BABBAN ɗan shahararren daraktan nan na Kannywood, marigayi Tijjani Ibrahim, wato Saleem Tijjani Ibrahim, ya bayyana irin gudunmawar da ‘yan Kannywood su ka ba shi a kan auren da zai yi a cikin wannan watan.
Saleem, wanda furodusa ne kuma shugaban kamfanin Fasaha Films, ya ce: “‘Yan Kannywood sun ba ni shawarwari sosai da kuma fatan alkhairi. Ina miƙa godiya ta a gare su baki ɗaya. Allah ya saka da alkhairi.”
Haka kuma ya ce, “Ina wa Allah (s.w.t.) godiya. Ina fatan Allah ya sanya albarka, ya kare dukkan fitina. Allah ya ba mu zuri’a ɗayyiba mai albarka. ‘Yan’uwa da abokan arziƙi kuma, Allah ya saka masu da alkhairi, ya bar zumunci.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa za a ɗaura auren Saleem da sahibar sa, Kaltume Zubairu, a ranar Juma’a, 25 ga Nuwamba, 2022 da misalin ƙarfe 2:00 na rana a masallacin Juma’a na Garu da ke Fadar Sarkin Dutse, Jihar Jigawa.
Kafin ranar, za a yi ƙunshin amarya a ranar Alhamis, 24 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a Hanan Hangout, Dutse.
Bayan an ɗaura aure kuma za a yi zaman al’ada da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a Garu, Dutse, Jihar Jigawa.
Sai kuma ɗaukar amarya daga Garu zuwa Tsada, Dutse, Jihar Jigawa.
Allah ya nuna mana ranar, amin.