• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sai da d’a na Lil Ameer ya rasu na kara gane daukakar shi – Hajiya Khadija

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 5, 2017
in Mawaƙa
0
Lil Ameer

Lil Ameer

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

RASUWAR Ali Isah Hassan, wanda aka fi sani da Lil Ameer, ta fito da shahara da kuma daukakar da Allah Ya ba yaron a fagen wakar Hausa ta zamani, wato hip-hop. Lil Ameer yaro ne karami, domin an haife shi a ranar 22 ga Mayu, 2003, wato shekarar sa 14 kacal. Allah Ya dau ran sa a ranar Alhamis, 14 ga Satumba, 2017 a wani hadarin mota da ya ritsa da shi a Titin Maiduguri cikin Birnin Kano. An yi jana’izar sa washegari. Lokacin rasuwar sa ya na gab da kammala karatun sa na sakandare.

Tun Ameer ya na dan shekara 9 ya soma waka, tare da goyon bayan iyayen sa; hasali ma dai akwai lokacin da mahaifiyar sa ce ke rubuta masa waka, kafin daga bisani ya rika rubutawa da kan sa. Kafin rasuwar sa, Ameer ya yi nisa wajen cirar tuta a fagen hip-hop. Ya yi wakoki da daman gaske wadanda ake saka su a rediyo; wasu shi kadai, wasu kuma shi da wasu mawakan. Sun hada da ‘Kai Matsa Mana,’ ‘Dance for Me’, ‘I Am a Champion’, ‘Ilimin Boko Da Na Addinin Musulunci’ da wakar da su ka yi da Danko mai taken ‘So Mai Son Ka, Duniya Haka Tai Mana nunin Zance’. Kusan duk wakar sa wa’azi ce ga al’umma baki daya. Wani abin mamaki shi ne yadda ya ke waka da Hausa da Turanci a lokaci guda, kuma ya na hawa kan kida da kafiya babu gargada ko kadan.

Zai yi wuya a kasar Hausa a ce ga wani mawaki da ya shahara duniya ta san shi tun ya na dan kankane kamar Lil Ameer, wanda wasu ke yi wa lakabi da ‘Dan’autan Mawaka’. Duk inda fasihi mai shekarun sa ya kai, to ya kai. An yi ittifaki da cewa ba a kasar Hausa kadai ba, a duk Nijeriya babu fitaccen mawakin hip-hop mai karancin shekaru kamar sa. Lakabin ‘Lil’ na nufin “Little”, wato karami, kamar yadda aka fi sanin mawakin Amurka din nan Dwayne Michael Carter, Jr., da sunan Lil Wayne.

Duk da cewar an yi labarai da dama a kan rasuwar Lil Ameer, sai dai akwai wani sirri na rayuwar sa wanda ba kowa ya san shi ba. Babu kuwa wanda ya san marigayin kamar mahaifiyar sa. Don haka ne wakilin mujallar Fim a Kano ya samu tattaunawa da mahaifiyar Lil Ameer, wato Hajiya Khadija Shehu Usman, inda ta bayyana masa yadda rayuwar su da Ali ta kasance. Ga hirar:

FIM: Hajiya  Khadija, ke ce mahaifiyar marigayi Lil Ameer. Ko za ki fada mana yadda ki ka samu labarin rasuwar tasa?

KHADIJA: To, assalamu alaikum. A matsayi na na mahaifiyar Ali, wanda aka fi sani da Lil Ameer, a ranar da ya rasu mun rabu da shi ne ya tafi Farm Centre za a duba masa wata sabuwar wayar sa da ya saya. To bayan ya tafi na yi ta kiran wayar sa don na fada masa ya gyara  min gida idan ya dawo kafin na koma, don a lokacin ina gidan mahaifiya ta. To, na yi ta kiran  sa ban same shi ba a waya. Ashe lokacin ya saka wayar ne a caji saboda an ce sai ta dauki tsawon lokaci ta na caji. Ko da ban same shi ba sai na tura masa sako. To dai ban ji wani abu daga gare shi ba. Sai zuwa can wani lokaci na ga an kira ni. Ina dagawa sai na ji ba shi ba ne; kawai sai na ji gaba na ya fadi. Na san dai ba lafiya ba.

Sai mu ka gaisa da mutumin, ya ke tambaya ta, “Ko menene alakar ki da mai wannan wayar?” Sai na ce da shi, “Da na ne, ni mahaifiyar sa ce. ” Sai ya ce da ni sun yi hadari ne, su na Asibitin Sir Sunusi.

To a lokacin ban gama jin maganar ba na bai wa mahaifiya ta wayar, ni kuma na fadi saboda kidima. A lokacin dai ban iya zuwa ba sai mahaifiya ta da kanwa ta ne su ka tafi, saboda ni ba na son na gan shi a cikin wani yanayi, duk da ba a sanar da ni ya rasu ba.

To, bayan sun je ina ta kiran su ina tambayar su halin da ya ke ciki, sai su ce ba a bar su sun shiga dakin da ya ke ba. Sai kawai na samu kai na cikin diriricewa, duk da ban kawo ya rasu ba. Amma ina tunanin yanayin da ya ke ciki. To ana cikin haka ne sai kawai na ji wani kanen Sani Danja ya kira ni ya na cewa, “Hajiya, ya mu ka ji da hakuri? ” To sai a nan na san Ameer ya rasu, kawai dai boye min aka yi.

FIM: Akwai maganganu a kan sanadin rasuwar tasa. Ko menene sanadiyyar rasuwar sa?

KHADIJA: To su dai su na tafiya ne a cikin mashin mai kafa uku, A Daidaita Sahu, sai mai tukin ya yi tukin ganganci, su ka fadi. A daidai lokacin kuma wani mai babbar mota ya zo, sai kawai ya debe su ya rinka jan su a kasa, kuma ya ja su waje mai nisa a kasa ba tare da ma ya sani ba. Sai daga baya aka fada masa. To shi ne ya yi sanadin mutuwar sa.

FIM: Yaya ki ka samu kan ki bayan rasuwar sa?

KHADIJA: To gaskiya ne na samu kai na a cikin yanayi da ban taba shiga ba, saboda irin shakuwar da ta ke tsakani na da shi. Don hakan na samu damuwa sosai da na rasa inda zan saka kai na.

FIM: A labarin rasuwar sa an fi ganin shakuwar ki da shi fiye da mahaifin sa. Ko yaya shakuwar sa da mahaifin sa?

KHADIJA: Haka ne, an fi nuna shakuwar mu da shi, amma shi ma mahaifin sa sun shaku da shi sosai, amma da yake shi ba mazaunin Kano ba ne, ya fi zama a Abuja, shi ya sa ya zama  ni ce mu ke tare da shi ko da yaushe.

Lil Ameer da mahaifiyar sa Hajiya Khadija Shehu Usman

FIM: Ko za ki fada mana yada zamantakewar ku ta ke da shi?

KHADIJA: To, gaskiya dai ka ga Ameer shi ne na uku a cikin ’ya’ya na amma mun shaku da shi, don ko karamar kanwar sa idan ta zo ta kwanta kusa da ni lokacin barci sai ya ture ta ya kwanta kusa da ni. Kuma duk da ina da mai yi min girki, amma shi ne ya ke yi min girkin abinci.

FIM: An ce ke ce ki ke rubuta masa wakokin da ya ke yi.

KHADIJA: E to, farkon lokacin da ya fara waka ni na ke rubuta masa, amma daga baya sai  ya zama shi ne ya ke rubuta wakar sa da kan sa. Don haka ko na rubuta masa sai ya ce ba ta yi masa ba.

FIM: Yaya ki ka dauki shaharar sa bayan rasuwar sa?

KHADIJA: To gaskiya rasuwar Ameer ta nuna min shaharar sa duk da cewa na san shaharar sa a baya, amma ban yi zaton ya wuce yadda na ke tunani ba sai bayan rasuwar sa. Don na ga yadda mutane su ke ta zuwa gaisuwa tare da tura min sako na ta’aziyya. Wasu sun san shi, amma ba su san da na ba ne sai bayan rasuwar sa da aka saka hoton da mu ke tare da shi. Akwai mutane da dama daga kasashen Turai da su ka kira ni su ka yi min ta’aziyya, ban da nan gida Najeriya.

FIM: A rayuwar sa wakokin sa za su kai kamar nawa?

KHADIJA: To ya yi wakoki sun kai talatin a yanzu, kuma akwai wadanda ya ke shirin yi na Sarkin Kano duk da a baya ya yi masa kala biyar. To ya na aikin daukar wakokin sa ma sai lamarin ya kasance.

FIM: Za ki iya sanin garuruwan da ya je don gudanar da waka?

KHADIJA: E, ya je jihohi irin su Jigawa, Gombe, Katsina, Kaduna da sauran su.

FIM: Da yake ya yi wakoki da yawa, ko akwai wani shiri da ki ke da shi na adana su don a ci gajiyar su nan gaba?

KHADIJA: E, ina da wannan shirin, amma dai sai nan gaba. Ka san  komai sai a hankali.

FIM: Daga karshe, wane sako ki ke da shi?

KHADIJA: To sako na godiya ce ga duk jama’ar da su ka yi mana ta’aziyya game da rasuwar sa. Ina yi wa kowa fatan alheri. Allah Ya bada lada.

Loading

Previous Post

Fati Nijar: Akwai rashin gaskiya a harkar fim

Next Post

Yadda mu ka yi alk’alancin gasar – Farfesa Malumfashi

Related Posts

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Next Post
Farfesa Ibrahim Malumfashi na gabatar da jawabi ga taron

Yadda mu ka yi alk'alancin gasar – Farfesa Malumfashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!