MANAJAN Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da a haɗa hannu domin a samu cigaba a ƙasar baki ɗaya da haɗin kai, babu bambance-bambance.
Shugaban ya wallafa saƙon ne a dukkan shafukan sa na soshiyal midiya a cikin saƙon taya Nijeriya murnar Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, wadda ake gudanarwa a yau 12 ga Yuni.
Ali ya ce: “Mu haɗa hannu don samar da Nijeriya da za ta haskaka da kuma samun damarmaki.
“Tare, za mu wargaza shingen da ke raba mu, da haɓaka al’adar haɗin kai da fahimta.
“Yayin da mu ke bikin Ranar Dimokiraɗiyya, mu na jaddada aniyar mu ta gina ƙasa dunƙulalliya, inda ake jin kowace murya kuma kowane mafarki ya na da damar bunƙasa.
“Haɗin kai duk da bambance-bambancen mu zai share mana hanya don samun makoma mai cike da alƙawari da cigaba ga kowa.”