• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ranar Rediyo ta Duniya: Minista na so gidajen rediyo su wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi

by ALI KANO
February 13, 2025
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga jihohi da kada su rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga gidajen rediyo a faɗin Nijeriya da su yi amfani da kafafen su wajen ilimantar da jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa.

A cikin wata sanarwa da ya baya domin bikin Ranar Rediyo ta Duniya ta 2025, wadda ake gudanarwa a duk shekara a ranar 13 ga Fabrairu (yau kenan), Idris ya jaddada muhimmancin rediyo wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa su don ɗaukar matakan da za su daƙile matsalar sauyin yanayi.

Taken ranar ta bana, wato “Rediyo da Sauyin Yanayi,” yana nuni da buƙatar gaggawa na ɗaukar matakan magance matsalolin muhalli da ke shafar Nijeriya da duniya baki ɗaya.

Ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli.

“A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.”

Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron duniya kan yanayi (COP29) na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na ƙasar Azerbaijan inda Shugaban Ƙasar ya yi bayanin yadda Nijeriya take fama da matsalar sauyin yanayi da matakan da gwamnati ke ɗauka don rage fitar da hayaƙin da ke dagula yanayi, ƙarfafa juriya, da shigar da hanyoyin magance matsalar cikin tsare-tsaren ƙasa.

Idris ya yi kira ga gidajen rediyo a Nijeriya da su gabatar da shiryayyun bayanai da ilimantarwa kan sauyin yanayi, su haɗa kai da masana, da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin isar da ingantattun bayanai ga jama’a.

Ya ce: “Ta hanyar shirye-shiryen ilimantarwa da bayanai, za mu iya bai wa al’umma ilimi da kayan aiki da za su taimaka masu wajen daidaita kan su da sauyin yanayi da kuma rage tasirin sa.

“Haka nan, yana da matuƙar muhimmanci ga gidajen rediyo su haɗa kai da ƙungiyoyi da masana a fannin sauyin yanayi don samar da ingantattun bayanai ga masu sauraro.

“Ta hanyar tattaunawa da masana kimiyya, da ƙwararru a fannin muhalli, da masu tsara manufofi, za mu ƙarfafa fahimtar mu game da wannan matsala tare da nemo hanyoyin magance ta, bisa la’akari da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Ministan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su duba halayen su na yau da kullum da kuma yin ƙananan canje-canje domin yaƙi da sauyin yanayi, kamar rage amfani da robobi, rage amfani da makamashi ko wutar lantarki, da haɓaka noma mai ɗorewa.

Har ila yau, ya jaddada cewa matsalar sauyin yanayi ba ta tsaya a wata ƙasa kaɗai ba kuma tana buƙatar haɗin gwiwar ƙasashe daban-daban don samar da mafita mai ɗorewa.

Yayin da yake taya UNESCO murna bisa ƙirƙirar Ranar Rediyo ta Duniya, Idris ya tabbatar da cewa gwamnati tana da niyyar amfani da rediyo don kawo sauyi mai kyau a cikin al’umma.

Ya ce: “Mu yi amfani da ƙarfin rediyo don kawo sauyi mai kyau a cikin al’ummomin mu da kuma yaƙi da mummunan tasirin sauyin yanayi.

“Ta hanyar haɗin gwiwa da himma tare, za mu iya gina Nijeriya mai ɗorewa da juriya.

“A wannan rana ta Ranar Rediyo ta Duniya, mu yi alƙawarin kawo sauyi da kare duniyar mu domin amfanin zuriyar da ke tafe.”

Loading

Tags: Mohammed IdrisRanar Rediyo ta Duniyayanayi
Previous Post

Gwamnatin Tarayya na ɗaukar matakai don rage farashin abinci ta hanyar zuba jari a noma – Idris

Next Post

Hoto: Jami’an Gwamnati Suna Jiran Isowar Shugaban Nijeriya A Habasha

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Hoto: Jami’an Gwamnati Suna Jiran Isowar Shugaban Nijeriya A Habasha

Hoto: Jami'an Gwamnati Suna Jiran Isowar Shugaban Nijeriya A Habasha

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!