TUN bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta mayar da aikin sabunta rajistar ‘yan Kannywood ga hannun ƙungiyoyin ‘yan fim mutane su ka zuba ido su ga ta inda za su fara.
Kan haka ne mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, waɗanda su ne ke da alhakin gudanar da rajistar, domin ya faɗa mana inda aka kwana a kan maganar.
FIM: Ko yaya wannan sabunta rijistar zai kasance?
ADO GIDAN DABINO: To waɗanda su ka bibiyi ayyukan Hukumar Tace Finafinai a can baya sun san da cewa kama ita hukumar ta tattara dukkan ayyuka ta na yi, da wanda ya kamata su yi, wanda ƙungiyoyi ne ya kamata su yi, domin idan ka kula ita hukumar akwai abin da doka ta ce su yi, akwai kuma wanda ƙungiyoyi ne ya kamata su yi. To shi ne aka rinƙa samun hayaniya da sauran su. To kuma a yanzu dai kila mu na ganin sabon shugabancin da aka yi, za a fahimci wannan lamarin, shi ya sa ake so a ba da wannan dama wadda ita ƙungiyar MOPPAN ita ce uwar ƙungiyoyi da kuma ita Arewa wadda ita ma ta na tafiya tare da MOPPAN; abin nufi su na da alaƙa ta aiki tare, don haka MOPPAN ce gaba da ita, amma da aka zo aikin sai aka yi haɗaka yadda ita za ta yi wa kamfanoni rajista, su kuma MOPPAN su kula da sauran ɓangare kamar daraktoci, jarumai da sauran su.
FIM: Tunda ku ƙungiyoyi ne za ku gudanar da aikin, yaya tsarin aikin zai gudana?
GIDAN DABINO: To, abin da mu ke ta ƙoƙarin yi shi ne musamman ka ga kamar ɓangaren jarumai, wajen ɓangaren mata a nan aka fi samun matsaloli da yawa, shi ne mu ke son za mu yi aiki da ita ƙungiyar jarumai domin tantance jarumi ko jaruma, idan ana son a zauna da shi ko a zauna da ita. To akwai wakilcin ƙungiyar MOPPAN da na Hukumar Tace Finafinai, sannan daga cikin Dattawan Kannywood an ɗauko. To wannan haka mu ke son mu yi, ko da a baya ba a yin hakan, a yanzu mu na fatan a yi hakan saboda a samu tsarkake harkar. Amma ba wai mun ce waɗanda su ka yi a baya ba su iya ba, sai dai ya zama kowane allazi da na sa amanu. Don haka ina ganin wannan wani tsari ne wanda za a yi shi a buɗe, wanda hakan zai rage mana hayaniya wanda ko a cikin fom ɗin za ka ga sai kamfani ya tsaya maka. Sannan akwai ɓangaren iyaye. To wannan duk mu na ƙoƙarin mu kauce wa matsalolin da ake gani akwai su a can baya.
FIM: Akwai matsala ta kwararowar mata, wasu daga Nijar, Kamaru, Chadi, da sauran su. Ko yaya matsayin wanda zai tsaya musu?
GIDAN DABINO: Abin da mu ka tsara a yanzu ko daga ina ka zo ai ka na da wanda ka sauka a wajen sa, wanda za ka cike a fom ɗin ka da lambar wayar sa, kuma za ka sanar da shi, sannan za a kira shi in aka zo wannan tantancewar idan mu ka tambaye shi ya amince kuma ya bayar da shaidar cewa ɗan’uwa na ne ko ɗa na ne, ƙane na, ko ma me za mu ce abin da ya sa aka kira ka shi ne kai ka tsaya wa wane, idan wani abu ya faru an tashi nema kai za a nema, ka yarda? In ya yarda shi kenan. Saboda ai yanzu ba za ka ce sai ka tashi ka tafi Kamaru ba ko Nijar tunda yanzu zamani ne na onlayin.
FIM: Zuwa yaushe ake tunanin za a fara aikin sabunta rajistar?
GIDAN DABINO: To yanzu dai abin da ake sa rai za a fara shi ne yi wa kamfanoni, wanda idan aka fara ta kan su, waɗanda su ne za su tsaya wa jarumai a matsayin kamfanin da su ke aiki, don haka ake son a fara ta kan su. Kuma daga an gama nasu, za a shiga na jarumai. Don haka a wannan gaɓa na ke son na yi kira ga ƙungiyoyi cewa duk wani abu da za a yi na ci-gaba, don Allah su rinƙa ba shi goyon baya don ya zama an yi abin cikin nasara, an gama shi cikin nasara.
Kuma mu ji tsoron Allah a kan ayyukan mu domin abu ne da mu ke yi na jagoranci kuma Allah zai tambaye mu a kan abin da mu ka gudanar.
FIM: To, madalla. Mun gode.
GIDAN DABINO: Ni ma na gode.
![]()






