• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mutane sun yi wa Adam Zango caa kan kare jarumar Kannywood Meerah da ya yi kwana ɗaya bayan ya saki matar sa

by DAGA ABBA MUHAMMAD
April 14, 2023
in Labarai
0
Meerah Shu'aib da Adam A. Zango

Meerah Shu'aib da Adam A. Zango

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MUTANE masu bibiyar jarumi kuma mawaƙi Adam A. Zango a soshiyal midiya sun masa rubdugu kan yadda ya ke bayyana kalaman goyon baya da kuma ƙauna ga jarumar Kannywood Meerah Shu’aib, kwana ɗaya kacal bayan ya saki matar sa.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba da labarin yadda wasu makusantan jarumin su ke zargin Meerah (Junaidiyya ta cikin diramar ‘Gidan Badamasi’) da zama ummulhaba’isin rugujewar auren Zango da matar sa ta shida da ya saki, wato Safiyyah Umar Chalawa. 

A labarin, wata majiya mai tushe ta faɗa wa wakilin mu cewa zafin soyayyar da Zango ya ke yi da Meerah a shirin sa mai dogon zango na ‘Asin Da Asin’ ita ce ta jawo rigimar da ta sa Safiyyah ta yi yaji har na tsawon wata biyar kafin ya aika mata da takardar saki a garin su, Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi, a ranar Litinin da ta gabata. Wannan saki shi ne na biyu da ya yi mata.

Da yawa masu bibiyar jarumin sun yi mamakin ganin Zango ya fara sakin kalaman ƙauna da goyon baya ga Meerah tun daga washegarin ranar mutuwar auren; sun ɗauka zai zauna ya yi jimamin rabuwar auren nasa.

Zango ya wallafa aƙalla saƙo guda biyu a kan Meerah tare da saka hotunan ta a Instagram, waɗanda ke bayyana shauƙin sa game da ita. Dukkan su ya rubuta su ne a matsayin saƙon kai-tsaye na ban-haƙuri ga jarumar. 

A saƙo na farko, wanda ya wallafa a ranar Talata, jarumin ya yi addu’ar Allah ya saka mata kan abubuwan da ake cewa game da ita, wato manufar sa dai ita ce labarin da mujallar Fim ta bayar game da soyayyar su ƙarya ce.

Ya ce: “Barka da azumi Sayyada Ameerah. ALLAH YA SAKA MIKI.”

A saƙo na biyu ne ya faɗaɗa maganar, inda ya rubuta da Turanci cewa, “Whoever is trying to bring you down is already below you. Rumours are carried by haters, spread by fools, and accepted by idiots. So let the donkeys believe whatever.” 

Mujallar Fim ta fassara wannan kalamin da ya yi a fusace da cewa: “Duk wanda ke so ya ga bayan ki, da ma can a ƙasa da ke ya ke. Ita ji-ta-ji-ta magabta ne ke yaɗa ta, kuma wawaye ne ke baza ta, sannan sakarkaru ne ke yarda da ita. Don haka ki ƙyale jakunan su ci gaba da yarda da ko ma menene.”

Ya ƙara da cewa, “Wani lokacin shirun ba ya magani.”

Da dama daga cikin waɗanda su ka karanta saƙonnin sun yi mamaki, kuma ba su aminta da irin yadda jarumin ya fito ƙarara ya na nuna wa Meerah so ba, musamman a halin jimami da ake ciki na sakin da ya yi wa matar sa da ya shekara huɗu da ita kuma har sun haihu.

A ganin su, kamata ya yi ya kama bakin sa ya yi shiru, maimakon ƙara iza wutar saɓanin da ya faru da matar sa da kuma ɗaure wa Meerah gindi.

Wata A’isha Sulaiman da mamaki ya ishe ta cewa ta yi, “Zango anya kai ne kuwa? Anya ba ‘hacking’ ɗin shafin nan aka yi ba?”

Da wani ya ce masa, “Me ya sa ka ke koɗa ta haka?” sai Zango ya kada baki ya ce masa: “To wannan zunubi ne?”

Saƙo na ɗaya da na biyu

Wani Parouq Junju, wanda da alama bai san zurfin mu’amalar jaruman biyu ba, tambaya ya yi, ya ce: “A nan jirgin ya sauka yanzu kuma?” Wato Zango ya koma wa Meerah kenan?

Shi kuwa wani mai laƙabi da Hausa Boi, zagi ya sha a wajen Zango saboda tambayar da ya yi kan maganar da jarumin ya wallafa, ya ce, “Me hakan ya ke nufi? Wannan mutumin ya taɓu wallahi.” Da wata ta ce, “Na rantse bai da lafiya,” sai Hausa Boi ya amsa: “Mutumin ya na yin abu kamar mara hankali. Idan ba haka ba, miye na tura irin wannan saƙon hoton yarinyar da kuma wannan rubutun?”

Nan da nan Zango ya fusata ya mayar masa da martani cewa: “Me zai hana ka ɗauke ni ka kai ni asibitin taɓaɓɓu na uban ka? Na san zai iya warkar da ni a can!”

Ganin haka, sai Hausa Boi ya mayar masa da cewa: “Uba na bai da shi, ya kai ɗan’uwa. Na san abin ya yi maka ciwo. To ka yi haƙuri da wannan. Amma shin ba ka san cewa kai fitaccen mutum ba ne? Mutane na sa ido a kan duk wani abu da ka yi. Ka dinga sanya wa zuciyar ka linzami, ɗan’uwa. Wani abin idan ka yi har kunya ke kama ni wallahi. Don Allah a kullum ka riƙa kulawa tare da sa tunani a kan abubuwan da ka ke yi, ka gane? Kai ne fitaccen mutum mafi munin ɗabi’a da na taɓa sani, ɗan’uwa. 

“Ba a daɗe ba fa da ka saki matar ka, amma kwatsam ka fara wallafa saƙo kan wata, da wani irin rubutu. Wallahi tallahi ba zagin ka na ke yi ba. Kawai ka je ka yi tunani. Ba daidai ba ne a yanzu. Gaskiya ce.”

Ita kuwa Hassana Maikyau (@hersaner_maikyau), ce wa Zango ta yi: “In da ni ce kai wallahil azim uffan ban ce wa kowa. Su je su yi tunani su soke ka, ai mutum ba shi ke rubuta wa kan sa ƙaddara ba. Kasancewa fitaccen mutum ba zunubi ba ne. Ka koyi yadda za ka sa ido a abu ba tare cewa komai ba. Wallahi shiru ma ita ce amsa mafi dacewa ga wawa. Allah ya yaye wa kowa abin da ke damun sa albarkacin wannan wata mai girma, amin. Gara ka koma gefe ka mai da hankali a kan ibadun ka, ka mori wannan goma ta ƙarshe. Ba za ka iya faranta wa kowa rai ba. Ba na goyon bayan rashin adalci, ba cewa na yi ka na da gaskiya ko a’a ba, sanin gaibu sai Allah.”

Da alama ita ma bai ɗauki shawarar ta ba, domin ya ba ta amsa ne kamar haka: “Rabu da su, na ga kamar su na ganin kamar ina jin tsoron yin rashin mutunci ne a yanar gizo. Wannan shekarar na ajiye rigar ɗaukakar, na sagale ta a gida. Kunyar marar kunya ai asara ne.”

Shi kuma wani mai laƙabi da ‘Digital Usterz’ shawara ya ba Zango a game da Meerah, ya ce masa, “Wallahi in da ni ne kai bayan Sallah zan aure ta. Haba mana jama’a, kun sa mutum a gaba!”

Mujallar Fim ta lura da cewa ganin bai samu goyon baya sosai ba yadda ya ke buƙata, jarumin a yau ya koma ya goge dukkan kalaman amsa da aka ba shi a ƙasan saƙonnin nasa, kuma ya kulle filin da wani zai iya yin magana kan saƙonnin, wato ‘comments’.

A yanzu dai dukkan mutanen da ke zagaye da Zango sun amince da cewa labarin da mujallar Fim ta bayar gaskiya ne, domin sun bincika sun fahimci hakan. Sun yarda da cewa ya saki matar sa a ranar Litinin, sannan da ma sun san akwai soyayya tsakanin sa da Meerah.

Mujallar Fim ta watan Mayu, 2019, ɗauke da labarin auren Zango da Safiyyah inda ya yi rantsuwar ba zai taɓa sakin ta ba

Wani makusancin sa ma ya ƙara wa wakilin mu bayanin cewa a yanzu Zango ya na ci gaba da hulɗa da jarumar ne ba domin komai ba sai don ya samu ta gama masa fim ɗin sa.

Ya ce: “Kamar yadda ku ka buga a labarin ku, yanzu Adamu ba soyayyar zahiri ya ke yi da Meerah ba, kawai ya na lallaɓa ta ne saboda ta ci gaba da shirin ‘Asin Da Asin’. Ina tabbatar maka nan gaba sai ka ji labarin kowa ya kama gaban sa, shi da ita.

“Shi ya sa ya ke ƙoƙarin nuna wa duniya cewa har yanzu su na tare. Amma idan ka lura, ita ba ta ce komai ba kan wannan cacar bakin da ake yi.”

Loading

Tags: 'Asin Da Asin''Gidan Badamasi'Adam A. ZangoaureMeerah Shu'aibSafiyyah Umar Chalawasakisoshiyal midiyasoyayya
Previous Post

Labarin wai na mutu ƙarya ce aka yaɗa, inji Al-Amin Ciroma

Next Post

Sharhin littafin ‘Jiki Magayi’

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post
Bangon littafin 'Jiki Magayi'

Sharhin littafin 'Jiki Magayi'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!