ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), ƙarƙashin jagorancin Alhaji Habibu Mohammed Barde, ta miƙa saƙon taya murna ga tsohon Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Muhammad Na’abba (Afakallahu), kan naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin memba na Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Habibu Mohammed Barde, ya yaba wa Afakallahu a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan masana’antar finafinai ta Hausa, wato Kannywood.
Ya ce ƙwazon sa da gudunmawar da ya bayar sun tsara yanayin masana’antar sosai, wanda hakan ya sa wannan naɗin ya zama abin da ya dace daga kyakkyawar hidima da jajircewar sa.
Shugaban ya tuna da zaman Afakallahu a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a matsayin abin koyi tare da himma sosai wajen tabbatar da ƙa’idoji da ɗa’a na Kannywood.
Ya ƙara da cewa, “Sabuwar rawar da zai taka a Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Jigawa wata shaida ce ta ci gaba da sadaukar da kai ga aikin gwamnati da cigaban ilimi da al’adu a Nijeriya.”
An bayar da wannan yabo ne cikin alfahari da mutunta irin goyon bayan da Afakallahu ke bayarwa da kuma gudunmawa mai kima ga masana’antar fim.
MOPPAN, a cewar sanarwa ga manema labarai wadda Sakataren Yaɗa Labarai na MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya sanya wa hannu, ta ce ta na da yaƙinin cewa ƙwarewa da gogewar Afakallahu za su amfanar da Jami’ar Tarayya ta Dutse sosai tare da ƙara inganta manufar ta ta fasaha da ilimi.
Tsohon babban sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Afakallahu ya samu muƙami a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa
Shi dai Afakallahu, ya samu wannan naɗi ne a ranar Juma’a, 17 ga Mayu, lokacin da Gwamnatin Tarayya ta bayyana naɗin aƙalla mutum 554 a matsayin membobin ‘yan hukumomin gudanarwa na jami’o’i da makarantun kimiyya da fasaha 111 da ke faɗin ƙasar nan.
Bayan sanar da amincewar naɗin nasu ne, Afakallahu ya yi wa shugaban ƙasa godiya a Instagram inda ya fara da yi wa Allah godiya da cewa, “Alhamdu lillah, Alhamdu lillah. Allah ya ƙara yi.”
Sannan sai ya ce, “Ni Isma’ila Muhammad Na’abba Afakallah da dukkan iyali na, mu na miƙa godiyar mu ga shugaban ƙasa kuma kwamandan rundunar sojin ƙasa, Bola Ahmed Tinubu (Jagaban), domin naɗa ni a matsayin memba na Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa. Ina ƙara yi wa Allah godiya.”
A ranar Alhamis, 30 ga Mayu da Juma’a, 31 ga Mayu, 2024 ne za a ƙaddamar da Hukumomin Gudanarwar a Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da ke Abuja.
A halin yanzu dai Afakallahu shi ne mutum na uku da ya samu muƙami a wannan gwamnati kuma ɗan fim na farko da aka naɗa memba na Hukumar Gudanarwar wata jami’a a ƙasar nan.