Wakilin mujallar Fim, ABBA MUHAMMAD, ya zanta da jagoran alk’alan gasar da BBC Hausa ta shira wa maruybuta mata ta bana, mai suna Hikaya Ta, wato Farfesa Ibrahim Malumfashi, a kan yadda su ka zak’ulo zakarun da aka karrama. Ga yadda ya yi masa bayani:
“Kamar yadda na sha fad’a, mu a wurin mu masu nazari da harka na adabi a cikin jami’o’i ne ko kuma a cikin makarantu ne abin alfahari ne a wurin mu. Sannan a hukumance mu na ganin wani samun ci-gaba ne, an dad’e ba a samu irin shi ba.
“A kullum mu kan ce marubuta su na buk’atar taimako, su na buk’atar tallafi, su na buk’atar su nuna cewa su ma su na buk’atar abin da al’umma za ta yi alfahari da shi. To irin wannan abin ne mu ke ganin cewa BBC ta d’auko, kuma ta zab’i wani b’angare na al’ummar, ita ce mata. Saboda kamar yadda aka sha fad’a, su mata su na da abubuwa da yawa cikin rayuwar su, wanda idan ba an ba su wannan damar ba ba za su bayyana shi yadda su ke so ba. Saboda haka wannan dama ce da aka ba mata a Arewacin Nijeriya da ma duk inda ake magana da Hausa, su fito su nuna fasahar su, su nuna bajintar su da duk irin fik’irar da Ubangiji Ya yi masu su bayyana irin matsalolin da ke addabar al’umma.
“Saboda haka mu na cewa Allah Ya k’ara wa BBC k’warin gwiwa, na a ga cewa wannan abu ba a daina shi ba, an k’ara hab’aka shi ne.”
Kasancewar kai ne ka shugabanci alk’alan da su ka fitar da wad’annan fasihan marubuta da su ka lashe wannan gasa, wace hanya ku ka bi don ganin kun zak’ulo wad’annan marubuta fasihai?
Amsa: “Kamar yadda mu ka sha fad’a, shi ma d’in alk’alancin wajen hawa uku ne aka yi. Akwai hawa na farko, wanda ba mu ne mu ka yi ba. Wannan BBC ne ta shirya da wasu mutane zab’ab’b’u, ta ba su dukkan labaran da ake da su ta tace mata guda sittin. Wad’annan guda sittin, sai aka samu wasu kuma su tace guda ashirin da biyar daga cikin su. Wad’annan guda ashirin da biyar su ne aka aiko mana, mu uku da ni da Hajiya Balaraba Ramat da kuma Rahama A. Majid. Mu ka zauna, kowa a gidan shi ya zauna ya zab’o guda sha biyar da su ka cancanci a yaba masu.
“Daga cikin sha biyar d’in nan kuma kowannen mu ya zab’i mutum uku da ya ke ganin cewa su ne ya kamata a ce sun yi na d’aya, na biyu da kuma na uku. Abin da kawai BBC ta yi mana, ta had’a mu a lokaci guda, ta ce mu had’u mu sake duba wannan jadawali namu a ga ko an samu daidaito tsakanin mu.
“To, abin da ya k’ara burge ni, babu inda aka samu daidaito sai a labari guda, shi ma mutum biyu ne kad’ai. Saboda haka wannan ya nuna cewa ni nawa guda uku daban su ke da wanda Rahama ta zab’a, daban su ke kuma da wanda Balaraba ta zab’a. Abin da mu ka yi shi ne, mu ka ce mu d’auko wad’annan labaran guda tara, mu sake bin su d’aya bayan d’aya, mu sake yi masu alk’alanci na musamman.
“Bayan mun yi wannan, bisa irin maki da mu ka ba kowanne, ya zamana cewa an zab’i ita Maimuna Idris Beli ta yi na d’aya. Sannan aka zab’i Bilkisu Makaranta ta yi na biyu. Sannan su kuma Hindatu da Habiba su ne ya kasance su ka yi had’in gwiwa.
“Mu abin da ya burge mu, ba mu san labarin had’in gwiwa ba ne. Mun d’auka labari ne na mace guda. Bayan an fad’a, sai mu ka gane cewa ashe mata ne biyu su ka had’u su ka tada labari guda!”
“K’alubale wurin tantance wad’annan marubuta: “{alubalen da kowa ya ke fuskanta wurin tace labari, shi ne ka rasa wanda za ka d’auka a cikin labarin. Nan wurin mu na magana ne a kan labarai guda ashirin da biyar, daga mata daban-daban masu magana kan jigo mabambanta, masu magana kan salo mabambanta. Sannan kuma kowannen su ya yi k’ok’ari ya kama dukkan abin da ya kamata ya kama don labarin ya yi dad’i.

“Abin da mu ka fuskanta shi ne mu iya fitar da ainihin gwarzuwar da mataimakan ta. Kamar yadda mu ka fad’a, mun amince wad’annan guda ukun da sauran sha biyun da aka d’ora su ne su ka dace su kasance gwarzayen wannan shekara na BBC.”
Shawarar Malumfashi ga sauran marubuta game da shiga wannan gasa: “In dama ta samu irin wannan, mu mu kan ce mutane su je su zauna su yi nazari su shiga irin wad’annan gasa, ta na taimakawa wuri uku. Na farko, ta na bada abin da mutum zai samu na d’an abin hasafi. Saboda kud’i ake badawa. Na biyu kuma, ta na ba mutum dama ya zama wani abu a cikin duniya. Yanzu dukkan wad’anda su ka shiga wannan gasar kowa ya san da su, ana ji da su. Na uku kuma ya iya zama wani kafa da marubuciyar nan ko kuma marubucin nan zai zama wani gagarumin marubuci ko marubuciya nan gaba. Saboda haka kada a yi wasa da irin wannan dama, a shige ta, za a k’aru da ita, in-sha Allah.”