HUKUMOMI a Nijeriya sun saki wasu ‘yan ƙasar Isra’ila uku da su ka kutsa kai a gabashin ƙasar nan da nufin shirya wani fim kan ‘yan ƙabilar Ibo masu iƙirarin cewa su ma Yahudawa ne.
Jami’an tsaro na rundunar DSS ne su ka kama shugabar ƙungiyar Ibo da ke iƙirarin su Yahudawa ne, Lizben Agha, kimanin wata ɗaya da ya gabata, amma aka sake ta a ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda jaridar ‘Times of Israel’ ta ruwaito shekaranjiya.
Mujallar Fim ta ambato jaridar na cewa jami’an DSS, kowanne sanye da baƙin takunkumin fuska, sun kama Lizben Agha a ranar da aka kama wasu ‘yan Isra’ila uku a ƙauyen Ogidi a ranar 9 ga Yuli, a wajen wata cocin bautar addinin Yahudu, a bisa zargin su na da alaƙa da ƙungiyar ‘yan tawayen a-waren Biyafra, wato IPOB.
Jaridar ta ce an tsare su har kwana 20 ba tare da an bar wani lauya ya gan su ba, sannan ba a kai su kotu ba.

Masu shirya fim ɗin sun ce su ko ita Agha babu wanda ke da alaƙa da ‘yan tawayen ko wata ƙungiyar siyasa.
An kama Agha ne saboda ta na taimaka wa ‘yan fim ɗin na Isra’ila.
Jaridar ta ce da farko ba a kama ta ba, amma lokacin da aka kama ‘yan fim ɗin sai ita ma ta tsaya kai da fata a kan lallai sai ta bi su inda za a kai su domin ta sasanta matsalar, shi ya sa aka haɗa har da ita.
Da farko an faɗa masu cewa wata ‘yar tattaunawa kaɗai za a yi da su.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa waɗanda aka tsare ɗin, wato Rudy Rochman, wanda ɗan gwagwarmayar goyon bayan Isra’ila ne kuma mai mabiya wajen 95,000 a Instagram; da mashiryin fim Andrew Noam Leibman; da ɗan jarida Bayahuɗe ɗan ƙasar Faransa, Edouard David Benaym, sun zo Nijeriya ne domin shirya fim mai suna ‘We Were Never Lost,’ wanda zai dubi zamantakewar al’ummar da ke kiran kan su Yahudawa a ƙasashen Afrika irin su Kenya, Madagaska, Uganda da Nijeriya. Tafiyar da su ka yi a watan Yuli sun shirya ta ne domin ɗaukar fim ɗin a cikin Inyamirai.
Sun iso Nijeriya ne a ranar 6 ga Yuli.

“Lizben mace ce mai gaskiya, mai ban-mamaki,” a cewar Rochman a hirar sa da ‘The Times of Israel’. Ya ƙara da cewa, “Ƙarfin halin ta na ban-mamaki ne, ga ta ƙaƙƙarfa, mai kara, kuma mai alfahari da kasancewar ta Bayahudiya, sannan ta tsaya mana tun da mu ka sauka a can.
“Abin da ya faru gare ta abin tsoro ne — a ce an tsare ta kwana 29 a kurkuku. Mu ma an tsare mu kwana 20 na waɗannan kwanakin, don haka mun san yadda ake ji.”
Su ukun sun riƙa aika mata da wani sashe na abincin Yahudawa (kosher) da ake kawo masu daga gidan limamin addinin su da ke Abuja, wato Chabad, ta hanyar masu gadin su a lokacin da ake tsare da su.
Amma Agha ba ta ci gaba da samun irin wannan abincin ba bayan an saki ‘yan Isra’ilan.
“Na yi magana da Chabad ɗin kafin mu tafi cewa a ci gaba da kai mata abincin. Sun kai abincin sau uku a lokuta daban-daban, amma ‘yan DSS su ka hana ta abincin.”
Rochman ya ce masu shirya fim ɗin ne su ka tara mata kuɗin beli.

A cewar mashirya fim ɗin, shi ma mai masu jagora a ƙasar, wani wai shi Priye Amachree, an damƙe shi kamar mako guda da ya gabata kuma har yanzu ana tsare da shi. Shi kuwa ba Inyamiri ba ne.
Shi ma Amachree, ba a ba shi lauya ba kuma ba a yi masa tuhuma ba, inji Rochman.
A sanarwar da su ka wallafa a Instagram bayan an sako su a ranar 27 ga Yuli, su ukun sun bayyana cewa an kama su an tsare su ba tare da ƙa’ida ba a ranar 9 ga Yuli, 2021 da ƙarfe 7:30 na safe (agogon Nijeriya), aka kai su inda DSS ke aje mutane a Jihar Anambara, inda aka tsare su tsawon awa 24 kafin a maida su hedikwatar DSS da ke Abuja, tafiyar awa tara.
Su ka ce jami’an tsaro sama da dozin, ɗauke da bindigogi ne su ka kama su.

Sanarwar ta ce, “An sakaya Rudy, Noam, da David tsawon kwana 20 a wani yanayi mai ban-tsoro, a kulle a wani ƙaramin sel, su na kwanciya a kan daɓe ba tare da an bar su sun yi wanka ba ko sun canza tufafi. An tattauna da su tare da gallaza masu ba tare da an fito an ce ga dalilin kama su ba.”
A sanarwar, mutanen uku sun ce a ƙarshe an bayyana cewa ba su aikata laifin komai ba, to amma gwamnatin Nijeriya ta umarce su da su bar ƙasar ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Sun yi alƙawarin cewa za su samo wata hanyar da za su bada labarin rayuwar Inyamirai Yahudawa.
* Tare da rahoton jaridar ‘The Times of Israel’