• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

KILAF 2022: Yau za a fara Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 22, 2022
in Labarai
1
Fostar taron KILAF na bana

Fostar taron KILAF na bana

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Talata, 22 ga Nuwamba, 2022 za a buɗe Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF),  kashi na 5 a birnin Kano.

Bikin, wanda ake shiryawa a kowace shekara, za a buɗe shi da yamma a Hukumar Raya Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano da ke Gidan Ɗanhausa.

Za shafe tsawon kwana biyar ana gudanar da bikin, wato daga yau zuwa ranar 27 ga Nuwamba.

A cikin waɗannan kwanakin za a gudanar da abubuwa da dama da su ka shafi kasuwanci da kuma harkokin cigaban harkar fim a ƙasashen Afirka.

Ana sa ran taron zai samu halartar jama’a daga ƙasashe da dama daga Afirka da Turai.

Alhaji Abdulkareem Muhammad

A lokacin da ya ke yi wa mujallar Fim bayani game da taron na bana, shugaban shirya taron, Malam Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa: “Duk da yake wannan taron shi ne karo na biyar da mu ka shirya, saboda darrusan da mu ka samu a baya hakan ya sa mu ka samar da abubuwan da su ka bambanta ta hanyar cigaba fiye da na baya.”

Ya ci gaba da cewa, “A wannan shekarar mun samu finafinai daga ƙasashen takwas da su ka shiga gasar kuma wannan shekarar ita ce aka samu finafinai masu yawan da su ka kai sama da tamanin waɗanda su ka fito daga ƙasashen Afirka ta Kudu, Fotugal, Kenya da Amurka, kuma duk an yi su ne da harsunan mu na Afirka.

“Baya ga haka, akwai taron sanin makamar aiki da aka shirya da kuma maƙaloli da za a gabatar a Tsangayar Aikin Jarida da ke B.U.K., kuma masana ne daga manyan jami’o’i na duniya za su gabatar, wasu a wajen, wasu kuma ta allon ga-ni-ga-ka. 

“Sannan kuma akwai kallon finafinai da za a yi a sinima da kuma yawon buɗe ido ga baƙin mu da kuma cin abincin gargajiya na Afirka. 

“Don haka a tsawon kwanaki biyar ɗin da za a yi duk za a gudanar da abubuwa na ilimi da nishaɗantar da jama’a, wanda kuma a rana ta ƙarshe za a bayyana sunayen finafinan da su ka ci gasar da kuma ba su kyautuka tare da karrama mutanen da su ka bayar da gudunmawa a harkar cigaban harkar fim a nan gida da ma Afirka baki ɗaya.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa taken bikin na bana dai shi ne: “Interrogating Change in African Cultures and Traditions through African Indigenous Language Films,” wato “Bin Bahasin Sauyin Da Ke Wanzuwa Cikin Al’adun Afrika ta Hanyar Finafinan Harsunan Gado na Afrika”.

Loading

Tags: Abdulkareem Muhammadbikin baje-kolin finafinaibuɗe tarofilm festivalGidan Ɗanhausaharsunan Afrikaharsunan gadoKanoKILAF
Previous Post

Abin da ya sa mu ka haramta finafinan Indiya masu fassarar Hausa – Gwamnati

Next Post

Magoya bayan Atiku sun yi wa taron gwamnonin PDP ‘yan G5 ƙafar angulu a Legas

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Gwamnonin G5 a wurin taron su a Legas

Magoya bayan Atiku sun yi wa taron gwamnonin PDP 'yan G5 ƙafar angulu a Legas

Comments 1

  1. Lami Hafsat Maccido says:
    4 years ago

    Salam,Alhamulillah,da muka kawo wannan Gabar a Harkar Fina finai,musamman na Harshen,Kasashenmu na Afirka.Malam Abdulkareem ku kara zage Dantse,dan ganin Cigaban wannan Masana’anta tamu.Ayi Biki lfy.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!