Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya jaddada muhimmancin raya al’adun gargajiya da kuma bunƙasa su domin amfanin matasa da ‘yan baya.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke da nasaba da bunƙasa al’adu da kuma ilimantar da jama’a game da su.
Gwamnan ya bayyana haka ne a taron bikin Ranar Al’adun Gargajiya ta Duniya wanda ake yi duk ranar 3 ga Agusta na kowace shekara.
Ma’aikatar Raya Al’adun Gargajiya da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano ce ta shirya taron, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Fadar Gwamnatin Jihar Kano, wato Coronation Hall.
Gwamnan ya ce: “Al’adu su ne ginshikin kowacce al’umma. Idan muka rasa su, to kamar mun rasa tushe ne.

An gudanar da taron ne domin tunawa da muhimmancin al’adu da kuma ƙara wayar da kai game da rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban al’umma.
A jawabin da ta gabatar kan manufar taron, Kwamishinar Raya Al’adun Gargajiya da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano, Hajiya A’isha Lawan Saje Rano, ta bayyana al’adun gargajiya a matsayin wani tushe na cigaban al’umma wanda hakan ya sa aka ware duk ranar 3 ga Agusta domin yin bikin Ranar Al’adun Gargajiya ta Duniya.

Ta ce: “Don haka ne a wannan shekara muka bai wa ranar muhimmanci domin nuna wa mutane, musamman matasan mu, muhimmancin wannan rana. Manufar mu dai ita ce koyar da al’umma ci gaba da riƙo da al’adun gargajiya.”



A taron, Ma’aikatar Raya Al’adun Gargajiya da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano ta shirya baje-kolin kayayyakin gargajiya da al’adun Hausawa wanda ya haɗa da wasannin gargajiya, raye-raye, kiɗan gargajiya da kuma nune-nunen sana’o’in hannu na mutanen Kano, lamarin da ya ƙara ƙayatar da mahalarta taron.
Taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, ciki har da shugabannin al’umma, malamai, da masu ruwa da tsaki a harkar raya al’adu.
![]()






