MATASHIN marubucin finafinai a Kannywood, Najib Abdulazeez Adam, wanda aka fi sani da Najib Marubuci, zai angwance nan da kwanaki kaɗan.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa Khadija Abdulkareem Yakub a ranar Asabar, 12 ga Nuwamba, 2022, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ƙofar gidan baban amarya Malam Abdulkareem Yakub da ke Tsohon Gari, Tudun Shuni, Tudun Wadan Ɗankadai, a Jihar Kano.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Najib ya na ɗaya daga cikin marubutan finafinai da tauraron su ke haske a Kannywood, musamman a Jihar Kaduna.
Shi ne marubucin fitaccen fim ɗin nan mai dogon zango mai suna ‘Da A Ce Ba Zuciya’ na jarumi Abdul M. Shareef.