ƘARSHEN tika-tika, tik! Cikin hukuncin Allah, a yau Asabar shahararriyar jarumar Kannywood da Nollywood, Hajiya Rahama Sadau, ta yi aure.
An ɗaura auren ta da sahibin ta mai suna Alhaji Ibrahim Garba, wani mazaunin Abuja, da misalin ƙarfe 10:30 na safe a masallacin kusa da gidan mahaifin ta mai suna Atiku Garba da ke Titin Lome, Unguwar Rimi, Kaduna, a kan sadaki N300,000.
Sai dai auren an yi shi ne ba tare da gayyatar jama’a ba.
Mutane da dama sun yi mamakin jin cewa an ɗaura wa jarumar aure.
Hatta wakilin mujallar Fim da aka kira shi aka sanar da shi labarin auren, sai da ya ƙara tambayar cewa ita ce ko ƙanwar ta, aka tabbatar da cewa ita ɗin ce.
Daga nan ya kira wani makusancin ta, wanda ya tabbatar masa da cewa lallai ita ce aka ɗaura wa aure.
A cikin makon nan an yi ta yaɗa labarin cewa ƙanwar ta Fatima ta auri wani Salim Gode, inda shi Salim ɗin ya ƙaryata.
Haka kuma an ga bidiyon wasu ƙannen nata, Zainab da A’isha, suna zolayar Fatima a cikin mota da cewa yanzu tunda tana da miji ta nemi izinin sa kafin ta sha zoɓon da Zainab ta ba ta a cikin raha. Sai dai kuma ita ma gabu tabbacin auren nata.
Wakilin mu ya yi ƙoƙarin ganin ya samu Rahama a waya, amma hakan bai yi nasara ba.
Rahama Sadau tana daga cikin fitattun jaruman Kannywood ‘yan mata waɗanda aka daɗe ana jiran ganin ranar auren su.
Ta yi aure wata ɗaya da rabi bayan rasuwar mahaifin ta, Alhaji Ibrahim Sadau, wanda Allah ya karbi ran sa a ranar 22 ga Yuni, 2025.
Yanzu za a iya cewa ta karya ƙwarin rashin yin auren ‘yan matan gidan su su huɗu waɗanda ake kira da Turanci The Sadau Sisters. Dukkan su sun fito a shirin fim.
Allah ya ba Rahama da mai sunan babban ta zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
![]()







