Kamar kowace shekara, a yau ma mujallar Fim ta kawo maku jadawalin manyan abubuwan da su ka faru a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood. Kamar kowace shekara, a bana ma ‘yan fim sun ga abin farin ciki, kuma sun ga na baƙin ciki; wasu sun ga samu, wasu sun ga rashi. To amma za mu iya cewa duniya ba ta taɓa ganin tashin hankali irin na wannan shekara ta 2020 ba, ba domin komai ba sai saboda cutar korona (COVID-19) wadda ta tilasta rufe duk wani al’amari na ɗan’adam in ban da numfashi. An yi zaman dole, an daina kusan duk wata sana’a sai ɗaiɗaiku. Sannan kuma an yi mace-mace.
A nan ƙasa, ga lissafin manyan abubuwan da su ka faru a Kannywood a cikin watanni 12 da su ka gabata.
JANAIRU
* An share ‘yan fim da mawaƙa a bikin sabuwar shekara wanda gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya.
* Ƙungiyar Ɗaliban Hausa ta Ƙasa (KUDHAN) ta karrama Babban editan jaridar ‘Daily Nigerian’, Malam Jaafar Jaafar, saboda ƙoƙarin da ya yi na taimaka wa shahararriyar zabiya Hajiya Magajiya Ɗambatta.
* Wasu mutane waɗanda ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki a shagon jaruma Samira Saje a Kano, su ka washe ta.
* Fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Kahutu (Rarara) ya kawo ƙarshen rigimar da ta ɓarke a tsakanin wasu mawaƙan siyasa da wasu muƙarraban gwamnan Jihar Kebbi a kan zargin sun yi wa gwamnan zambo.
* Gobara ta lashe gidan fitaccen jarumi Aminu Ilu Dambazau (Asid) da ke Kano, ta ƙone gidan da dukkan kayan da ke cikin sa ƙurmus.
* Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya naɗa babban furodusa Alh. Abdullah Tahir Al-Kenanah matsayin Darakta-Janar na Hukumar Ƙawata Birane.
* Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya, MOPPAN, reshen Jihar Katsina, ta yi sababbin shugabanni.
FABRAIRU
* Fitaccen mawaƙi Malam Yahaya Makaho ya ƙaddamar da gidauniyar ‘Malam Yahaya Makaho Foundation’ wadda za ta riƙa taimaka wa naƙasassu ‘yan’uwan sa.
* Fitaccen furodusa Abdulkareem Muhammad ya yi bikin cika shekara 40 a aikin jarida.
* Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta kulle shagon ɗaukar hoto na fitaccen jarumi Sani Musa Danja mai suna ‘Celebrity Photography’.
* Jami’an tsaro sun kama mawaƙin siyasa da ke Katsina mai suna Muhammadu Buhari (Kozan Waƙa), wanda ɗan ga-ni kashe-nin ƙungiyar Kwankwasiyya ne, sanadiyyar wata waƙa da ya yi mai suna ‘A Wanki Gara’ inda aka ce ya yi ɓatanci a kan Gwamnan Kano.
* Bidiyon tsiraicin fitacciyar jaruma Maryam Booth ya fito bayan shekara 3 da ɗaukar sa. Fitaccen mawaƙin hip-hop Ibrahim Rufa’i Balarabe (Deezell) ya musanta zargin da aka yi masa na cewar shi ne ya fitar da bidiyon.
MARIS
* Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i na Jihar Kano, Alh. Isma’il Na’abba (Afakallahu) ya yi barazanar zai yi ƙarar Yusuf Haruna (Baban Chinedu) saboda ƙazafin da ya ce ya yi masa na cinye kuɗin marayun marigayi Ibro.
* Ma’ajin ƙungiyar MOPPAN, Alh. Sani Rainbow, ya yi murabus daga muƙamin sa sakamakon saɓanin wargaza haɗin kai tsakanin shugabannin.
* Fitacciyar jaruma Samira Ahmad ta gina wa ɗaliban Makarantar Sakandaren ‘Yanmata ta Gwamnati da ke Jogana a Jihar Kano rijiyar tuƙa-tuƙa kyauta.
* Ɓarayi sun sace marubuci, mawallafi kuma furodusan finafinan Hausa, Malam Abdullahi Yahaya Maizare a Zariya, Jihar Kaduna.
* Ƙungiyar MOPPAN ta dakatar da shirya finafinan Hausa baki ɗaya sakamakon ɓarkewar cutar ‘corona virus’.
* Kotun Shari’ar Musulunci ta aika wa jarumi Haruna Yusuf (Baban Chinedu) da sammaci sakamakon ƙarar da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallahu), ya kai shi bisa zargin ƙazafi da ɓata suna.

AFRILU
* Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da shirin ‘Kwana Casa’in’ da na ‘Gidan Badamasi’, waɗanda gidan talbijin na Arewa24 ke nunawa saboda ta ce ba a kai mata su domin tacewa.
* Fitaccen jarumi Adam A. Zango ya yi mubaya’a ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ya yarda zai yi rijista da ita kamar sauran ‘yan fim.
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da gidan talbijin na Arewa24 sun sasanta a kan taƙaddamar da ta ɓarke a tsakanin su.
MAYU
* Tsohuwar jaruma Fati Ladan ta yi rabon kuɗi ga mabuƙata a cikin watan azumi don rage raɗaɗin rayuwa a lokacin zaman gida sakamakon cutar korona.
YULI
* Jaruma Khadija Kyari ta tsallake rijiya da baya sakamakon haɗarin mota da ya ritsa da ita a hanyar Katsina zuwa Kano a hanyar su ta dawowa daga biki a ƙasar Nijar.
* Fitaccen furodusa Abdul Amart ya shirya bikin bada kyaututtuka ga waɗanda su ka lashe gasar da ya sanya a fim ɗin sa ‘Manyan Mata’.
* Gwamnatin Kano ta buƙaci gidajen rediyo su bi dokar tace waƙoƙin yabon Annabi.
* Gwamnatin Kano ta kasafta kuɗi N16,373,699 don gina cibiyar fasahar zamani a ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai ta jihar.
AGUSTA
* Jaruma Hauwa Abubakar Ayawa ta yi bikin kafa gidauniyar tallafa wa mabuƙata a Kaduna mai suna ‘Hauwa Ayawa Foundation’.
* An yi bikin baje kolin finafinai na ‘Kaduna Films Festival’ na bana ta yanar gizo.
* Wani kamfani mai zaman kan sa ya gabatar wa da gwamnatin Kano wani tsari kan yadda za ta gyara masana’antar finafinai ta Kannywood domin a samu ƙarin kuɗin shiga.

OKTOBA
‘Yansanda sun tsare mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi a kan zargin dukan kawo wuƙa da wani abokin sa ya yi wa wani mutum.
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta kafa kwamitin tantance sha’irai masu waƙoƙin yabon Manzon Allah.
* Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta yi kira ga masu shirya finafinan Hausa masu dogon zango da su ke ɗorawa a YouTube da su gaggauta su je su yi rajista da ita.
* Jaruma Rahama Sadau ta jawo wa kan ta terere da ta tura wasu hotuna masu bayyanar da surar ta a Instagram da Twitter. Da yawa an soke ta a kan hotunan.
*Rahama Sadau ta bayyana baƙin cikin ta kan yadda wani wanda ba Musulmi ba ya yi amfani da hotunan ta ya yi kalaman ɓatanci kan Manzon Allah (SAW).
NUWAMBA
* MOPPAN ta yi magana a kan Rahama Sadau, ta ce ta taɓa korar ta daga industiri a cikin 2016 amma Hukumar Tace Finafinai ta dawo da ita.
* Mazan Kannywood sun nesanta kan su da Rahama Sadau sakamakon ɓatanci da wani wanda ba Musulmi ba ya yi a ƙasan hoton ta a Twitter.
* Rahama Sadau ta nemi yafiyar ɗaukacin al’ummar Musumi kan abin da ya faru sakamakon hoton ta da wani arne ya yi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).
* Sufeto-Janar na ‘Yansandan Nijeriya, Alhaji Mohammed Adamu, ya ba Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna umarnin ya binciki Rahama Sadau kan iƙirarin da aka yi cewa ta aikata saɓo a kan Manzon Allah (SAW).
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta sake kama mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) a kan wata waƙa da ya saki ba tare da izini ba.
* Lawal Gusau, mutumin da ya yi ƙarar Rahama Sadau wajen ‘yansanda, ya janye ƙarar.
* Gabar da ke tsakanin fitattun jarumai Ali Nuhu da Adama A. Zango ta ƙare. Jaruman sun samu sasancin ne inda dukkan su su ka yi rubutu a kan junan su, kuma su ka haɗu a sinima wurin nuna fim ɗin ‘Fati’. A baya sun samu rashin jituwa na tsawon lokaci.
* An gudanar da taron duniya kan finafinan harsunan Afrika na gado (KILAF) a Kano. Shi ma taron an yi shi ne ta hanyar intanet.
DISAMBA
* Wata kotun majistare a Kano ta soke shari’ar da gwamnati ke yi da mawaƙi Naziru M. Ahmad da darakta Sanusi Oscar sakamakon bada haƙuri da su ka yi.
* Fitacciyar mawaƙiya Jamila Kogi ta yi haɗarin mota tare da wasu abokan sana’ar ta a hanyar Nassarawa, har ta samu raunuka.
* Fittacen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya samu sarautar Ɗanburam Sarkin Gobir daga Sarkin Gobir, Alhaji Isah Muhammad Bawa.