HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta ƙara zaɓo mutum 15 cikin 50 a gasar marubutan Hausa da ta sanya.
Hukumar ta bayyana labaran su a matsayin waɗanda suka yi nasarar fitowa a zagayen kusa da na ƙarshe wanda kwamitin da ke lura da gasar ya fara bayyanawa a makon da ya gabata.
A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu a yau, an ce dukkan waɗanda sunayen su suka bayyana a wannan zagayen za su iya sa ran samun nasarar lashe gasar.
Idan ba a manta ba, a makon jiya ne hukumar ta bayyana sunayen mutum 50 a matsayin waɗanda suka yi nasara a zagayen farko cikin mutane 126 da suka shiga gasar domin a fafata da su.
Yanzu a cikin mutum 15 za a fidda gwaraza, daga na 1 zuwa 3 sai na 4 zuwa na 15.
Hukumar za ta bayyana sunayen waɗanda suka yi nasara a ranar babban taron da aka shirya wa marubutan wacce za a faɗa nan gaba kaɗan.