SHAHARARREN mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya ja hankalin mawaƙa da su kama wata sa’ar bayan waƙa.
Rarara ya yi wannan jan hankali ne yayin taron sada zumunci da ya haɗa wa mawaƙan da su ka yi masa waƙoƙi.
Mawaƙin ya ce, “Ina godiya ga dukkan mawaƙan da su ka halarci wannan taro. Da ma na kira taron ne don mu ci abinci, mu gaisa, sannan mu yi zumunci, sannan in ba da shawara.
“Ina godiya, mahaifiya ta Hajiya na godiya, iyali na ina godiya. Ni na san dukkan da ku ka yi min waƙa ba don wani abu ku ka yi ba, ƙauna ce.”
Ya ci gaba da cewa, “Alhamdu lillahi, wannan taro ba tun yanzu na so a yi shi ba, sai an saka lokaci, sai a ɗaga saboda a lokacin ana siyasa, ban zauna ba; yau ina Abuja, gobe Kaduna, Maiduguri da sauran su. Wannan lokacin na ga ya dace tunda ina nan, na kira ku mu gaisa.

“Ina mai ba ku shawara da ku kama wata sana’a bayan waƙa. Rarara ba waƙa ya ke yi ba kaɗai, ina kasuwanci da wasu harkokin, don haka ku yi ƙoƙari ku riƙa wata sana’a bayan waƙa. A lokacin da na zo Kano da robar bara na na zo, ni ƙolo ne, na yi tallar rake, amma yanzu sai dai a ce tirela kaza aka saya na rake, sai dai in ga alert kawai ina zaune.
“Sannan wannan guruf na Tsangayar Mawallafa, ina so ta koma ƙungiya. Zan zauna da jagororin wannan guruf, haka kuma zan zama uba a wannan ƙungiya.
Yayin da ya ke ba da labarin yadda ya haɗu da Fati Mai Zogale, Alhaji Dauda ya ce ya je sayen zogale ne, sai Fatin ta nuna farin cikin ta na ganin mawaƙin da ta daɗe ta na son gani. Sai abokin shi da su ka je tare ya ce sai a yi mata waƙa. “Sai na ce ‘Fati Fatima Mai Zogale’. Daga wannan kalma ya tsaya a cikin kai ne ko da yaushe ina jin shi. Ranar na kira a yi min kiɗan wata waƙa, sai kawai waƙar Fati ke kai na, sai na ce yi min kiɗan ‘Fati Fatima Mai Zogale’.
“Waƙar Fati ta na daga cikin waƙar da ban ɗauke ta komai ba, amma ga ta nan yanzu ita ce ta huɗu da aka fi saurare a faɗin Nijeriya; yanzu ma ita ce ta uku, kuma ita ce waƙar Hausa a cikin waƙoƙin.
“To, kun ga yadda Allah ya ke lamarin sa. Ta yiwu a cikin ku akwai Rarara ko Shata ban sani ba.”

Daga ƙarshe, Rarara ya ƙara godiya ga mawaƙan. Sannan ya ce a yi haƙuri, wannan taron shi ne na farko, kuma ya kira ne a ci abinci a yi zumunci. Don haka wannan taron ba komai aka yi ba, nan gaba za a ƙara kiran wani taron.
An fara taron da misalin ƙarfe 1:30 na rana a ɗakin taro na Water Fall da ke Sharaɗa, Kano.
Bayan an buɗe taron da addu’a, Alhaji Abdullahi Al-Hikima ya yi jawabin maraba.

Daga nan kuma sai aka fara kiran manyan mawaƙan Rarara su ka nishaɗantar da taron da waƙoƙin da su ka yi masa ɗaya bayan ɗaya. Sai kuma aka kira mawaƙan gargajiya su ma su ka baje kolin su.
Haka kuma an gabatar da Malama Fatima Mai Zogale a wurin, sannan aka kira Abbany, ɗaya daga cikin mutanen da ke kama da Rarara, ya nishaɗantar da taron tare da ita Fatima Mai Zogale ta na zaune a kujera shi kuma ya na mamin ɗin waƙar da jita a hannun sa.

Mawaƙan da su ka yi wa Rarara waƙa aƙalla sun haura mutum ɗari uku maza da mata. Amma an samu sama da ɗari da hamsin sun halarci taron. Wannan ya sa aka yi wani tsari, tunda ba zai yiwu kowa ya zo ya hau waƙar sa a wurin ba.
An yi guruf-guruf na mutum biyar, inda za a kawo ƙananan takardu a nannaɗe, sai kowane mutum ɗaya ya ɗauki ɗaya, wanda ya ɗauki sifiri, bai ci ba, wanda ya ɗauki ɗaya shi ya ci, don haka shi ne wanda zai gabatar da waƙar sa da ya yi wa Rarara a wurin.
Haka aka ci gaba da yi, amma duk da haka wasu ba su samu gabatar da waƙoƙin su ba duk da yake sun ci.
Bayan nan sai kuma aka yi shutin ɗin waƙar Fati Mai Zogale a wurin tare da A’isha Ahmad Idris (A’ishatulhumaira), wanda darakta Sadiq M. Mafia ya ba da umarni.
Ɗaukar waƙar ya ƙayatar sosai, duba da yadda aka yi amfani da mutanen da ke cikin ɗakin taron.
Bayan an gama ɗaukar waƙar ne Rarara ya yi bankwana da baƙin sa, ya fice daga ɗakin taron ya nufi gida.

Tun farko mawaƙin ya ce wa baƙin nasa su yi haƙuri za a ba su kuɗin mota. Da ya so ya yi kacici-kacici a cikin mawaƙan da su ka samu damar gabatar da waƙoƙin su, amma sai ya tambayi sauran mawaƙan da cewa ko kar a yi? Wasu na cewa a yi, wasu kuma na cewa kar a yi, masu cewa kada a yi su su ka yi rinjaye. Nan take ya fara yin kaci-kacin, ya kuma ce sauran mawaƙa ba za su ji daɗi ba, domin su ma duk sun yi waƙa, zai zama kamar an ware wasu ne an yi masu kyauta, an bar wasu. Ya ce, “Waƙoƙin ne da na ji na wannan sai in ce wannan ne, da na ji wata sai in cire wancan in sa wannan.”



Rarara ya yi ƙoƙari matuƙa, domin duk baƙin da su ka halarci taron sai da aka ba kowa ɗaki a otal da kuma abinci, sannan kuma aka ba kowa kuɗin mota.
Wannan taro dai an shirya shi ne don mawaƙan da su ka yi wa mawaƙi Rarara waƙa kamar yadda ya ke yi wa mutane. Kuma a tarihin Kannywood ba a taɓa samun mutum da aka yi masa waƙoƙin masu yawan na Rarara ba.
Ƙudirin Rarara a kan mawaƙan shi ne a yi ƙungiya wadda za ta riƙa tafiya tare da su domin taimaka masu.
Sannan ya yi gargaɗi da cewa dole sai mawaƙi na da wata sana’ar, sannan za a tafi da shi a ƙungiyar Tsangayar Mawallafa.

Wani abin burgewa a wurin taron shi ne Fati Mai Zogale ta kwashi masoya maza da mata, kowa so ya ke ya yi hoto da ita.