• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rikicin mawaƙa: Ummi B.Y. ta maka El-Mu’az Birniwa a kotu a Kaduna

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 4, 2022
in Labarai
3
Ummi B.Y. da El-Mu'az Birniwa

Ummi B.Y. da El-Mu'az Birniwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘIYA kuma jaruma a Kannywood, Amina Abdullahi, wadda aka fi sani da Ummi B.Y., ta maka fitaccen mawaƙin nan El-Mu’az Muhammad Birniwa a kotu kan zargin tsoratarwa.

Ta shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Majistare da ke unguwar Rigachikun, Kaduna, a ranar 29 ga Satumba, 2022, ta hanyar lauyan ta, Abdulsaleem Umar na cambar ‘M.T. Mohammed and Co. (Pinnacle Chambers)’ da ke Titin Alƙali, cikin garin Kaduna.

Sammacin ƙarar, wanda mujallar Fim ta samu kwafen sa, ya nuna cewa Ummi ta yi ƙarar El-Mu’az ne bisa babban laifin barazana (direct criminal complaint for the offence of intimidation) wanda ya saɓa wa sashe na 377 na kundin finalkod na Jihar Kaduna na shekarar 2017.

A sammacin, jarumar ta faɗa wa kotun cewa ita mazauniyar garin Birnin Yero ce, yayin da shi El-Mu’az mazaunin Unguwar Kaji ne da ke garin Kaduna, don haka kotun na da hurumin sauraren ƙarar.

Ta ce a ranar 2 ga Satumba, 2022 ta kira wanda ta ke ƙarar a waya domin su gaisa a matsayin sa na abokin hulɗar ta, amma sai kawai ya shiga surfa mata zagi tare da yi mata barazanar sai ya sa yaran sa sun kashe ta kuma babu abin da za a yi tunda ya na da iko a cikin al’umma.

Sammacin ƙarar da Ummi ta kai El-Mu’az

Ta ƙara da cewa a cigaba da barazanar da ya yi mata, da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar 22 ga Satumba sai ga wasu ‘yan daba ya turo mata har gida domin su ɗauke ta su tafi da ita zuwa wani waje da ba ta sani ba, amma wasu bayin Allah su ka taimaka mata su ka hana ‘yan iskar shiga gidan.

“Yanzu wadda ke ƙarar ta na fargabar fita daga gida saboda tsoron kada wanda ake ƙarar ko yaran sa su da ya ɗauka su kai mata hari ba tare da wani dalili ba,” inji lauyan ta.

Ya ce a yanzu haka El-Mu’az ya na nan ya na neman Ummin ruwa a jallo a kan tunanin cewar shi wani isasshe ne wanda ko me ya aikata ba za a iya yi masa komai ba.

Lauyan ya nuna wa kotun cewa wannan abu da ake zargin El-Mu’az da aikatawa babban laifi ne wanda ya saɓa wa sashe na 377 na kundin finalkod na Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Idan kun tuna, mujallar Fim a makon jiya ta ba da labarin yadda rigima ta kaure a tsakanin mawaƙan biyu.

Loading

Tags: Abdulsaleem UmarAmina MohammedbarazanaBirnin YerofinalkodintimidationKannywoodkotun majistarelauyaM.T. Mohammed and Co.mawaƙaPinnacle ChambersRigachikunUmmi B.Y.Unguwar Kaji
Previous Post

Za mu samar da cibiyar koyar da sana’ar fim a Kano – Gwamna Ganduje

Next Post

Bikin auren jarumar Kannywood Ruƙayya Dawayya da shugaban Hukumar Tace Finafinai, Afakallah ya matso

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post
Dawayya da Afakallah

Bikin auren jarumar Kannywood Ruƙayya Dawayya da shugaban Hukumar Tace Finafinai, Afakallah ya matso

Comments 3

  1. Pingback: Mawakiya Ummi B.Y ta maka mawaki El-Mu'az Birniwa a kotu kan yi mata barazanar zai sa a kashe ta - Kyauta Blog
  2. Pingback: Mawakiya Ummi B.Y ta maka mawaki El-Mu’az Birniwa a kotu kan yi mata barazanar zai sa a kashe tah - Dailygistnaija
  3. Pingback: Mawakiya Ummi B.Y ta maka mawaki El-Mu’az Birniwa a kotu kan yi mata barazanar zai sa a kashe ta - Mr ATG News.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!