• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Darakta K-eza na so gwamnatocin Arewa su horas da matasa kan sana’ar fim

by DAGA ABBA MUHAMMAD
February 15, 2023
in Labarai
0
Mahalartan taron horas da 'yan Kannywood a Katsina

Mahalartan taron horas da 'yan Kannywood a Katsina

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DARAKTA a Kannywood, Aminu Mannir K-Eza, ya yi jan hankali da kira ga gwamnati da ta yi ƙoƙari wajen tallafa wa ‘yan fim don a rage zaman banza.

K-Eza, wanda mazaunin Katsina ne, ya yi wannan maganar ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim game da horas da ‘yan fim ɗin Jihar Katsina da su ka yi a watan Fabrairu da ya gabata.

Daraktan ya ce, “Ina kira ga gwamnatocin jihohin mu da su ƙara ƙaimi wajen taimaka wa matasan mu masu sana’ar fim da sauran sana’o’in hannu domin a rage zaman banza, saboda aƙalla a yanzu akwai sama da mutum dubu ɗari a masana’antar, wanda duk jihohin mu akwai masu sana’ar fim, amma kashi 70 ba a samun tallafi a wurin gwamnati kamar yadda mu mu ka samu, har mu ka gudanar da ‘workshop’ na kwanaki uku. Ka ga in mu na samun tallafi a gwamnatance, za mu samu nasara.”

Ya ƙara da cewa, “Alhamdu lillahi, mu a yanzu babu abin da za mu ce wa Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, wato Muntari Lawal, sai godiya domin ya nuna mana mu ‘ya’yan shi ne, kuma shi masoyin mu ne na haƙiƙa.

“Abin da ya sa na ce haka, Muntari Lawal shi ne ya yi mana jagora, ya kuma ba mu gudunmawa har gwamnati ta ba mu damar gudanar da ‘workshop’ ɗin da mu ka yi, wanda shi ne karo na farko da aka gudanar a Jihar Katsina. Mu na godiya a gare shi, mu na kuma jinjina a gare shi. Allah ya saka masa da alkhairi.”

Aminu Mannir K-Eza na jawabi a wurin taron

Da mujallar Fim ta tambaye shi yadda su ka gudanar da ‘workshop’ ɗin, sai ya ce, “Mun ɗauki ajujuwa biyar ne, wanda su ka haɗa da ba da umarni, kyamara, editin, rubuta labari da kuma aktin.

“A waɗannan ɓangarori da na lissafo, aƙalla mun ba mutum tamanin da shida horo,  cikin ikon Allah a tsawon kwanaki uku mun ciyar da dukkanin waɗannan mutane. Haka kuma mun ba da alawus ga kowannen su.

“Sannan an yi jarabawa, inda wanda su ka samu cin jarabawar sun samu kyaututtuka kamar kwamfotoci a duka ɓangarorin.”

Shin wani kamfani ne ya ɗauki nauyin ‘workshop’ ɗin? K-eza ya amsa: “A’a, gwamnati ce ta ɗauki nauyi. Mun rubuta mata a rubuce cewa ‘yan fim ɗin Katsina ba su taɓa samun wannan horo ba, ta kuma taimaka mana mu ka shirya. A zahiri ma, an ba mu taimakon mutum talatin ne, sai mu ka ga abin ya yi kaɗan, sai mu ka faɗaɗa ya zama na mutum tamanin da shida.”

A game da ko su waye shugabannin gudanar da taron, ya ce: “Ni, Aminu Mannir K-Eza, ni ne ciyaman, sai Mas’ud Sarkin Hawa, Aminu Dagash, Rufaida Ahmad Adam. Mu na da yawa gaskiya, amma mu huɗun nan ne a gaba, kuma ni na jagoranci abin gaba ɗaya, da neman aikin, da taimakon wurin gwamnati duk ni na yi.”

Shin kwalliya ta biya kuɗin sabulu ya yi gudanar da horaswar? Sai ya ce, “Tabbas, mun samu nasara sosai domin mutane sun yaba ƙwarai da gaske. Saboda abu ne wanda ba a taɓa yi ba a jihar. Sannan duk abin da mutane su ke yin shi ba tare da sun samu horo ko koyo ba, za su riƙa yin shi cikin jahilci ne.

Mika’ila Gidigo ya na jawabin horaswa ga mahalarta

“Babban nasarar mu a yau shi ne mutanen mu da ke Jihar Katsina ba su taɓa halartar ‘workshop’ ko ‘seminar’ a kan abin da ya shafi fim ba, sun yarda da cewa ya kamata su nemi ilimin harkar, saboda an koyar da su abin da ba su san shi ba. Domin akwai abokai na da ke gidan talbijin na KTTV da su ka ce ai su ma da na gayyace su su ma an yi da su, saboda abu ne mai matuƙar muhimmamci a jihar tunda ba a taɓa yi ba.

“Nasara ta biyu, ita kan ta gwamnati ta yi na’am da yadda aka gudanar da abin, saboda ba su taɓa tunanin za a yi abin haka ba.

“A ranar da mu ka kammala, mun ba kowa shaidar kammala horo, satifiket ɗin, sannan kuma mun haɗa da alawus.”

A game da ƙalubale, K-Eza ya ce, “Gaskiya ba mu samu ƙalubale ba. Ƙalubalen da mu ka ɗan samu, akwai mutanen da mu ka gayyata ba su samu damar zuwa ba, wannan kuma yanayi ne na rayuwa. Amma kuma mutanen da mu ka yi tunanin za su zo taro, sun ninka na tunanin mu. To, ka ga ƙalubalen da mu ke tunani bai zama ƙalubale ba. 

“Amma kuma akwai ‘yan ƙasar Nijar da su ka halarta, saboda maƙwabtakar da ke tsakanin mu da Nijar. Akwai kuma wasu daga Kano da su ka halarta. Amma kashi 70 ‘yan Katsina ne mazauna wani garin su ka halarta.”

K-Eza ya yi wani jan hankali game da irin wannan taron, da ya ce, “Jan hankalin da zan yi na farko dai, waɗanda su ke da dama da za su iya taimaka wa matasa abokan sana’a don su samu ilimi a harkar su zage damtse. Saboda duk abin da aka ce a cikin jahilci za a riƙa yi shi, faɗuwa ne a cikin shi. Sannan kuma mu matasa da ke cikin harkar nan, idan aka gayyace mu irin wannan ‘workshop’ ɗin mu riƙa halarta. Babu wani abu da zai zame maka ci-gaba a rayuwa in ba ka da ilimin shi. Wannan shi ne kiran da zan yi.”

Furodusa kuma ɗan jarida, Isah Bawa Doro, a wurin taron

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an gudanar da taron horaswar a ranar Asabar, 13 ga Fabrairu, Lahadi, 14 ga Fabrairu, da Litinin, 15 Fabrairu, 2023. An kuma yi taron ne a tsohon Gidan Gwamnatin jihar.

Wasu daga cikin waɗanda su halarci taron sun haɗa da Isah Ibn Hassan (Gidigo), Mansur Sadiq, Binta Ola, Bawan Mata, Aminu Dagash, Isah Bawa Doro, da Umar Katsina (Sarkin Fawa).

Mawaƙi Sanusi Anu (a hagu) ya na karɓar satifiket ɗin sa
Gidigo da Mansur Sadiq a wurin taron
Dandazon mahalarta taron

Loading

Previous Post

Kiran Atiku ga al’ummar Inugu: Ku zaɓi PDP don a tafi tare da ku

Next Post

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata a sani game da zaɓen shugaban ƙasa kafin ranar zaɓe

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata a sani game da zaɓen shugaban ƙasa kafin ranar zaɓe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!