SHAHARARREN mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa), ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hana amfani da manhajar nan ta TikTok tun kafin lokaci ya ƙure.
Sarkin Waƙa ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a Facebook ranar Asabar.
Naziru ya ce, “Ya kamata gwamnati ta dakatar da TikTok a Nijeriya tun kafin lokaci ya ƙure.”
Mutane da dama a Arewa su na kallon wannan manhaja a matsayin wajen yin abubuwan da su ka saɓa wa addini da al’adu.
Tik Tok na ɗaya daga cikin sababbin kafofin soshiyal midiya inda ake wallafa gajerun bidiyo.

Ban da Sarkin Waƙa, malamai da dama sun daɗe su na nusar da iyaye wajen ganin sun sanya wa ‘ya’yan su ido kan wannan kafa wadda mata su ka fi yin amfani da ita.
A iya jiya da daddare kimanin mutane 657 ne su ka bayyana ra’ayin su a ƙarƙashin wannan saƙon da Sarkin Waƙa ya yi, inda wasu su ke goyon bayan sa wasu kuma su ke sukar sa.
Duk wanda yasoki maganar sarkin waka akan batun tiktok to wlh ya gaggata sawa sanka Questionmark.