HARKAR rubutun littattafan Hausa ta daɗe da rikiɗa domin a yayin da yawancin tsofaffin marubuta su ka janye daga fagen, su ka zura ido, kusan dukkan sababbin marubuta ‘yan onlayin ne. Har ta kai idan makaranci ba ya shiga intanet sai ya ɗauka ma babu marubuta a yau. Marubutan onlayin su ke yin tashe, su aka sani, kuma su ne ke samun kuɗi da rubutu.
Firdausi Muhammad Sodangi ta na ɗaya daga cikin irin waɗannan marubutan. Ta rubutu littattafai masu yawan gaske, wanda hakan ya sa ta zama fitacciyar marubuciyar da masu karatu da yawa su ke bibiyar rubutun ta a dandalin zamani na duniya.
Mujallar Fim ta tattauna da Firdausi domin jin tarihin ta da ruƙuƙin da ta ratso har ta kawo inda ta ke a yau.
FIM: To da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
FIRDAUSI MUHAMMAD: Ni dai suna na Fiddausi Muhammad Sodangi, kuma haifaffiyar garin Katsina daga Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa. Na yi karatun boko da na addini, na yi sauka a shekarar 2007. A ɓangaren karatun boko kuma na yi difloma ɗi ta a ‘Hassan Usman Katsina Polytechnic’ inda na karanci ‘Mass Communication’. Daga nan kuma na tafi A.B.U. Zariya inda nan ma na ɗora da ‘Mass Communication’. Wannan shi ne tarihi na a taƙaice.
FIM: Tun a wane lokaci ki ka fara yin rubutu?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Na fara rubutu ne a shekarar 2013. Kuma na samu kai na a matsayin marubuciya ne ta hanyar karance-karance. Ni mace ce ma’abociyar karance-karance, tun daga kan na Turanci har zuwa na Hausa, daga nan na samu kai na da sha’awar yin rubutu da son zama marubuciya. Da haka na fara rubutawa a littafi ina ajewa har ƙawaye na su ka fara karɓa su na karantawa su ce ya yi daɗi. A lokacin ban san ta yadda zan yi in buga ba. Sai bayan an fara rubutu a yanar gizo sannan ne ni ma na samu damar farawa.

FIM: Ko kin taɓa buga littafi kin shigar da shi kasuwa?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: A’a, ban taɓa buga littafi ba gaskiya, sai dai a onlayin kawai Amma yanzu haka ina shirye-shiryen buga littattafai na guda biyu, ‘Wa Ya Kashe Ruƙayya?’ da kuma ‘Mugun Sartse’.
FIM: Ta wace hanyar ake samun kuɗi a rubutun onlayin?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Ana samun kuɗi ne ta hanyar sayar da labaran a wasu manhajoji, kamar Arewabooks, Okada, Telegram, da kuma Whatsapp. Amma gaskiya mun fi samun kuɗi a manhajar Whatsapp saboda ba ko wane makaranci ba ne ya ke iya zuwa can manhajojin don sayen littafi ba, saboda su na ganin matakan da ake bi kafin a kai ga sayen littafin su na da ɗan tsauri.
FIM: Ko yaya alaƙar ku ta ke da marubutan littafi waɗanda a yanzu ake ganin su kamar tsofaffin marubuta?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Mu na da kyakkyawar alaƙa a tsakanin mu da marubuta masu buga littafi, saboda dai duka sunan mu marubuta, kuma abu ɗaya mu ke yi shi ne isar da saƙo. Sannan kuma da yawa marubuta masu buga littafi sun dawo rubutu a onlayin, saboda yanzu dai kasuwar ta fi ci a onlayin ɗin.
FIM: A wane lokaci ki ka fi jin daɗin rubutu?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Ni na fi jin daɗin rubutu a lokacin da na kaɗaice kuma na ke cikin nishaɗi.
FIM: A yanzu idan za a tambaye ki irin nasarorin da ki ka samu, ko akwai su?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Alhamdu lillah, tabbas na samu nasarori masu tarin yawa a harkar rubutu daga lokacin da na fara zuwa yanzu. Babbar nasarar da na ke alfahari da ita a ko da yaushe ita ce yadda na san mutane da dama masu daraja da a ko da yaushe cikin yi mini addu’a su ke ni da iyaye na da su ka riga mu gidan gaskiya. Sannan kuma ina samun kyaututtuka da dama daga masoya na masu bibiyar littattafai na. Sannan kuma na samu nasara a gasar rubutu da ‘Association of Nigerian Authors’ su ka shirya inda na zo ta biyu. Alhamdu lillah! Sosai na ke alfahari da wannan nasara da na samu, saboda na samu kyautar kuɗi da kuma kambu. Abin farin cikin ma shi ne na samu ƙarin ɗaukaka a sanadiyyar wannan nasara da na yi. Sannan kuma na sake samun nasara a gasar gajeren labari da marubuta su ke shiryawa duk wata a manhajar Whatsapp inda shi ma na zo ta ɗaya. Sannan kuma alhamdu lillahi kwanaki ‘Freedom Radio FM’ Kano sun gayyace ni sun yi hira da ni a matsayi na na marubuciya. Alhamdu lillah, wannan ma wani mataki ne na nasara.
FIM: Ana ɗan ƙorafi game da ku masu rubutun onlayin wajen rashin bin ƙa’idar rubutun Hausa. Wasu abubuwan da ku ke rubutawa sai su kasance su ba Turanci ba, kuma ba Hausa ba.
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: To maganar gaskiya rubutun da mu ke yi a onlayin a da da kuma yanzu ba ɗaya ba ne akwai bambanci sosai, saboda yanzu mu na tare da manyan marubuta waɗanda a kullum burin su shi ne su ga mun gyara rubutun mu mun kuma tsarkake alƙalamin mu. Kullum cikin kula da mu su ke, sai dai mu ce Allah ya saka masu da alkairi.
Sannan yawancin masu rubutun batsa ɗin nan a yanzu za ka ga ba su da ƙungiya, zaman kan su su ke yi. Idan mutum ya na cikin ƙungiya babu yadda za a yi a bar shi a rinka rubutun batsa dole za a tsawatar masa, ƙungiya ba za ta taɓa bari ‘ya’yan ta su ja mata ɓacin suna ba.
FIM: Ko akwai wasu matsaloli da marubutan onlayin su ke fuskanta?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: E to, gaskiya marubutan onlayin mu na fuskantar satar fasaha daga wasu mutane za a ɗauki labarin mu ba da izinin mu ba a je a karanta shi a YouTube, wanda kuma kuɗi su ke yi da hakan, ko kuma a cire sunan mu ma a jiki a juya labarin zuwa wata sigar ko kuma a rinƙa fitar mana da shi ana karantawa ba tare da an biya kuɗi ba. Wannan shi ne kaɗan daga cikin matsalolin da mu ke fuskanta.

FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Saƙo na na ƙarshe zuwa ga marubuta ne da kuma makaranta; marubuta mu ji tsoron Allah, mu sani cewa duk abin da mu ka rubuta za a tambaye mu a kan sa. Don haka ya zama dole mu tsarkake alƙaluman mu, mu rubuta abin da zai amfani al’umma wanda ko bayan ran mu za a yi alfahari da shi.
Sai kuma saƙo zuwa ga makaranta masoya na masu bibiyar littafai na. Ku sani, ina ƙaunar ku saboda da bazar ku na ke taka rawa. A kullum ina faɗin cewa idan babu makaranci tabbas babu marubuci. Ina yi maku fatan alheri.
FIM: To madalla mun gode.
FIRDAUSI MUHAMMAD SODANGI: Ni ma na gode.
Ma sha Allha
Masha, Allah anty feedonmu Allah ya qara daukaka