• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, July 21, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na ƙalubalanci masu cewa na shigo Kannywood da aure a kai na da su fito neman aure na – Rahama Yakawada

by DAGA ABBA MUHAMMAD
July 24, 2022
in Taurari
0
Rahama Aminu Abdullahi Yakawada: "Ba ni da aure"

Rahama Aminu Abdullahi Yakawada: "Ba ni da aure"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MASANA’ANTAR Kannywood a kullum ƙara samun matasan jarumai mata ta ke yi. Rahama Aminu Yakawada ta na ɗaya daga cikin sababbin jarumai da ake sa ran tauraruwar su za ta fara haskawa nan ba da jimawa ba, domin kuwa jaruma ce kuma mawaƙiya, sannan kuma marubuciyar littattafan Hausa.

Rahama yarinya ce da ba ta wuce shekara 25 ba, ga ta kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa. Haka kuma yarinya ce mai ladabi da biyayya da girmama na gaba da ita.

Sai dai ta na daga cikin irin jaruman nan da su ka shigo industiri da ƙalubale, wanda kusan duk wanda ke mu’amala da ita ya shiga tashin hankali da damuwa. Ba tun yanzu ba, an sha samun matsaloli da matan da ke shigowa Kannywood da auren su, daga baya a zo a yi ta rigima da mazajen auren su. Ita ma Rahama ta samu irin wannan matsalar, amma kuma tata ta bambanta da ta sauran.

Wannan dalilin ya sa mujallar Fim ta nemi jarumar don jin menene gaskiyar lamari game da auren ta. Rahama ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta feɗe mana biri har wutsiya, kamar haka:

FIM: Ki faɗa wa masu karatu cikakken sunan ki da tarihin rayuwar ki a taƙaice.

RAHAMA: To, ni dai suna na Rahama Aminu Abdullahi Yakawada, wadda aka fi sani da Rahama Yakawada. An haife ni a garin Yakawada da ke Jihar Kaduna. Na yi karatun firamare na da ƙaramar sakandari na a garin Yakawada, sai kuma na koma Zariya inda a can na ƙarasa karatu na na sakandari.

Rahama Yakawada

FIM: Ga ki mawaƙiya, ga ki kuma ‘yar fim. Me ya ba ki sha’awar shiga wannan harka?

RAHAMA: Gaskiya ba wai wani abu ba ne ya burge ni daga baya ba, da ma can na tashi da son abin a rai na tun ina ƙarama. Ba zan manta ba lokacin ina ƙarama na kan tsaya a gaban madubi in riƙa gwadawa a gida, na daɗe da ra’ayin abin a rai na, ba wani abu ba ne daban ya ja hankali na ba.

FIM: Tsakanin fim da waƙa, wanne ki ka fara yi?

RAHAMA: Fim na fara.

FIM: A wane fim ka ka fara fitowa?

RAHAMA: ‘Farmakin So’.

FIM: Zuwa yanzu fim nawa ki ka fito a ciki?

RAHAMA: Gaskiya ba su da yawa, ina tunanin ba za su fi bakwai ba.

FIM: Za ki iya lissafo mana muhimmai daga cikin su?

RAHAMA: E, akwai ‘Farmakin So’, ‘Zanen Ƙaddara’, ‘Baba Audu’, da ‘Kunnen Ƙashi’ na Musa Maisana’a. 

FIM: Wace hanya ki ka bi don samun shiga wannan masana’anta?

RAHAMA: Ni da kai na na kawo kai na industiri.

FIM: Da wa ki ka fara haɗuwa?

RAHAMA: Na fara haɗuwa ne da Dikko Yakubu.

FIM: Idan mu ka koma ɓangaren waƙa, me ya ja hankalin ki har ki ka fara waƙa?

RAHAMA: Abin da ya sa na fara waƙa gaskiya siyasa ne, shi ne dalilin da ya sa na fara waƙa. Tun ina tunanin ba zan iya ba, har na zo na fara rubutawa, har na je na fara rerawa da kaɗan-kaɗan.

FIM: Da wace waƙa ki ka fara?

RAHAMA: Na fara da waƙar wata ƙungiya ne ta Atiku Abubakar mai suna ASO.

FIM: Zuwa yanzu kin yi waƙoƙi za su kai nawa?

RAHAMA: Kai! Gaskiya ban san yawan su ba.

FIM: Ana kallon mawaƙan siyasa a matsayin hamshaƙan masu kuɗi. Kenan ana iya kiran ki da Hajiya Rahama kenan?

RAHAMA (dariya): Gaskiya tukunna dai.

FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a cikin wannan harka?

RAHAMA: Gaskiya an samu nasarori, tunda an fara samun abin da ake so. Da farko ina son zama jaruma, kuma an kai wannan gaɓa ɗin. Haka kuma ga shi na samu zama mawaƙiya.

FIM: Ta ɓangaren ƙalubale kuma fa?

RAHAMA: A ko’ina ba a rasa ƙalubale a rayuwa. An fuskanci ƙalubale, sun kuma zo sun wuce. Na san kuma wasu za su zo a nan gaba, don ba a gama ba. Ka san in ka na rayuwa cikin mutane dole akwai ƙalubale.

FIM: Kin samu matasala a gida lokacin da ki ka shigo industiri?

RAHAMA: Na samu. Ka san da ma ya na da wahala a ce ga yarinya za ta fara waƙa ko fim iyayen ta su bar ta kai-tsaye. Akwai irin wannan matsalar; na samu matsala ta ɓangaren yaya na da su kan su iyaye na. 

FIM: Akwai maganganu a kan ki, ana cewa ki na da aure a kan ki a halin yanzu. Mecece gaskiyar maganar?

RAHAMA (dariya): Gaskiya maganar aure da ake yaɗawa a kai babu ita. A halin yanzu ni ba matar aure ba ce. Na dai taɓa aure da daɗewa, amma yanzu babu wannan maganar. Don haka mutanen da ke cewa ina da aure a daina mu’amala da ni ta yiwu akwai wani abu a ran su da su ke ɓoyewa ne, shi ne ba su so mutane su yi mu’amala da ni don sun nemi damar ba su samu ba.

FIM: A tunanin ki, me ya kawo wannan maganar?

RAHAMA; A gani na, ba zai wuce hassada ba, ganin irin ka zo babu jimawa an karɓe ka duk da ka na ƙarami, kuma ka na yin abubuwan ka ba tare da ka saurari wani ba. Ko kuma kai da zuwan ka ka samu abin da su sun daɗe su na nema ba su samu ba.

FIM: Ina maganar kan-ta-waye da aka ce ana yi wa mata kafin su samu damar shiga fim? Ya ki ka samu masana’antar? Shin da gaske ne?

RAHAMA: A gaskiya ni dai ban ga wani abu makamancin haka ba. Kuma wasu su na amfani da wannan ne don ɓata wa masana’antar suna. Yawancin mutanen da ke cewa su na kan-ta-waye, da dama ba ‘yan fim ba ne, kawai dai su na amfani da masana’antar ne su na cin karen su babu babbaka, kuma su na cin wani buri nasu. Amma ni gaskiya ban ci karo da irin wannan shirmen ba.

FIM: Ya zuwa yanzu kin cimma burin ki?

RAHAMA: E, to, na dai fara. Amma ina so in zama shahararriyar jaruma kuma fitacciyar mawaƙiya.

FIM: A wani ɓangaren kuma an ce ki na rubutun littafi. Haka ne?

RAHAMA: Wannan magana haka ta ke, na ɗan taɓa rubutun littafi kaɗan. Wasu daga cikin waɗanda na rubuta, kuma su ka fito kasuwa, akwai ‘Wata Uwar Miji’, ‘Rayuwar Najwa’, da kuma ‘Ƙaddarar Zuciya’.

FIM: Labaran ki ƙirƙira ki ke yi ko kuma abubuwan da su ke faruwa ne ki ke rubutawa?

RAHAMA: A cikin labarai na ɗaya ne ƙirƙirarre, amma akwai abubuwan da su ka faru a gaske a ciki.

FIM: A yanzu wane littafi ki ke shirin fitarwa?

RAHAMA: ‘Ni Da Miji Na’.

FIM: Me labarin ya ƙunsa?

RAHAMA: A kan zamantakewar aure ne.

FIM: A kwanakin nan maganar auren ki ta ƙara tasowa, wadda ta tada hankalin mutanen da ki ke hulɗa da ke. Me za ki ce?

Ga hujja: Takardar sakin Rahama a kotu

RAHAMA: Maganar da zan yi ɗaya ce: ni ce dai ake cewa ina da aure, kuma ni na ce ba ni da aure. Sannan duk wani wanda ke kokwanton ina da aure, ya fito ya nemi aure na, daga nan zai tabbatar da ko ina da aure ko ba ni da aure.

FIM: Ki na da shaidar da za ta tabbatar da cewa ba ki da auren?

RAHAMA: Akwai shaida, domin akwai takardar saki ta kotu. Ka ga ina da babbar shaida kenan. Sannan su iyaye na da ‘yan’uwa na sun san cewa babu aure. 

FIM: To, madalla. Rahama, mun gode.

RAHAMA: Ni ma na gode, Malam Abba.

Rahama tare da Musa Maisana’a a lokacin ɗaukar shirin ‘Kunnen Ƙashi’
Rahama Yakawada tare da ƙawar ta Maryam Malumfashi a lokacin ɗaukar shirin ‘Baba Audu’
Rahama Yakawada ta ƙalubalanci duk mai tababar mutuwar auren ta da ya fito ya gwada neman auren ta!

Loading

Tags: jarumaKannywoodmarubuciyamatamawaƙaRahama Aminu Abdullahi YakawadaRahama Yakawada
Previous Post

Jaruman Kannywood sun tara wa ƙungiyar AKAFA aƙalla naira miliyan ɗaya

Next Post

Raliya ta cikin ‘Daɗin Kowa’ ta zama amarya

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Amarya Amina Lawal (Raliya 'Daɗin Kowa') a wajen bikin auren ta

Raliya ta cikin 'Daɗin Kowa' ta zama amarya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!