MEMBOBIN Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna a yau sun zaɓi Malam Uwaisu Abubakar a matsayin sabon shugaban su.
A yau Asabar, 25 ga Disamba, 2021 aka gudanar da zaɓen a ofishin Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj) da ke Rigachikun, Kaduna.
Sai dai kuma zaɓen ba kaɗa ƙuri’a aka yi ba, yarjejeniya ce (consensus) aka yi, kuma an samu haɗin kai aka gabatar da taron lami lafiya.
Bayan an buɗe taro da addu’a, tsohon ciyaman, Malam Murtala Aniya, ya yi dogon tsokaci a kan muhmancin ƙungiyar ta masu shirya finafinai, sannan ya yi jan hankali a kan fifita manufar ƙungiya tare da sadaukarwa.
Aniya ya nuna cewa dole ne dukkan zaɓaɓɓun shugabannin su zama masu biyayya ga na gaba da su, musamman shugabannin MOPPAN.
Daga wannan kuma sai aka nemi shawarar gida a kan a yi zaɓe ko kuma a ɗaga zuwa wani lokaci. A nan take wasu su ka yi tsokaci a kan cewa babu lokaci a bisa ƙa’idar da babban taron ƙungiya (congress) ta bayar, bisa la’akari da cewa ‘congress’ na gaba da komai.
Hakan ya sa aka fara tantance ‘yan takara inda aka samu wasu abubuwa kamar haka: na farko, akwai wasu waɗanda su ka sayi fom, amma ba su da rijista ƙungiya; na biyu, akwai wasu su na da rijiista da ƙungiya sun yi fosta, amma kuma ba su sayi fom ɗin takara ba.
Ƙungiyar ta yi gudun saɓa wa ‘congress’, sannan kuma ta yi lura da ‘yancin gashin kaida dukkan ƙungiyoyi (guilds) su ke da shi wanda ya hana MOPPAN ta sanya masu baki a cikin batun zaɓen su kamar yadda aka tabbatar a wajen ‘congress’.
Haka kuma ƙungiyar ta lura da cewa ita ce uwa a kan dukkan ‘guilds’, sannan su ke kashe nasu kuɗin wajen shirya fim.
An kuma sake lura da cewa dole ne a kan dukkan membobi na wannan ƙungiya su amsa kiran shugabanta a duk lokacin da ya kira wani taro, sai dai idan akwai uzuri mai ƙarfi.
Waɗannan dalilai ne su ka sa aka zartar da yin zaɓe.
Abubuwan da aka lura da su a wurin zaɓe, na farko, kasancewar mutum memba, sannan da gabatar da shaidar shi ɗin memba ne. Na biyu, tabbacin cewa mutum ya sayi fom, sannan da gabatar da shaidar hakan.
Na uku, an yi la’akari da cewa ana da ɓangarori guda uku a Kaduna: 1. cikin garin Kaduna, 2. Zariya, da 3. Kafanchan.
Ƙungiya ta lura da hakan wajen sulhunta kan ‘yan takara tare da son yin tafiya babu bambanci.
Ga yadda aka raba muƙaman:
Ciyaman – Uwaisu Abubakar – Zariya
Mataimakin Ciyaman – Garba Shehu PS – Kaduna
Sakatare-Janar – Falalu I.M. Sani – Kafanchan
Mataimakin Sakatare Janar – Ibrahim Abubakar
Ma’aji – Yusuf M. Gidaje – Kaduna
PRO – Khalid Gamagira – Kaduna
Sakataren Kuɗi – Aisha Usman – Kaduna
Sakataren Tsare-tsare – Ibrahim Captain – Kaduna
Auditor – Aminu Mirror – Zariya
Welfare – Abubakar Ɗanmasani
Ex-officio:
1. Ibrahim Tahir – Zaria
2. Adamu Ibrahim – Kaduna
3. Musa Shahu – Kafanchan
4. Tukur Alwadawi
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Murtala Aniya, Hajiya Fatima Lamaj, Maiwada Gwanki, Yusuf Gidaje, Garba Shehu PS, Musa Shehu Kafanchan, Adamu Ibrahim, da sauran su.