• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kiran Atiku ga al’ummar Inugu: Ku zaɓi PDP don a tafi tare da ku

by DAGA WAKILIN MU
February 15, 2023
in Nijeriya
0
Atiku ya na gabatar da jawabi a taron PDP a Inugu

Atiku ya na gabatar da jawabi a taron PDP a Inugu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar zama shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’ar Jihar Inugu da su zaɓi PDP a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi domin su ma su sha romon dimokiraɗiyya daga wajen Gwamnatin Tarayya.

Atiku ya faɗi haka ne a ranar Talata a lokacin taron yaƙin neman zaɓen PDP da aka yi a Inugu.

Ɗan takarar ya ce zaɓen PDP shi zai ƙara kusantar da jihar ga fadar shugaban ƙasa domin a tafi tare da ita.

Ya bayyana jin daɗi kan ɗimbin mutanen da su ka fito su ka halarci taron, ya ce wannan na nufin da ma can Jihar Inugu jiha ce ta jam’iyyar PDP.

“Ni ne zan zama matakalar da wani ɗan ƙabilar Ibo zai taka ya kai ga zama shugaban ƙasa a nan gaba,” inji shi.

Kiran Atiku ga al’ummar Inugu: Ku zaɓi PDP don a tafi tare da ku

Atiku ya ƙara da cewa: “Ina so ku ci gaba da ba PDP goyon baya domin kuwa gwamnatin da za ta kafa mulkin shugaban ƙasa a nan gaba ta Ibo ce a ƙarƙashin jagorancin Ibo.

“Ina ba ku shawara da ko yaushe ku riƙa tashi ana yin tafiya tare da ku domin ku ma ku sha romon dimokiraɗiyya,” in ji shi.

Sai dai an lura da cewa Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Inugu ɗin bai halarci taron ba.

Ugwuanyi, wanda ya na daga cikin gwamnonin nan biyar da su ka yi tawaye su ka ƙi bin Atiku, wato ‘yan gungun G-5, an ce wai ya tarbi Atiku ne a Gidan Gwamnati a matsayin sa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa kawai.

Dakta Iyorchia Ayu, wanda shi ne Shugaban jami’ar PDP na ƙasa, a nasa jawabin ya bayyana Inugu da cewa jihar PDP ce tun fil’azal.

Ya ce: “Inugu sai PDP; kuma PDP sai Inugu.”

“PDP na cikin jinin ku, kuma na tabbatar da cewa a ranakun zaɓe, wato ranar 25 ga Fabrairu da ranar 11 ga Maris, daga nan za ku zaɓi PDP daga sama har ƙas, kuma daga ƙasa har zuwa sama.”

Bugu da ƙari, ya shawarce su da kada su kuskura su saurari wata jam’iyyar; ya ce: “Rayuwar ku na wajen PDP”.

Kuma ya ce, “Ba sai na tsaya yi maku wani dogon wa’azi ba domin kun riga kun dawo wajen mu.”

Loading

Tags: 2023 electionsAtiku AbubakarEnugu rallyIyorchia AyuPDP
Previous Post

Aikin zaɓen 2023: Duk wanda zai yi wa INEC aiki sai ya yi rantsuwa – Yakubu

Next Post

Darakta K-eza na so gwamnatocin Arewa su horas da matasa kan sana’ar fim

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Mahalartan taron horas da 'yan Kannywood a Katsina

Darakta K-eza na so gwamnatocin Arewa su horas da matasa kan sana'ar fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!