A ƘOƘARIN da ta ke yi na samar da bunƙasar masana’antar finafinai ta Kannywood, gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin samar da wata cibiya domin koyar da harkar fim.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke buɗe taron sanin makamar aiki wanda gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin gudanarwa a otal ɗin Central da ke Titin Bompai a ranar Lahadi.
Gwamnan ya ce, “Duba da irin muhimmancin da sana’ar fim ta ke da shi a duniya mu ka ga ya kamata mu samar maku da wasu hanyoyi na inganta sana’ar ku yadda za ta tafi da zamani da kuma ilimi. Don haka ne mu ka samar da wani tsari a yanzu na koyar da ku dabarun sanin makamar aiki da kuma ilimi a cikin harkar taku, shi ya sa mu ka taru a wannan waje domin buɗe fara koyar da ku da za a yi na tsawon kwanaki biyar saboda ku ƙara sanin yadda harkokin kasuwancin naku ya ke.”
Gwamnan ya ce hakan ya samu ne a sakamakon yadda gwamnatin sa ta damu da sana’ar fim kamar yadda su ma ‘yan fim ɗin su ke ba gwamnati goyon baya wajen gudanar da al’amurran ta.
Ya ƙara da cewa, “Duba da irin alaƙar ku da wannan gwamnati ya sa mu ka zaɓi wasu daga cikin ku mu ka saka su a cikin ƙunshin gwamnatin mu domin ku ma ku ba da taku gudunmawar a matsayin ku da ku ka daɗe ku na bayar da goyon baya a tafiyar da gwamnati.

“Ga Afakallahu nan, ɗan cikin ku ne mu ka ba shi Hukumar Tace Finafinai ya ke riƙe da ita. Kuma ga Mustapha Badamasi Nabraska shi ma S.A. ne na Farfaganda, da kuma wani babba a cikin ku da mu ka ba shi babban mai ba da shawara a kan Kannywood. Don haka mu na tare da ku kamar yadda ku ke ba mu goyon bayan ku.”
Gwamnan ya ce, “Bayan wannan hosarwa da za a yi maku, mu na da burin gina maku sabuwar cibiyar koyar da dabarun harkar fim a wannan jiha. Amma aikin zai yiwu ne idan kun haɗa kan ku kun samar da tsari a tsakanin ku, wanda hakan ne zai sa a samar da ƙwararru da za su tafiyar da harkar cibiyar.
“Don haka ina kira a gare ku da ku haɗa kan ku domin tafiya tare. Mu kuma a namu ɓangaren na gwamnati, za mu samar muku tsare-tsare masu muhimmanci a kan masana’antar ku.”
Tun da farko da ya ke nasa jawabi, shugaban Gidauniyar Kannywood, Malam Shu’aibu Yawale, ya bayyana Dakta Ganduje a matsayin gwamnan da ya bai wa masana’antar Kannywood kulawar da babu wani gwamna da ya taɓa ba ta.
Ya ce: “Babu shakka, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne gwamnan da ba a taɓa samun wani gwamna da ya ke kula da masana’antar Kannywood kamar sa ba, domin an ɗauki mutane daga cikin mu an saka su a cikin harkar gwamnati, an ɗauki nauyin karatun wasu daga cikin mu, za su tafi ƙasashen waje karatu. A yanzu kuma mu na taro ne na buɗe koyar da mu ilimin harkar fim aƙalla mutane 450
“Don haka a kullum mu ke godiya tare da jinjina ga wannan gwamnati. Kuma a shiye mu ke mu bayar da duk wata gudunmawar da ta dace don ganin gwamnati ta cimma manufofin ta da ta sa a gaba.”
Shi kuwa a nasa jawabin, malami a Jami’ar Bayero kuma masani kan harkar fim, Farfesa Abdalla Uba Adamu, kira ya yi ga ‘yan fim da su gane cewa shi fim ba kasuwanci ba ne, sana’a ne, don haka su daina tunanin samun kuɗi a lokaci guda.
Ya ce: “Duk ƙasashen da su ka ci gaba a harkar fim sun ɗauki harkar fim ne a matsayin sana’a, don haka su ke samun cigaba. Amma mu namu finafinan mun tsaya har yanzu a kan rawa da waƙa. Tun da aka faro harkar daga bidiyo aka koma sidi zuwa dibidi, har yanzu abu ɗaya ne. Babu wani abu da ake nunawa na zahirin al’adun Bahaushe ko ilimin sa da sana’o’in sa.
“Saboda haka, a yanzu da duniya ta canza aka koma YouTube, ya kamata a samu wani sauyi da za a riƙa kallon rayuwar Hausawa da cigaban da su ke da shi.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa taron ya samu halartar jama’a masu yawa daga cikin masana’antar Kannywood, kuma an yi waƙoƙin siyasa tare da tallata jam’iyyar APC a wajen, wanda hakan ya sa wasu ke ƙorafin ko dai Dattawan Kannywood sun sayar da masana’antar da gwamnati ne.
An kammala taron da shirya liyafar cin abincin dare a Gidan Gwamnati, inda aka zaɓi wasu daga cikin ‘yan masana’antar aka kai su su ka ci abinci tare da gwamna.

![]()








Comments 1