ƊAYA daga cikin dattawan masana’antar finafinai ta Kannywood, Malam Sa’idu Isa Gwanja, ya yi kira ga masu gudanar da harkar fassarar finafinan Indiya da su yi taka-tsantsan wajen ɗaukar mataki da kuma kalaman da su ke yi dangane da haramcin da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta yi wa sana’ar su.
Malam Gwanja ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim a kan matsalar da ta kunno kai inda masu harkar fassarar su ka fusata kan dakatar da su da hukumar ta yi.
Ya ce: “Abin da na ke gani a soshiyal midiya da kuma maganganu da yaran su ke faɗa, sam bai dace ba, don haka su kalli abin da idon basira tare da saka hankali wajen bin hanyar da ta dace wajen warware matsalar.
“Idan hukuma ta ce ba bisa ƙa’ida ku ke kasuwancin ku ba, to sai ku zauna da su ku ji menene ƙa’idar kuma ta yaya za a bi ta.”
Ya ƙara da cewa: “Finafinan Indiya da sauran ƙasashe ba yanzu aka fara kawo su ƙasar nan ba, domin tun a baya ana kawo su ana nunawa a sinimu irin su El-Duniya, Wapa, El-Dorado, Marhaba da sauran su. Sannan akwai manyan kantina da su ke sayar da finafinan, kuma na san duk dokoki su ka bi wajen shigo da su tare da sayar da su ko nuna su, don haka ma su ka ci gajiyar su a lokacin.
“To tunda haka ne, wannan abu ne mai sauƙi ta hanyar Hukumar tace Finafinai ta Ƙasa a samar da hanyoyin da za ku haɗu ku yi yarjejeniya da masu kayan da ku ke fassarawar domin ku yi abin ku cikin tsari.
“Amma babu hukumar da za ta bar ku ku na karya doka ta bar ku a haka, sai ta ɗauki mataki. Kuma ko da ku ka ga an kawar da kai daga kan maganar, sai yanzu aka tayar da ita, to da man dokar ta na nan. Kuma idan ku na ganin sai yanzu aka yi maganar, to a baya ba a fassara finafinan, sai yanzu ake yi.”
Dattijon na Kannywood ya ƙara da nuna cewa: “A baya dokar ana yin maganar wadda ta shafi finafinai da mu ke yi na Kannywood, tun mu na yi a bidiyo, mu ka dawo sidi, dibidi, to yanzu kuma harkokin duk sun koma ‘online’, wanda hakan ne ya samar da kasuwancin naku.
“A yanzu duk wani fim da za a yi sai dai a kai YouTube ko gidan talbijin. To su ma abin duk ya zama kale, don haka ku ma taku harkar ta fassarar finafinan Indiya ko ba a hana ba, nan gaba sai zamani ya tafi da ita. Amma tunda yanzu ku na yin harkar, sai ku bi hanyar da za ku yi ta cikin tsari ta hanyar haɗa kai da gwamnati yadda za ku rinƙa cin gumin ku.
“Amma dai a yanzu ku na yi ne ba bisa yadda ta dace ba, don haka idan hukuma ta zo ta ce ku bi ƙa’ida, to taimaka muku ta yi.
“Saboda haka ni ina ganin gwamnati ta na son ta taimake ku ne wajen tafiyar da sana’ar cikin tsari da bin doka, kuma duk wani mai kishin ƙasar sa zai so a yi hakan. Don haka a bi doka a yi abu cikin tsari.”