• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rahama Sadau ta samu muƙami a gwamnatin Tinubu 

* Yadda 'yan Kannywood za su ci moriyar naɗin da aka yi mata

by IRO MAMMAN da ABBA MUHAMMAD
April 4, 2024
in Labarai
0
Rahama Sadau ta samu muƙami a gwamnatin Tinubu 

Hajiya Rahama Sadau a wajen taron ƙaddamar da kwamitin iDICE jiya a Abuja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMA a Kannywood da Nollywood, Hajiya Rahama Sadau, ita ma ta samu shiga cikin gwamnatin Tinubu.

Gwamnatin ta naɗa jarumar ne cikin kwamitin gudanarwa na Shirin Zuba Jari a Harkokin Intanet Da Fasahar Ƙirƙira, wato Investment in Digital and Creative Enterprise (IDICE).

Manajan-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya NFC) kuma jarumi Ali Nuhu, shi ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya a daren jiya.

Tun da farko sai da ya taya ta murnar samun muƙamin, ya ce, “Ina ƙara taya murna ga tamu, Rahama Sadau.”

Sannan ya biyo da bayanin cewa: “Gwamnatin Tarayya ta naɗa Rahama Sadau ta yi aiki a kwamitin gudanarwa na shirin IDICE (Investment in Digital and Creative Enterprise).

“Kwamitin ya na da matsayi na biyu mafi girma a cikin shirin IDICE ɗin, kuma aikin sa shi ne ba da taimako na dabaru, fasaha, da aiki ga Sashen Gudanar da Shirye-shirye (Programme Coordination Unit, PCU) da Hukumar Ba Da Shawara Ga Asusu (Fund Advisory Board) na shirin.”

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Kashim Shettima, ya ƙaddamar da kwamitin a Abuja.

Rahama dai ita ce ta biyu daga Kannywood da gwamnatin Tinubu ta ba muƙami. Na farkon shi ne shi kan shi Ali Nuhu, wanda aka naɗa darakta-janar na NFC.

Alhaji Kashim Shettima da ‘yan kwamitin su Rahama Sadau bayan ya ƙaddamar da su jiya a Abuja

Mujallar Fim ta binciko cewa wannan asusun na IDICE wani gagarumin shiri ne na Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na ba da tallafi ga matasa mata da maza (‘yan shekaru daga 15 zuwa 35), domin haɓaka harkar kasuwancin su a ɓangarori biyu, wato harkokin intanet da masana’antun fasahohin ƙirƙira irin su waƙa da shirya fim, inda za a samar da aikin yi.

Gwamnatin Nijeriya da haɗin gwiwar Bankin Cigaban Afrika (ADB) tare da wasu hukumomin ƙasa da ƙasa ne su ke tara kuɗin gudanar da shirin.

A tsarin ɗaukar nauyin shirin, ADB da hukumomin za su ba da gudunmawar dala miliyan 216, inda ADB zai ba da $170 miliyan; Hukumar Cigaba ta Faransa, wato Agence Française de Développement, €100 miliyan ($116 miliyan); sai Bankin Cigaba na Islama (Islamic Development Bank), $70 miliyan.

Ita kuma gwamnatin Nijeriya, ta hannun Bankin Masana’antu (Bank of Industry, BOI) za ta ba da nata kason na $45 miliyan ta hanyar ba da rance ga sababbin kamfanonin matasa da su ka cika ƙa’idoji.

An ƙaddamar da shirin na IDICE ne a zamanin mulkin Buhari, a ranar 13 ga Maris, 2023.

A wajen taron ƙaddamarwar a Abuja, Shugaban bankin na ADB, Mista Akinwumi Adesina, ya yi bayani kan muhimmancin asusun na IDICE wajen samar da aikin yi da gina tattalin arziki. Ya ce: “Mu na ƙara wa Nijeriya ƙarfi saboda ta haɓaka kan ta a duniyar da ake tsere a fagen fasahar intanet. Mu na samar da sabuwar fata ga sabuwar Nijeriya, saboda ƙarfin tasiri da matasa ke da shi.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa shigar Rahama Sadau cikin wannan kwamiti wata babbar dama ce ga ‘yan Kannywood domin za ta iya yi masu jagora kan yadda za su ci moriyar shirin na IDICE.

Duk wanda ke son cikakken bayani game da asusun da yadda ake cin moriyar sa sai ya duba sashen bayanin iDICE ɗin a gidan yanar bankin ADB, wato:

https://www.afdb.org/en/news-and-events/frequently-asked-questions-idice-project-59933.

Rahama a taron ƙaddamar da kwamitin

Loading

Tags: ADBasusuiDICERahama Sadau
Previous Post

Gwamnatin Kano ta hana shirya fim kan daba ko ‘yan daudu

Next Post

Kiran furodusa Iyan-Tama ga Tinubu: Ka dakatar da komai sai an samu tsaro a ƙasa

Related Posts

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Next Post
Kiran furodusa Iyan-Tama ga Tinubu: Ka dakatar da komai sai an samu tsaro a ƙasa

Kiran furodusa Iyan-Tama ga Tinubu: Ka dakatar da komai sai an samu tsaro a ƙasa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!