• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rikicin PDP: Na amince da tayin sulhun da su Wike su ka yi, inji Atiku

by DAGA WAKILIN MU
November 12, 2022
in Nijeriya
0
Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, ya bayyana cewa ya na maraba lale da tayin neman yin sulhu da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, da magoya bayan sa su ka nema.

Atiku ya kuma nuna cewa ya amince da sasantawa da su Wike ɗin domin a kawo ƙarshen rikici da dambarwar da su ka dabaibaye PDP.

Ya ce yin hakan abu ne mai muhimmancin da zai ƙara haɗa kan ‘yan jam’iyya, sannan ya ƙara ƙarfafa PDP ƙwarai da gaske.

Atiku ya yi tsinkayen cewa tun da aka fara wannan dambarwa da Wike da ‘yan ɓangaren sa, bai taɓa rufe masu ƙofar shiga a sasanta ba.

Daga nan ya yi kira ga dukkan shugabannin jam’iyya da magoya bayan ta su kasance masu goyon bayan wannan ƙoƙarin sasanci.

Idan ba a manta ba, bayan ɓangaren Wike ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, sun shaida wa manema labarai cewa har yanzu ƙofar zama a sasanta tsakanin su da Atiku da PDP a buɗe ta.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Atiku mai suna Paul Ibe ya fitar, ya ce sasancin shi ne mafi alheri domin a ƙara wa jam’iyya ƙarfi, karsashi, sannan kuma a samu haɗin kai baki ɗaya.

Sannan kuma a wurin ne Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi afuwar zafafa kalaman da ya yi kan Atiku, inda ya ce da ya zaɓi Bafulatani, gara ya mutu.

Loading

Tags: Atiku AbubakarBala MohammedNyesome WikePaul IbePDPrikiciSamuel OrtomsasancisulhuZaɓen 2023
Previous Post

Najib Marubuci da Khadija sun angwance

Next Post

Jami’a a ƙasar Togo ta ba furodusan Kannywood Abdul Amart digirin girmamawa

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Bikin ba da digirin dakta ga Abdul Amart a Jami'ar IHIRIS, a Lomé

Jami'a a ƙasar Togo ta ba furodusan Kannywood Abdul Amart digirin girmamawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!