SHAHARARRIYAR jaruma a Kannywood da Nollywood, Hajiya Rahama Sadau, ta saka murmushi da annashuwa a fuskokin jaruman Jihar Kaduna.
A yau Alhamis ne jarumar ta tara ɗimbin ‘yan fim na jihar domin ba su barka da Sallah.
An gudanar da taron harabar Abdulkarim Plaza da ke Mogadishu Layout, Kaduna, kusa da ofishin darakta Nasiru Ali Ƙoki (Shehu Jaha).
Rabon barka da Sallah ɗin ya samu jagorancin wakilin ta ne, wato jarumi Yusuf Lazio, wanda a yanzu shi ne na hannun damar ta a Kannywood, sai kuma yayan ta Abba Sadau.
Tun da farko, Lazio ya yi taƙaitaccen jawabi kafin fara rabon, inda ya ce, “Ina yi wa kowa barka da zuwa, sannan ina mai ba da haƙurin rashin farawa da wuri.”
Ya ce, “Haƙiƙanin gaskiya a Jihar Kaduna ba mu da wanda ya wuce Rahama Sadau, domin abin da take yi, a Kano an daɗe ana yi masu irin wannan. Mu kuma a Kaduna ma da kowa, daga Allah sai Rahama Sadau.
“Magana ta gaskiya, raguna ta so ta raba tun kafin Sallah, sai ta ga gaskiya ba za su isa ba, akwai waɗanda muka jira za a kawo ba a kawo ba, shi ne kawai ta ga tunda Sallah ta wuce, bari kawai ta ba da barka da Sallah.”

Bayan jawabin nasa , sai aka shiga abin da ya tara mutane a wurin. Rabon an yi shi cikin tsari, inda aka rinƙa bin mutane ɗaya bayan ɗaya ana ba su barka da Sallar su, inda kowa ya rabauta da N10,000.
Aƙalla an samu mutane sama da ɗari biyar a wurin.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa wannan taro ya bar tarihi, domin an sada zumunci da juna; da ma wasu sun daɗe ba su ga juna ba, wasu ma ko lambar wayar juna ba su da ita, amma a yau sun sake haɗuwa.
An yi wa jarumar addu’o’i kala-kala a wurin. Kuma wakilan nata sun yi dukkan abin da ya dace.