Haruna Talle Maifata
- Jami’ar Walwala: Wasila Isma’il