JARUMIN barkwanci a Kannywood, Nura Yakubu (Ɗandolo ko Yaya Ɗanƙwanbo a yanzu), ya aurar da ‘yar sa a ranar Lahadi, 20 ga Nuwamba, 2022.
An ɗaura auren Murshida Nura Yakubu da sahibin ta, Yaƙuba Muhammad Lawal Maiharawa, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin filin Kashu da ke Unguwa Uku, Kano, a kan sadaki N40,000.

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci bikin sun haɗa da Falalu Ɗorayi, Aminu Mirror, Nazir Adam Salih, Umma Shehu, da Hauwa Ayawa.
Nura Yaya Ɗanƙwambo ya yi godiya ga abokan sana’ar sa da ‘yan’uwa da abokan arziƙi.
Haka kuma ya shaida wa mujallar Fim cewa lallai ya daɗe bai yi farin ciki irin na wannan rana ba saboda “yadda aka yi taro lafiya, aka tashi lafiya, amarya ta na murna, iyaye su na murna.”
Ya ƙara da cewa: “Wannan ita ce ‘ya ta ta uku da na aurar. Na gode ƙwarai da gaske.”


Allah ya sanya alkhairi.,
Muna Taya Yaya Ɗanƙwambo murnar biki.
Allah ya bada xaman lpy daga Ahmad Umar Dan oga kundulum