• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rayuwa da gwagwarmayar Daudu Galadanchi (1934-2020)

by DAGA MUKHTAR YAKUBU DA IRO MAMMAN
May 14, 2020
in Nijeriya
0
Alhaji Daudu Ahmed Galadanchi (1934-2020)

Alhaji Daudu Ahmed Galadanchi (1934-2020)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DAUDU Ahmed Galadanchi ya jima ya na fama da rashin lafiya, ga tsufa. Sai da ta kasance a tsawon shekaru ba ya zuwa ko’ina, a ko da yaushe ya na cikin gida, sai ɗan sa ɗaya tilo da ya ke kula da shi. 

A watannin baya da membobin ƙungiyar jarumai ‘yan fim su ka kai masa ziyara a gida, ɗaya daga cikin abokan aikin sa, Hajiya Ladin Cima (Tambaya), ta shaida wa mujallar Fim cewa a lokacin ba ya gane kowa. Ya na dai kallon mutane kamar zai yi magana, amma ba ya iya maganar, kuma ba ya gane wanda ya je wajen sa ɗin. 

 Tambaya, wadda ita ma tsohuwar ‘yar wasa ce, ta ƙara da cewa ko ita ma da su ka yi aiki tare ya daina gane ta idan ta je, sai dai ta duba shi ta tafi.

 A jiya Laraba, 13 ga Mayu, 2020 Allah ya ɗauki ran wannan fitaccen ɗan dirama. A safiyar yau aka a yi jana’izar sa, aka rufe shi a maƙabartar Goron Dutse. Ɗimbin jama’a, ciki har da ‘yan fim, sun halarta.

 Alhaji Daudu Galadanchi, ɗan shekara 86 a duniya, ya rasu ne a gidan sa da ke unguwar Galadanchi a cikin Birnin Kano. Ya bar mace ɗaya da ɗan sa ɗaya. 

An yi ittifaƙi da cewa marigayin ya kasance shi ne kaɗai ya yi saura a cikin abokan aikin sa da su ka samar da harkar dirama a Kano. 

Domin jin asali da tarihin Alhaji Daudu Galadanchi, mujallar Fim ta binciko wata hira da ta taɓa yi da shi wadda aka buga a watan Agusta 2006, inda ya bayar da tarihin rayuwar sa da irin gwagwarmayar da ya sha.

 Da mu ka tambaye shi tarihin sa, ya amsa da cewa: “Tarihin rayuwa ta dai ya na da tsawo, sai dai kamar yadda ka ce na taƙaita, to a taƙaice za ka samu. 

 “An haife ni a unguwar Kankarofi a gidan mahaifi na a shekara ta 1934. Kuma ni kaɗai ne namiji a wajen mahaifi na a lokacin. To, bayan na cika shekara 12 sai aka saka ni a makarantar allo. A lokacin kuma da na kai shekaru 14, sai aka mayar da ni Elementare ta gidan Sarki da ke Ƙofar Kudu. 

 “Bayan na kammala shekara huɗu sai na samu shiga Middle School a 1942. A wannan lokacin, Mai Martaba Sarkin Ringim da Mai Martaba Sarkin Kano su na gaban mu da aji ɗaya. 

“Bayan da aka yi wa mahaifi na Hakimi a ƙasar Gezawa, ganin na kammala karatu, sai ya ɗauke ni domin na yi masa Malamin Hakimi.  

“Da aikin nasa na Gezawa ya ƙare, sai mu ka dawo nan Kano inda ni kuma na fara aiki a Gidan Gona. Ina wannan aikin sai na tafi Sakkwato, inda na yi wani kwas na shekara ɗaya  na ‘Clerical’, da ma aikin akawu na yi.  

“Bayan na dawo, sai aka yi mini canjin wajen aiki, na koma Babban Kurkuku inda na zama akawun su na kuɗi, kuma ina nan har lokacin da na yi ritaya a shekarar 1984, wanda kuma daga nan ne na koma Hukumar Tarihi Da Al’adu ta Jihar Kano inda aka naɗa ni ‘Board Member’ na wurin, daga baya kuma aka nada ni ‘Board Member’ na gidan CTV.” 

Dangane da yadda ya fara dirama kuwa, cewa ya yi, “A lokacin da na ke makaranta ba a yin dirama, sai bayan na dawo nan Galadanchi inda na ke tare da ‘yan’uwa na da abokan arziki. Sai mu ka kafa ƙungiyar wasan kwaikwayo a nan cikin gidan Galadiman Kano, kuma a wannan lokacin mun samu haɗin kan mutane masu yawa. Daga cikin waɗanda mu ka kafa wannan ƙungiyar da su akwai Malam Muhammadu Bamalli da sauran mutane da yawa tun da ya ke unguwanni ne mu ka taru. 

“A wannan lokacin ne sai Sardauna ya fito da taro na gasa wanda ake kira da sunan ‘Home Arts and Culture’, inda mu ke tafiya Kaduna domin yin gasar.  

“A lokacin da mu ka je daga nan Kano, mun samu nasarar ciwo wani takobi da Sarki ya saka a gasar, Sunan ƙungiyar tamu ‘Maitama Sule Drama Group’. 

“Wannan gasa da mu ka shiga har mu ka yi nasara shi ne silar shigar mu talbijin, domin a lokacin da ake gudanar da gasar wani daga cikin masu aikin gidan talbijin ɗin ya lura da irin wasan da mu ka gabatar, shi ne ya ce ya na so mu rinƙa yi masa ana sakawa a talbijin.  

Gawar Daudu Galadanchi cikin makara za a kai ta kushewa

“Saboda haka tun daga Kaduna ya ke zuwa Kano ɗaukar mu, idan mun gama ya dawo da mu har ta kai mu na ɗaukar mota daga nan Kano mu tafi Kaduna duk bayan sati biyu. To a taƙaice dai diramar da mu ka yi ta farko ta burge jama’a har su ka nuna su na da sha’awar ta.  

“Daga nan sai aka kawo wani shiri na shari’a ko in ce a kan shari’a wanda aka saka wa suna ‘Ƙuliya Manta Sabo’, kuma aƙalla mun yi wannan wasan ɗai ɗai ya fi ɗari biyu. 

“Daga nan sai Kano su ka fara shirye-shiryen kafa gidan talbijin ɗin su na NTA. Da dai a nan Kano akwai shiyya, ‘sub-station’ wanda su kan kamo su watsa bayan an yi a Kaduna.  

“Bayan da aka buɗe NTA Kano sai aka nemi mu dawo mu rinƙa yi a nan Kano. Da haka sai aka buɗe CTV a GZidan Gwamna kafin su koma inda aka gina musu, kuma mu ka tambaya ko wanne shiri su ke so? Sai su ka ce mu ci gaba da yin ‘Ƙuliya’. 

Ana wannan hali, bayan Sadiq Ɓalewa ya dawo daga London, sai ya zo da wasu Turawa ya ce ya na so za mu yi wani fim mai suna ‘Ƙasar Mu Ce’, tare da ni da Mustapha Ɗanhaki da wani da mu ke yin wasa tare mai suna Malam Uba da wasu yara biyu daga Hukumar Tarihi Da Al’adu aka tafi da mu Bauchi, sai da mu ka yi wata biyu a can kafin mu kammala wannan fim ɗin. Ba mu kaɗai ba ne a lokacin; ya ɗauko wasu daga Sakkwato, wasu daga Kaduna, wasu kuma daga Bauchi ɗin. 

“Bayan mun kammala mu na dawowa  sai wani furodusa daga Sakkwato ya gayyace mu wani fim mai suna ‘Life and Times of Shehu Usman Ɗanfodio’, amma har yanzu ba su fito da fim ɗin kasuwa ba. Gwamnatin Jihar Sakkwato ce ta ɗauki nauyi, kuma ta kashe kuɗi masu yawa, domin sai da aka gina wani gari babba a Shinkafi, mu kuma aka ɗinka mana kaya irin na wancan zamanin, shi kuma zaman mu na Sakkwato watan mu uku a nan Shinkafi, sai dai mu kan samu hutu mu dawo gida. Kuma an yi wannan fim ɗin a wajen 1986 ko kusa da haka. 

“Sai dai ban iya riƙe shekarun da mu ka fara dirama ba, amma dai a lokacin Sarkin Kano Inuwa ne.” 

Da yayin shirya finafinan bidiyo na Hausa ya zo, Alhaji Daudu Galadanchi na daga cikin tsofaffin ‘yan dirama da su ka shiga ciki, aka tafi tare da su. Ya fito a irin waɗannan finafinai masu yawan gaske. 

Shi ya sa mutuwar ɗan wasan ta girgiza ‘yan fim da dama, musamman waɗanda su ka san shi, su ka yi aiki da shi. Da yawa sun yi masa addu’ar samun rahamar Ubangiji.

 A saƙon ta’aziyya da ya rubuta, ɗaya daga cikin magadan sa a fagen dirama, wato fitaccen jarumi, furodusa kuma darakta Alhaji Ibrahim Mandawari, ya bayyana cewa, “Wannan bawan Allah na daga cikin ƙalilan da ya riƙa karɓar gayyatar shirin ‘home videos’ ba tare da girman kai ba, daga ‘ya’yan sa da jikokin sa na masana’antar finafinan Hausa.

 “Kazalika, Alhaji Daudu ne kaɗai ya sami tagomashi wajen matasan ‘yan fim na Hausa domin kuwa su kan kai masa ziyarar girmamawa a lokuta daban-daban.”

 Shi kuwa fitaccen jarumi kuma tsohon shugaban ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta ƙasa (Motion Pictures Practitioners Association, MOPPAN), Alhaji Sani Mu’azu, ga abin da ya ce: “Allahu Akbar! Allah ya jiƙan Alhaji Daudu Galadanchi. Ya na daga cikin dattawan da su ka yi saura daga cikin masana’antar mu, idan ma ba shi ne na ƙarshe ba cikin waɗanda su ka yi zamanin farko.  

“Alhahi Daudu dattijo ne na ƙwarai wanda na ke girmamawa matuƙa. Ya daɗe ya na fama da jiyya. 

Dandazon mahalarta jana’izar Alh. Daudu Galadanchi … yau a Kano

 “Allah ya sa jiyya ta zama kaffara. Allah ya jiƙan sa da rahama. Allah Ya sa shi a gidan Aljanna. Allah Ya kyautata namu ƙarshen, amin.” 

A tasa ta’aziyyar, babban furodusan nan mazaunin Zariya, Alhaji Magaji Sulaiman, ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya jiƙan kakan mu Dauda Galadanchi, ya sa Aljanna makoma a gare shi da al’umman Annabi baki ɗaya, amin.”

 To mu ma mun ce amin. 

Loading

Previous Post

Daudu Galadanchin da na sani, daga Mandawari

Next Post

Cewar Iyan-Tama: A dinga uziri ‘yan’uwa

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Alh. Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama

Cewar Iyan-Tama: A dinga uziri 'yan'uwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!