• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata a sani game da zaɓen shugaban ƙasa kafin ranar zaɓe

by DAGA WAKILIN MU
February 16, 2023
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

YANZU dai kwana tara kacal su ka rage a yi zaɓen shugaban ƙasa. Akwai muhimman batutuwa 10 da ya kamata a sani dangane da wannan zaɓe.

Mutum miliyan 93.5 su ka yi rajistar zaɓe. Sai dai ba lallai dukkan su ne za su yi zaɓe ba.

Zaɓen Nijeriya ya kai kwatankwacin zaɓen sauran ƙasashen Afrika ta Yamma baki ɗaya yawa, idan da a ce za su haɗu su yi zaɓe a rana ɗaya.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta buga ƙuri’u miliyan 187 don zaɓen shugaban ƙasa. Za a yi amfani da rabin su a lokacin zaɓen 25 ga Fabrairu. Idan ta kama sai an yi zaɓen raba-gardama, wato zagaye na biyu, sai a yi amfani da sauran rabin ƙuri’un kenan.

Jam’iyyu 18 ne su ka fitar da ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu.

Idan ta kama a yi zaɓen raba-gardama, wato zagaye na biyu yayin da zaɓen shugaban ƙasa bai fitar da wanda ya yi nasara ba, to INEC za ta shirya zaɓen a cikin kwanaki 21.

Idan kuma ba za a yi zaɓen raba-gardama ba, kuma wani ɗan takarar shugaban ƙasa bai kai ƙara kotu ba, to INEC za ta ƙone sauran ƙarin takardun zaɓe miliyan 93.5 da ta buga.

Akwai rumfunan zaɓe 176,846 da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa. Amma yanzu sun koma 176, 606, saboda INEC ta sanar cewa ba za a yi zaɓe a rumfuna 240 cikin jihohi 28 da FCT Abuja ba.

9. Adadin ejan-ejan ɗin da Jam’iyyu 18 za su tura wurin zaɓe ya kai 1,642,386. A cikin su 1,574,301 ejan ne a rumfunan zaɓe, wato ‘polling egents’. Sai 68,088 kuma ejan-ejan ne masu sa-ido wurin tattara sakamakon zaɓe, wato ‘collation egents’.

Jihohin Taraba da Imo ne ke da mafi yawan rumfunan da ba za a yi zaɓe a cikin su ba. Yayin da Taraba ke da rumfuna 34, Jihar Imo kuwa har 38.

INEC ta ce ta rigaya ta bayar da katin shaidar ejan ga wakilan jam’iyyu a wurin zaɓe da wurin tattara sakamakon zaɓe. Saboda haka ba ta yarda mutum biyu su fito su ce jam’iyyya ɗaya su ke wakilta ba. Ejan ɗaya kaɗai INEC ta sani. Wanda ya yi karambani ko gangancin yi wa INEC shisshigi, za a damƙe shi ya fuskanci hukunci.

Loading

Tags: INECjam'iyyun siyasamuhimman abubuwaZaɓen 2023zaɓen shugaban ƙasa
Previous Post

Darakta K-eza na so gwamnatocin Arewa su horas da matasa kan sana’ar fim

Next Post

Kotu ta sake tura Murja Kunya da wasu mutum uku zuwa kurkuku

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Murja Ibrahim Kunya da Ashir Idris (Maiwushirya)

Kotu ta sake tura Murja Kunya da wasu mutum uku zuwa kurkuku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!