• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa mu ka haramta finafinan Indiya masu fassarar Hausa – Gwamnati

by DAGA ALI KANO
November 21, 2022
in Labarai
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta jaddada dalilin ta na haramta finafinan Indiya da ake fassarawa da Hausa.

A cikin wata sanarwa da Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta bayar a yau, mai ɗauke da sa-hannun shugaban shiyyar Arewa-maso-yamma na hukumar, Alhaji Umar G. Fage, gwamnatin ta ce fassara finafinan ya saɓa wa dokar ta ne.

Takardar sanarwar da hukumar ta turo wa mujallar Fim, mai taken “Fassarar Finafinan Indiya Da Hausa”,  ta na ɗauke da kwanan wata 15 ga Nuwamba, 2022.

A ciki ta faɗa wa masu harkar finafinai cewa: “Doka ta 85 ta 1993 wato ‘CAP N40 LFN 2004 da Ƙa’idojin 2008’, a ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Al’adu ta Tarayyar Nijeriya, ita ce ta kafa Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa.

“Hukumar ta na da hurumin tsaftace ayyukan fim da bidiyo (wato masana’antar nishaɗantarwa).

“Aikin hukumar ne kamar haka:

Alhaji Umar G. Fage

“Ta ba da lasisi ga mutum ya bayyana ayyukan sa na fim da bidiyo; ta ba da lasisi ga gida domin nuna ayyukan fim da bidiyo; ta tace ayyukan fim da bidiyo; ta tsaftace tare da kafa ƙa’idojin kula da lafiya a wuraren haska su; ta tsaftace tare da sanya ido kan abubuwan da ake haskawa a gidajen sinima; kuma ta gudanar da duk wasu ayyuka makamantan waɗannan da aka ga sun zama tilas ko sun dace wajen cikakkiyar gudanuwar dukkan ko wani haƙƙi da wannan dokar ta ɗora mata.

“A bayyane ya ke ƙarara cewa dokar ta bayyana abubuwa kamar haka:

“Ba a yarda wani mutum ya shiga harkar rabawa ko nuna wani aikin fim ko na bidiyo ba har sai ya samu lasisin yin hakan daga hukumar.

“Ba a yarda wani mutum ya nuna ko ya sa a nuna wani fim ba tare da ya samo satifiket ɗin tacewa daga hukumar domin ya nuna shi ba.

“To amma ofishin shiyyar Arewa-maso-yamma na hukumar ya lura tare da damuwa ƙwarai kan yadda wasu mutane su ka shiga harkar kwafa, fassarawa, da rarraba finafinan ƙasashe waje zuwa harshen mu na gado, wanda yin hakan ya saɓa wa sashe na 25(1), 33(1), 56 da 1(3) 5(1) na dokar da ta kafa hukumar, wato Dokar 1993 CAP N40 LFN 2004 da Ƙa’idojin 2008.

“A bisa wannan sanarwa, hukumar ta gargaɗi irin waɗannan mutanen da su kiyayi aikata abin da su ke yi wanda ke iya jawo matsala ga masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya.

“Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa ba za ta iya ci gaba da amincewa da wannan abu ba daga kowane mashiryin fim maras gaskiya.

“Fassarar finafinan Indiya zuwa Hausa ya saɓa wa doka, kuma duk wanda aka kama ya na aikata hakan zai fuskanci shari’a.

“Don haka wannan gargaɗi ne gare ku. Mun gode.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa hukumar ta aika da sanarwar ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar fim irin su furodusoshi, daraktoci, masu sayar da fim, masu nuna fim, da ƙungiyoyin ‘yan fim.

Loading

Tags: dokafassarar finafinaifimgwamnatiHukumar Tace FinafinaihukunciIndiyaNFVCBUmar G. Fage
Previous Post

Nura Ɗandolo ya aurar da ‘yar sa ta uku, Murshida

Next Post

KILAF 2022: Yau za a fara Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Fostar taron KILAF na bana

KILAF 2022: Yau za a fara Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!