• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nijeriya ta tabbatar wa Amurka da ci gaba da yin riƙo da ‘yancin ‘yan jarida

by DAGA WAKILIN MU
November 27, 2023
in Nijeriya
0
Nijeriya ta tabbatar wa Amurka da ci gaba da yin riƙo da ‘yancin ‘yan jarida

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙara tabbatar wa da gwamnatin Amurka cewa Nijeriya na kan turbar da ta ke a kai ta yin riƙo da ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.

Ya ce akwai buƙatar wannan ‘yanci sosai domin ta hanyar kafafen yaɗa labarai ne dimokiraɗiyya ke ka ƙara karsashi, tasiri da nagarta a cikin zukatan al’umma.

Hakan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman a fannin yaɗa labarai ga ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya fitar a ƙarshen makon jiya.

Ministan ya bayyana haka a lokacin da Babban Jami’in Amurka mai Kula da Al’amurran Nijeriya, Mista David Greene, ya kai masa ziyara cikin makon jiya.

Ya ce: “A yayin da mu ke goyon baya da ɗabbaƙa ‘yancin kafafen yaɗa labarai da na ‘yan jarida, mu na kuma yin kira ga gwamnatin Amurka da ta ba mu goyon baya ta hanyar ƙara zurfafa horaswa ga ‘yan jarida, musamman a fannin binciken tabbatar da gaskiya da fayyace sahihin labari daga labaran bogi.”

Idris ya ƙara da cewa, “Yin hakan zai ƙara rage yawan watsa labaran bogi, bayanan karkatar da hankalin jama’a, da rage bazuwar ji-ta-ji-ta a cikin jama’a.”

Ministan ya jaddada aniyar da Nijeriya ta sa a gaba wajen ƙara wa dimokiraɗiyya daraja da ƙima, ya na mai cewa, “Muhimmin abu ne a matsayin Amurka na babbar ƙawar Nijeriya ta ƙara zurfafa goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan.”

A jawabin sa, Mista Greene ya ce Amurka na goyon bayan Nijeriya ɗari bisa ɗari wajen inganta dimokiraɗiyya da inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai.

Ya ce an keto shekaru da dama ƙasar sa ta na bayar da guraben ƙaro ilmi, bada horaswa da kuma fannin inganta tsaro.

Loading

Tags: Mohammed Idris Malagi
Previous Post

Furodusa Abdul Amart ya saya wa iyalan darakta Aminu Bono gida, Rarara kuma ya ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan marigayin

Next Post

Gwamnatin Tarayya za ta fito da manhajar DSO na aikin talbijin kwanan nan – Minista 

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya za ta fito da manhajar DSO na aikin talbijin kwanan nan – Minista 

Gwamnatin Tarayya za ta fito da manhajar DSO na aikin talbijin kwanan nan – Minista 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!