• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sharhin littafin ‘Jiki Magayi’

by DAGA KABIRU YUSUF FAGGE (ANKA)
April 15, 2023
in Marubuta
0
Bangon littafin 'Jiki Magayi'

Bangon littafin 'Jiki Magayi'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
LITTAFI: Jiki Magayi
MARUBUTA: John Tafida Umaru Zariya da Rupert East
SHEKARA: 1995
MAƊABA’A: Northern Nigeria Publishing Company (NNPC), Zariya
BUGAWA: Ahmad Bello University Press, Samaru, Zariya
SHAFUKA: 52
MAI SHARHI: Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
‘Jiki Magayi’ labari ne na wani ƙasurgumin kuma shahararren attajiri mai suna Mallam Shaihu mazaunin cikin birnin Galma. Saboda yawan kudin Mallam Shaihu ba inda sunan shi bai kai ba (shafi na 1). Kai hatta shi kan shi Mallam Shaihu bai san yawan dukiyar sa ba (shafi na 2). Sai dai kash! Duk da tarin dukiyar Mallam Shaihu, Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba, ya yi aurarraki don samun haihuwa, amma bai taɓa samu ba. Haka nan ya ɓatar da dukiya ba adadi a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori duk don neman maganin haihuwa, amma ko ɓatan wata ba a taɓa samu a cikin matan sa ba.
Damuwar Mallam Shaihu ta rashin haihuwa ta yawaita wanda har ta kai shi ga yin mafarki da wata yarinya a gidan Mallam Audu mai suna Zainabu, wanda a mafarkin aka yi masa isharar idan ya aure ta lallai zai sami haihuwa.
Mallam Shaihu bai yi ƙasa a gwiwa ba ya tuntuɓi malamin duba da tsibbu a kan mafarkin da ya yi. Malamin ya duba masa, ya ba shi labarin zai auri wata yarinya ‘yar gidan Mallam Audu ɗin, kuma za su haihu, sai dai auren ya na cike da wahala da da-na-sani, ya ba shi shawarar ya haƙura da batun auren.
Mallam Shaihu ya yi ta tunani dangane da wannan al’amari, amma saboda son haihuwa ya shure maganar malamin ƙasa, ya sa aka kira masa Mallam Audu don neman auren ‘yar sa.
Yarinyar da Mallam Shaihu ya gani a mafarki ita ce Zainabu, sai dai ta na da wanda ta ke so, don haka ko da mahaifin Zainabu, wato Mallam Audu, ya zo gare shi ya sanar da shi cewa: “Wannan magana ta na da wuya, domin kuwa ita Zainabu, tun su na ƙanana akwai wani yaro, sunan sa Abubakar, tare su ka taso, ta na son sa, shi kuma ya na son ta, har kuwa kowa ya sani ita zai aura…” (shafi na 3).
Duk da haka Mallam Shaihu bai gamsu ba, ya ci gaba da neman auren Zainabu, har a wajen malamin duba.
Mallam Shaihu ya nemi yardar Zainabu, amma ta ƙi. Don ya cimma burin sa sai ya sa wani shahararren malamin tsibbu mai suna Mallam Sambo ya yi masa aiki a kan yarinyar wanda ya juye mata hankali ta dawo gare shi. Ta rabu da saurayin ta Abubakar wanda aka yi masu ‘baiwa’ da shi.
Mallam Shaihu ya auri Zainabu bayan ya saki guda daga cikin matan sa. Wannan abu ya tunzura Abubakar ya sha alwashin ɗaukar fansa, ya ƙudiri aniyar cewar in har a kan da ne aka yi masa haka, to zai yi maganin da sai albarkar da yake nema ga ɗan ta zama la’ana. Hakan ya sa ya shiga faɗi-tashi tsakanin bokaye da wahalar duniya a garuruwa, har sai da ya samo maganin da ya je, wanda a lokacin Mallam Shaihu da Zainabu sun haifi yaron kirki mai suna Abdullahi, ana kiran sa Kyauta, ya yi masa magani, yaron ya zama fitinanne kuma ƙasurgumin ɓarawo har ya haɗu da wani shahararren ɓarawo mai suna Dogon Yaro.
A ƙarshe, a yawon yin sata har Kyauta ya je yin sata garin da mahaifin sa ya gudu, kuma gidan sa tsautsayi ya sa, ya kashe uban.
Sharri ɗan aike, kuma alhaki kwikuyo ne, mai shi ya kan bi, bayan mutuwar Mallam Shaihu, mahaifiyar Kyauta; Zainabu ta gaya wa ɗan ta wanda ya yi masa asiri ya zama ɓarawo. Wannan ta sa Kyauta ya yi nadama kuma ya doshi Galma don ɗaukar fansa a wurin Abubakar. Sai dai kash! lokacin da ya isa Galma, har wajen Abubakar ɗin, ya tarar da shi ya na cikin tsananin rashin lafiya. Ko da shi Abubakar ɗin ya gan shi sai ya ce: “Ka makara! Wata fansar sai gobe kiyama.” (shafi na 49) sai ya tintsire ya mutu saboda ya na cikin tsananin rashin lafiya.
A ƙarshe, Kyauta ya koma Ganye don ɗauki mahaifiyar sa. Dukiyar mahaifin sa kuwa bayan an yi mata ƙima an cire ushura aka damƙa masa komai. Ya tara dukkan malaman garin don yi wa uban sa addu’a ya raba masu ita. Haka ya rabar da kuɗi da kayayyakin mahaifin sa da takarce da dabbobi. Su ka dawo Galma shi da mahaifiyar sa. A nan ma aka ba shi gado, ya bai wa mahaifiyar sa, shi kuma ya yi sallama da ita don barin garin domin ya tafi neman rage alhakin da ya ɗauka. Ya fita daga shi sai sandar sa da gafaka da ‘yar buta.
Babban jigon littafin ‘Jiki Magayi’ shi ne “neman/son haihuwa”, domin waɗannan dalilai. Misali, a shafi na biyu, marubutan littafin sun ce: “Shekarar sa ashirin da yin aure amma bai taɓa haihuwa ba. Ya yi aure da yawa, kullum gidan sa ba a rasa matan aure huɗu. Ya ɓatad da dukiya ba iyaka wajen malamai da bokaye da ‘yan bori garin neman maganin haihuwa, amma cikin matan sa babu wadda ta taɓa ko ɓatan wata. Ko yaushe idan ya tuna da wannan babbar hasara ta rashin da sai ransa ya dugunzuma.”
Haka a wannan shafin, a mafarkin sa sun ce: “Godiya ta na gidan sa har ta haifa masa ɗan dukushi kyakkyawa…”
A shafi na 3: “Amma don tsananin son da ya mai da duk wannan ba a bakin kome ba idan buƙatar sa ta biya.”
A shafi na 8: an sake fito da jigon dai. “….kuma ka cika aure-aure da yawa, duk wadda ka aura kuwa idan ku ka yi ‘yan shekaru ka ga ba ta haihu ba sai ka sake ta da cin zarafi…”
A shafi na 13: “Dalili dai ya na son ɗa ne, an kuwa gaya masa idan ya auri yarinyar nan zai samu…”
A shafi na 14: “To, tun da yake kwaɗayin ɗa ne ya sa ya yi mini wannan abu…”
A shafi na sha bakwai ma an bayyana jigon: “….sa’an nan zai ga ƙwan sa…”
“Zainabu ta sami ciki….” Shafi 18 kenan da sauran su.
Ƙananan Jigogi
Bayan babban jigon “neman haihuwa” littafin ‘Jiki Magaji’ ya na da ƙananan jigogi masu mara masa baya kamar:
Ɗaukar fansa,
Sata,
Bokanci
=> Ɗaukar Fansa – mun ji yadda Abubakar ya sha alwashin ɗaukar fansar ƙwace masa masoyiya da Mallam Shaihu ya yi, shi ya sa ya nemo maganin da ya sa ɗan sa Kyauta ya zama ƙasurgumin ɓarawo.
Haka shi ma Kyauta da ya sami labarin wanda ya yi masa magani har ya zama ɓarawo, ya sha alwashin zuwa don ya ɗauki fansa a kan Abubakar.
=> Sata – Kyauta ya zama ƙasurgumin ɓarawo tun ya na yaro, har ya bar gida, ya je garuruwa ya na sata – ta dalilin sata ya haɗu da ƙasurgumin ɓarawo mai suna Dogon Yaro, kuma ta dalilin sata ya kashe mahaifin sa.
=> Bokanci/Tsibbu – waɗannan su na cikin ƙananan jigogi na labarin ‘Jiki Magayi’ – domin tun a farko-farkon labarin mun ji yadda Mallam Shaihu ya riƙa ɓatar da dukiya mai yawa a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori wajen neman haihuwa (shafi na biyu, sakin layi na 1).
Bugu da ƙari, da malamin duban ƙasa ya yi amfani wajen juyo da hankalin Zainabu gare shi (shafi na 6).
Shi ma Abubakar ya shiga duniya ne neman shahararren malami don ɗaukar fansa (shafi na 11). Kuma har ya riski malamin mai suna Tausayin-Ka-Da-Sauƙi, wato Zakari (shafi na 12), wanda daga jin sunan ka san boka ne.
Wurare Da Garuruwa
A cikin littafin ‘Jiki Magayi’ marubutan sun yi amfani da garuruwa kamar irin su: Birnin Galma, Yale, Dawan Ruƙuƙi, Sanga, Rimi, Garuje, da sauran su.
Ƙa’idojin Rubutu
In ban da amfani da wasu daga tsoffin salon ƙa’idojin rubutun Hausa da marubutan su ka yi, to a littafin an kiyaye ƙa’idojin rubutu yadda ya kamata. Misalan tsoffin ƙa’idojin rubutun sun haɗa da:
– “Kwantad da” maimakon “kwantar da”
– “sanad da” maimakon “sanar da”
– “sayad da” maimakon “sayar da”
– “sa’ad da” maimakon “sa’ar da”
– “garimmu” maimakon “garin mu”
– “Halimmu” maimakon “halin mu”
– “lalle” maimakon “lallai”
– “izni” maimakon “izini”
– “ko me” maimakon “komai”.
Sai kuma wajen da su ke rubuta sunayen lokuta da ƙananan baƙi. Ban da waɗannan lallai marubutan sun yi ƙoƙarin kiyaye ƙa’idojin rubutu.
Sannan akwai wani abin dubawa a littafin, duk irin tafiye-tafiye da yada zango da shiga garuruwa da wasu taurarin littafin su ka yi ba a nuna inda su ka yi sallah ba ko sau ɗaya – sai dai kawai an ambaci sunayen sallolin azahar da la’asar a matsayin lokaci kawai.
Haka nan yanayin littafin ya fi kama da fassara.
* Kabiru Yusuf Fagge (anka) marubuci ne mazaunin Kano
23 ga Ramadan, 1444 = 14 ga Afrilu, 2023

Loading

Tags: hikayaJiki MagayiJohn Tafida WusasalittafiRupert East
Previous Post

Mutane sun yi wa Adam Zango caa kan kare jarumar Kannywood Meerah da ya yi kwana ɗaya bayan ya saki matar sa

Next Post

Bikin Sallah: Daso ta raba wa mata 60 kyautar atamfofi

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Saratu ya tsakiyar matan da ta ba tallafi

Bikin Sallah: Daso ta raba wa mata 60 kyautar atamfofi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!